Page 31

933 81 48
                                    

Hotel ɗin da yake sauka tare da yin rayuwarsa secret and privacy a Kano ɗin nan ya nufa da ita, a jikinsa yake jin idanuwanta na yawo a kansa ya share fuskarsa babu walwala ta yi jajur a haka driving da gudu dukda kasancewarsa Ustaz baya ƙaunar yin tuki a hankali.

Ustaz ya yi parking a harabar hotel ɗin a hankali ya kifa kansa a kan sitiyarin motar yana fid da numfashi wani irin zafi zuciyarsa ke yi masa, ciwon da ya yi na kwana biyu bayan faruwar abun shi ya hana shi dawowa, so yake ya zama mutum mai uzuri baya son nuna zafin zuciyarsa a kan Ridayya akwai tarin abubuwan da idan ya duba ya ke yi wa Ridayya uzuri. Yanzu ma a hargitse ya fito kuma baya son taga fushinsa domin ya fahimci idan ya nuna damuwarsa kamar hakan take so shi ne abinda take buƙata.

Fitowa ya yi daga cikin motar wani ya zo wajansa da sauri ya ɗan jingina da motar yana sauraren bayanin mutumin wanda tsayin lokaci ya kasa zama ya ji bayanin sai yanzu.

"Da gaske depression yana neman cin ƙarfinka damuwa ta yi wa zuciyarka yawa baka samun yin bacci cikin dare haka da rana ba yi kake ba, zuciyarka a ƙuntace take sosai hatta yawan ciwon kan da kaɗaitar da kake buƙata duk alamomin depression da rashin son maganar ka yi ƙoƙari ka samu nutsuwa ka ɗan ɓata lokacinka a kan wani abun da zai ɗauke maka kewa gudun kar kwakwalwarka ta samu matsala"

Ustaz ya yatsunsa fuska yana jan gemunsa dake yi masa ƙaiƙayi saboda sauyin yanayi baya son zafi weather ɗin Kano dana Lagos are different. Ya jima kafin ya ce

"Ina jin kamar ana kiran sunana ko ana jana wani wajan idan na rufe"

"Dole za ka ji hakan, amfanin zuwa asibitin kenan idan wasu ne cewa za su yi mutanen ɓoye ne ai cutar damuwa haka take signs and symptoms na depression yake you have to be very careful Sir, symptoms ɗin suna da yawa. Feelings of sadness, tearfulness, emptiness, or hopelessness
Anxiety, agitation, or restlessness
Behavior that looks like extreme laziness, rudeness, or disregard for others. Ɓacin rai da kulawa da lokaci, takaici, jin rashin fahimta da rashin kulawa, jin rashin sha'awa da wasu ayyukan al'ada, janyewa daga jama'a rashin mayar da kira rubutu da saƙon imel. Soke wasu tsare-tsare gajiyawa da rashin kuzari rashin samun wadataccen bacci,Jinkirin tunani, magana, ko motsin jiki. Feelings of worthlessness or guilt
Fixating on past failures or self-blame
Trouble thinking, concentrating, making decisions and remembering things"

Dr ɗin ya jinkirta kafin ya ce "Kai namiji ne wanda bai kamata a samu haka daga gare ka ba, i wonder why har ka samu kan ka cikin cutar damuwa dole ka kula kuma.....,"

"Enough!" Ustaz ya furta yana runtse idanunsa ya girgiza kansa kaɗan sai kuma kawai ya jinjina wa Dr ɗin kai tare da bashi damar tafiya.

Gabaɗaya ji ya yi jiri na neman ɗaukar shi, yana ganin mutane bibbiyu a idanunsa ga wani irin sabon ɓacin rai dake wanzuwa a zuciyarsa me miliyan yake nufi? Mahaukaci zai zama ko me sunan Allah kawai yake ambata har ya ɗan samu sassauci ya buɗe bayan motar ya ɗauki Little da har yanzu bacci yake, a nutse ya nufi ɓangaren ɗaya ƙofar ya saka key ya buɗe ya ganta ta kifa kai tana shassheƙar kuka ga rigar jikinta duk ta manne mata a fata da yatsunsa ya fara mata magana taƙi ɗago kanta shi ba zai iya tashin hankali ba ko buɗe baki ya yi zai yi magana har tsakiyar kansa yake jin wani irin dokawa.

Ta ɗago kai ta kasa kallonsa domin duk abinta bata iya kallon idanunsa, a hankali ta fito daga motar Ustaz ya bita da kallo yaga rigar sam ba ta yi masa ba

"Riƙe shi muga"

Amsar Little ta yi sai cin ɗaci take tana ɓata rai jerseyn jikinsa taga ya cire ya zama sai farar singlet a jikinsa da trouser ya zama ƙato a gabanta ya miƙa mata ta tura baki ta ce

"Ni ka mayar dani"

Ya girgiza kansa bai ce komai ba ya gyara tsaiwarsa tare da marsad ya saka mata jerseyn ta rufe mata kirji ya ɗan sauke numfashi maganar ita kanta ba komai take ji ba kamar mai raɗa ya ce

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now