Page 11

554 51 9
                                    

A rikice Ridayya take kallon Mama, da alama ta kasa yarda da kuma fahimtar zancen nata. Mama ta ce "Wallahi tallahi bani da haɗi da wani Zameer, ba dangin iya babu na baba, ai asali da tushen shi yana ƙauye da ina jin? Almajiri ne sosai a nan makarantar almajirai ta Malam Iro, tun yana ƙarami dai da kashinsa a gindi aka kawo shi, ba kowa zai san ba ɗan Kano bane, tunanin kowa mune iyayensa"
Bakin Mama Ridayya ke kallo, ta kasa sanin ainahin inda zata zuba kalaman nata, har ta fahimta daidai. Da ƙyar ta buɗe baki ta ce "Mama kin gane wa nake magana akai anya? Mijina fa Zameer ɗan'ki"

"A'a gyara kalman bakinki, ban yi cikinsa ba balle na haifa na ba ki shi ki aura, bai kuma sha nonona ba, lafiya ras nake da alama kece tunaninki ya yi ƙaura daga kwakwalwarki, nutsuwarki ta bar gangar jikinki, Zameer Almajirin Malam Iro ne" Ridayya ta fara kallon Mama dishi-dishi hawayen da suka jima da yin hijira daga idanunta suka fara bin fuskarta ba tare data shirya zubar su ba, bakinta na ɓari da ƙyar take iya motsa bakin saboda ƙonan fuskar daya kame tare da tattare wa waje guda.
"Me ya sa Mama? Me ya sa kika ɓoye wa iyayena gaskiyar al'amarin? Kun rufe ni kun cuce ni"
Mama ta buga cinya ta ce "A'a a hir ɗinki wallahi kar ki kuma cewa mun cuce ki, idan akwai wanda ya cuce ki bai shige iyayenki ba, da suka kasa yin bincike a kan wanda za ki aura, sai kuma zuciyarki data zama kurma akan Zameer ɗin, don me ake cewa a yi bincike kafin aure? Ai saboda irin haka ka je ka auri ɗan fashi ko kidnapa babu uban wanda ya sani, kinga ni fice mini daga gida kada ki saka bakina ya yi tsini" Kuka Ridayya take kamar ranta zai fita wannan wanne irin lamari ne? Ikon Allah da ƘUDIRAR ALLAH ke riƙe da rayuwarta a yanzu. Waye Mijinta? Ina ne garinsu mene mafita? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un.

"Mama kin cutar da rayuwata ki sani Allah ba sai bar ki ba, na san ba za ki so a yi wa ɗiyarki dake gidana haka ba, domin aure ba abin wasa bane" Sheƙeƙe Mama ke kallon Ridayya kafin ta ce "Wacce ƴar rawa ce a gidan ki?"

"Khairiyya!"
Ta bata amsa a raunace ƙirjinta na ɗaga wa sama, kamar wacce Asthma ke shirin kama ta. Mama ta ce "Tab, wata aba ce haka kuma? Bani da wata yarinya mai irin wannan sunan nikam" Dam! Ƙirjin Ridayya ya bada sauti juwa na ɗaukar ta, ta sulale a wajan tana riƙe da ƙirjinta sunan Allah take son kira ta gagara furta komai. Ganin haka ya saka Mama figar hannunta ta ce "A'a ba za ki mace mini a gidana ki ja mini jarfa da zunɗe, ke da can ba ki yi tunani da nazarin wanda kike tare da shi ba sai yanzu da masifa ta faɗa miki? Ni duk wani Almajiri nawa ne ba ruwana da sanin waye shi" Ta hankaɗa Ridayya waje ta rufe ƙofar gidan. Tana faɗin

"Yaran zamani da masifar kwaɗayin abin hannun samari, da shegen iyayi da kinibibi da kunga namiji yana murza shadda ya kafa hula kyakkawa da shi sai ku liƙe masa? Ba kusan kura ce da fatar a kuya ba, yawanci cima zaunane masu burin tsiya, su kuma iyayinki ganin Allah ya rufa musu asiri suka bashi ke da tunanin ya cancanta, ko kuma tunaninsu arziƙi gare shi?" Ta yi ƙwafa tana komawa tare da zama ta ci-gaba da yanka albasa da kabejin awarar daren da take yi almajirai da ƴan unguwa na siye, ta girgiza kai ta ce "Ai bada kuɗi ne kawai arziƙi ba, hadda miji na gari a wannan zamanin arziƙi ne, ni kuma mene nawa? Kuɗi kawai ya biya ni ya ce na yi masa komai a matsayin uwa" Haka kurum ta ji kamar bata kyauta ba na ɓoye gaskiyar waye Zameer da ta yi, kila a kyau masu sonta wanda suka fishi nagarta da komai, idan ta tuna kuɗi ya bata fa sai ta ji ko a jikinta. Ta share batun Ridayya tare da ci-gaba da aikin gabanta domin a yanzu bata da wani abu daya dameta.

Ƙafafuwanta kawai take cillawa ba tare da sanin inda take saka su ba, wani irin duhu ne ya mamayewa idanunta jiri na ɗaukar ta tare da ƙoƙarin yasar da tsamurarren jikin nata, har ta ƙarasa tsakiyar titi bata sani ba, dukda irin horn da masu abeben hawa suke mata. Wawan burkin da aka ja, da kuma sauke mata lafiyayyen marin da aka yi ya saka ta dawo cikin hayyacinta mutumin daya fito daga cikin mota ba shiri ya ce

"Ke wacce irin mara tunani ce da za ki zo tsakiyar titi kamar kin samu hanyar gidan ubanki, e?" Wani ya leƙo daga mota ya ce
"Da ka yi mata afuwa bana jin data da cikakken hankali fa, ko babu komai a girme ta girmeka sai ta ci albarkacin hakan" Cikin kumfar baki ya ce
"Matsalar ta ce wannan kuma hauka ai bani na ja mata, irin su ne masu yawa mutane bala'i"

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now