Page 35

1.4K 109 56
                                    

Sakin ƙafarsa ta yi ta fasa abinda ta yi niyya jin kanta ya sara da ƙarfi Ustaz ya kalleta kamar zai share sai ya ce "Sai dai fatan Allah ya bawa ƴar rainota lafiya, amma Ustaz tuni kin ci kai bayan tsaraicina da kika gani kina ƙarama yanzu kike son sake gani? Zunubi har haka Ustaza?"

Ta tura baki taƙi cewa komai kanta a ƙasa maganganun Mami na mata yawo a kunne kamar yanzu take faɗa mata. "Abbiey wai zan iya zama matarka?"

Ya ware idanu da kyau yana mai gyara zaman shi ya ce "Kuma injiwa?"

"Haka na ji" girgiza kai ya yi yana sauke idanunsa a kanta a nutse ya ce

"Kina son zama matar tawa ne?" Ta tura baki ta ce "Ni dai kawai na tambaya ne, kaga ni ai ba zan iya haɗa Idanu da kai ba idan ka zama mijina"

"Jiki ma za ki haɗa dani soon Ustaza"

"Ma ka ce Abbiey?"

"Ke na ce mana" ta fara lumshe idanunta da suka fara yi mata laushi ga wani abu dake mata yawo saman fatarta.

"Ni ban ji ba ka sake faɗa" ya miƙe daga kishingiɗan da yake zuwa zaune ya gyara da kyau hannunsa ya miƙa masa ya ce "Zo mu yi sirri" ta ɗauke kanta sai kuma ta runtse idanunta ta miƙe da ƙyar tana ƙoƙarin zama ƙasan carpet ɗin wajan ƙafafuwansa ya yi saurin tare ta, ta hanyar kama hannunta ya zaunar da ita a gefensa kafaɗarsu na gogar ta juna.

"Wassh Abbiey jikinka ya jani" wuyanta ya bi da kallo da mamaki domin bai taɓa lura ba sai yanzu wasu yanka yanka ya gani kamar wacce aka saka reza aka tsatsaga mata fata ko aka karce ta, ta kasa kallonsa ya saka hannunsa masu taushi a saman haɓarta ya juyar da fuskarta ɗaya gefen wanda ya ƙone ga ɗan raguwar tabo nan ga wani karcewar ne. Ya saka yatsunsa biyu ya fara shafa wajan da son tantance mene.

Ridayya kamar wata wuta haka take jin yatsun Ustaz jikinta ya fara rawa ɗakin ya shiga juya mata ga wani murɗawa da mararta ta yi ta kumburu nan ta nan ta fara fitar da numfashi.

"Ya aka yi kika samu wannan ciwon Mimi?"

Baki ta buɗe da nufin faɗa masa cewa Zameer tsohon mijinta ne silar komai shike shaƙe mata wuya a duk sanda suke tarayya. Nauyin Ustaz da girman shi da yadda kullum yake cika mata idanu da kwarjininsa yasa ba zata iya faɗa masa cewa mijinta na baya ke shaƙe mata wuya ba idan zai nutsu har suma take wani lokacin, ta yi ƙasa da kanta zuciyarta na bugawa.

"Bana son tabo bana so ko kaɗan ina kika same su?" Ya faɗa yana juyo da fuskarta zuwa dab da tasa numfashinsa na sauka a kan tata fuskar.

Kasa bashi amsa ta yi jikinta na rawa ta fashe da kuka tana kifa kanta a cinya tare da yarfe hannunta kuka take sosai ɗaya hannun tana riƙe mararta. Ta kasa daurewa da abinda take ji bata saba da wannan sabon yanayin ba ji ta yi akwai abinda take buƙata idan bata samu ba zata iya mutuwa.
Ustaz ya zuba mata Idanu shi dai babu abinda ya yi mata ya miƙa hannu zai ɗago ta a firgice ta ce "Don Allah kar ka taɓa ni Abbiey ƙara mini azaba kake" Ya jinjina mata kai ya rasa mai ma zai ce bai ɗauka taɓarar Ridayya ta je har haka ba.

Ya zame a hankali zuwa ƙasan carpet kansa daidai cinyarta a hankali ya ce "Ok meke miki ciwo? Jikin ne? Mu je asibiti"

"Abbiey wallahi mutuwa zan yi na shiga uku, wani abu ke mini yawo a jiki marata ƙirjina wani iri Abbiey" Kuka take har da majina ta fita daga hayyacinta nan da nan kanta ya fara ciwo wani irin zazzabin ya fara rufe ta saboda abin yawa jininta girma ya fi ƙarfinta. Shi kansa Ustaz ya fara rikicewa bai kulata ba yama mance bashi da lafiya ya saka hannunsa duka biyun ya jawota zuwa ƙasa saman cinyoyinsa ta riƙe hannunsa da kyau jikinta kamar an jona mata wutar lantarki ga wata uwar zufa data gama wanke mata jiki.

Addu'a ya fara yi mata yana ɗan buga kumatunta "Wifey, Little Mama, Angel buɗe Idanunki"

Buɗe Idanunta ta yi ta zubawa fuskarsa Idanu musamman laɓɓansa ta saki wata ajjiyar zuciya mai ƙarfi ta yi saurin rufe idanun "Ban san meke mini ciwo ba Abbiey ka taimaka mini ƙirjina marata, Abbiey ina son....,"

MUNAFUKIN MIJITahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon