Sai Lokacin kuma Abun yayi mata Shar cikin Ranta Da Sauri ta Mike tana Salati Cikin Ranta Tuna Abdullahi baya som Miyar Nika yafison kuma na Jajjage,ita kuma Abunda yaasa bata Jajjaga ba Taga kayan Miyan yana da yawa ne Bata iya zaman Jajjagasa Shiyasa takai Nika ajiyar rai ta Sauke afili ta Furta.."Fada ne da korafi yau zan Shashi Acikin Gidan nan Har sai na Godema Allah.."

Yunusa na Dawowa Daga kai mata Nika ya karbo mata ta Bashi Abun karyawansa Bayan ya gama ta Bashi Sakon Danmagaji tace ya Siyo mata kayan Lambu,Kabeji,da caras,sai Cocumber,Tana so tayi Cowslow ne kuma Ta Duba Cikin Fridge dinta Duka sun kare,Bama kadai Gareta sai kwai kudin Mota ta bashi Tace yayi Sauri ya Dawo yana Fita ta Dauki Tsintsiya ta Share Tsakar Gidan Tas ta kwashe Dattin Takai Bola aranta Tana Fadin kafin yunusa ya Tafi zai Zubda da Sharan Domin Ta Taru da yawa.

Yunusa bai Dade ba ya Dawo koda ya Komo har ta Gama Miyarta,Already dama Tana da Sauran Naman Jiya da Abdullahi ya Zo Dashi batayi amfani Dashi Duka ba sai tayi amfani da Sauran yau,Ruwan Farar Shinkafa ta Dora,Sauran gawayin Safe ne bai kare ba,Ta bama yunusa Hamsin ya karo mata kada ya yanke mata kuma Babu kowa Sallaman yunusa tayi ya Tafi makaranta yace mata yana da Rubutu sai Zuwa anjuma zai zo ya karbi abincinsa Dayake makarantar Allon nasu kusa ne babu Nisa Sosai.

Kokafin 12pm na Rana Hafsah ta Gama Komai Ta kwashe Cikin Kula,Cowslow ne din ne Bata Hada ba sai Zuwa anjuma Gudun karya ya Lalace,sai da ta gama yanka komai ta wanke ta Adanashi acikin Kitchen dinta,Dama ta saka Ruwan zafi Cikin Kittle ta juye tayi wanka Dashi ta Sauya kaya Zuwa Atamfar wata Doguwar Riga,Falo ta Dawo tazo ta kunna kallo Tashar africa Tv ta saka Tana kallon Wa"azi Domin Hafsah kallo bai Dameta ba har gwara ma India tana kallonsu akan Hausa Film.

Sallar azahar ne ya Tada ita ta Tashi ta Shiga Cikin Bedroom dinta ta Dauro alwala tazo Tayi Sallah,Ta idar da sallar kenan tana Addu"o'inta Taji wayarta na neman Dauki Daga Falo da Sauri ta Shafa Addu"arta ta Fito Falo ta Dauki Wayarta Ganin Sunan mai Kiran yasa sai da Gabanta ya Fadi Abdullahi ne.

Tana Gabda Katsewa Ta Daga Kiran Tana mai sallama Dagachan Bangaren Abdullahi yace"Yau kuma wani Salon Wulakancin kika sake samu Hafsah...?

Ido ta Runtse kafin tace"Wulakanci fa kace Abban Amira..? Kai tsaye yace"Eh mana Banda Wulakanci kinaji ina Kiran Wayarki ammh Saboda ki Kaini Bango sai da kika Ga Dama zaki Daga Kiran nawa."Batace komai ba kawai tamai Shurun jin Shurunta yasa yace kara Fadin"Au kina Jina ina mgana Shine kika min Banza.."Hafsah tace"Ba banza na maka ba Jira nake kagama Fadan naka sai na Baka Hakuri na kuma gayamaka Cewa Lokacin daka Kira ina Sallah ne.."Jin Haka kuma sai Jikinsa yayi sanyi Sai kawai yayi kwafa yana Fadin"Dama kiran  Saboda Nace miki in Lokacin Tashinsu Amira yayi Daga makaranta ki Kulle Gida kije da kanki ki Daukosu mai Mashin dinsu yau bai Fita aiki ba yana Gida Baya Jin Dadi ni kuma aiki yayi min yawa Bazan samu Lokacin Zuwa na Daukosu ba.."Yafada Cikin Sanyin Murya Cikin Sanyinta tace"Shikenan...Allah ya kaimu zan je na Daukosu in Lokacin Tashinsu yayi.."

Daga Haka bai kara mgana ba Tana Shirin yanke wayar Taji yana Fadin"Akwai kudi a hannunki ne..?kai Tsaye tace mai"Eh akwai.."Bai Tsaya jin wani mgana ba ya katse Kiran Ajiyar Numfashi ta Sauke kafin ta Ijiye wayar nan saman kujera Ta koma ta Zauna tana kada kai,gefe Daya kuma Jifa Jifa Takan maida Hankalinta Wajen Tibi.

2pm na Rana Daidai ta Saka Babban Hijabinta ta Dauki Wayarta da Kudi Cikin yar karamar pos dinta ta Fito Bayan ta Kulle Gidan,Adaidaita ta samu ya Dauketa har makarantansu Amira wato Alhazawa Acadamey Zaria,Amira tana primary 1 ne Shi kuma Amir yana Nursery 2 ne,Shi karfe 1pm na Rana ake Tashinsu su Amira kuma 2:10pm ake Tashinsu,In Abdullahi yakaisu da Safe in an tashesu wani mai mashin nan yake makotansu Abdullahi ya Dauka yana Biya Duk wata yana zuwa yana Dawowa Dasu Amir zai Jira Har atashi su Amira a Daukosu Tare,Sai da ma ta jira aka tashesu kana ta Shiga cikin makarantar har ajinsu Amir suka gaisa da malamansu ta Daukoshi Dayake tana zuwa Daukosu Wani Lokacin in Wata mtsala ta Faru haka Amira kuma aharaban makarantar da Ganta Tashinsu kenan Ta Riko mata Hannu suka Tafi Mai adaidaitan nan nan dama tace ya Jirata ya maidasu sai ta Bashi kudinshi Gabadaya.

MASIFAFFAN NAMIJI..!Where stories live. Discover now