016

1K 110 11
                                    

*MASIFAFFAN NAMIJI..!*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*

*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!

_*Wannan Shafin ya Tafi ne kai Tsaye Zuwa ga Hazikan marubuta Masu Nuna min Kaunarsu Afili,Hakika Bakina yayi Kadan Wajen Nuna musu Godiyata....Ina Kike MY JIKA KAUSAR AGLAN NISSA,dake HASINA AUTAR MANYA,Sai ke My Mom DEEJART,ina kike FATIMA FATNOOR,Da ke kanki Kanwata NIMCYSARAUTA,Bazan Manta Dake ba FAUZIYA S MADAKI,Da ke kanki  My Habibaty AISHA IDRIS ABDULLAHI...Dukkanku ina Rokon Allah yayi Riko Da Duka Hannayenku Wajen Rubuta alheri..Alherin  Allah yakai muku adukkan Inda kuke Ku sani ku Kara Sani Ni Janaftyshakira Kuna Burgeni...*_

*016*

"Duka yanmata Hudun ajere suka Shigo Kowacce na Bin Bayan yar"uwanta Cikin Shiga ta alafarma da kece Raini na musamman kowacce tana Tashin kamshi da Gayunta na musamman wanda take ji Har acikin Ranta itace zatayi nasaran samun Zankadeden Miji irin Abokin yayansu Salisu.

Barkat Itace Babbansu Itace kan Gaba Doguwar mace ce mai Fadin Fuska da Dara Daran Idanuwana Farace tas kamar atabata Jini ya Fito Tana da Dirin Jiki na Mata Daidai gwargwardo,Itace ke Bin Salisu Duk da akwai wata tsakaninsu Sadiya Allah yayi mata Rasuwa,Barkat Tana aji uku ne a Abu Samaru inda take karantar Micro Biology,Tana kuma sanye ne da Wata Ubansu Doguwar Rigar leshi wacce aka mata Dinkin A Shape ya kama ajikinta Sosai sai Daurin Maryam babangida Datayi ta yane Jikinta da wani Siririn gyale Fuskarta yana Fitar da wani Annuri wanda Daga gani kasan Haka baiwarta Take ammh kuma Daga kallonta zaka Fahimci bata da yalwar Fara"a kamar Sauran kannenta,akallah a shekaru bazata wuce Shekaru 25 aduniya ba ammh Fuskarta da yanayin Tsarin Jikinta ya Boye Duka Shekarunta.

Sai Bahiya wacce ke Bimata Itama Farace sosai sai Doguwar Fuska gareta Mai Dauke da madaidaicin Hanci da kuma Karamin Bakinta,Idanuwanta basu kai na Barkat ba,Ita nata suna da kwarmin Sosai Sudan Shige kadan itama Tana sanye Cikin Riga da Sikat na Atamfa tayi Daurin Ture ta bazo gashin Dokin datayi kari Dashi ta baya Bayan ta saka wani Mayafi baki ta yane kanta Dashi,Bahiya tana Abu ne itama aji Biyu Tana karantar Computer Science ne akallah a shekaru zatayi Shekaru 23 aduniya,ita tana da Fara"a soaai Domin Duka Fararan Hakoranta Suna Washe ne,sabanin Barkat da Ko Burbushin Fara"a bashi a saman Fuskarta.

Sai Ta ukunsu Bahijjat,Itama Farace Kamar sauran ammh bata kaisu haske ba,sai dai bata da Diri Sosai Sirintantan ya Fito Sosai,tana da kyau Ammh kuma Fuskarta Doguwa ne,haka Karan Hancinta,itama karatu take a poli tana Nd2 tana karantar SLT,ashekaru bazata wuce 20 aduniya ba sai Karamarsu Aina ita kuma Yarinya Sosai Ammh bata da Haske kamarsu Black beauty ce,Tafi kyau ma sai dai Bata da Tsawo Gajera ce Sosai,tana Shekaran Karshe a makarantar Sakandiri ta yanmata Dake basawa Ashekaru bazata wuce 18 ba in ka kalleta ma zaka Fahimci yarinyartar sosai itama taci kwalliyarta Sosai Duk dama Hajiya ce ta matsa mata sai tabi Jerin yan"uwanta ammh ita sam Bata Ma Fatan tayi Aure yanzu Shiyasa ma bata damu kanta ba kuma Tana Fatan Insha Allahu ma baza"a zabeta ba Tunda ga Na sama da ita su Anty Bahiya.

Duk acikin Mintunan da basu gaza Goma ba Nazifi da Abdullahi Suka karesu musu kallo Dama already Salisu yayi musu Bayanin Sunayensu da kuma matakin karatun kowaccensu Shiyasa suna ganinsu suka Tantance kamannin kowaccensu,Su kuwa Dukkansu zama sukayi saman Kujeran Dake Fuskanta Abdullahi da Nazifin kansu na kasa kowacce da Abunda take sakawa acikin Zuciyarta,bayan sun Hada baki wajen gaishesu Cikin Girmamawa.

Abdullahi ya waiga ya kalli Nazifi Shima ya kallesa,Kana Abdullahi ya maida kallonsa kansu yana amsa gaisuwan nasu Cikin kulawa Da Sauri Barkat ta Dago Idanuwanta sama suka Hada Ido Hudu da Abdullahi Lokaci Daya taji gabanta ya yanke ya Fadi,Shi kuwa Kansa ya dauke sama yana Fadin"Sannun ku da Fitowa yan mata.."Yafada batare Daya Shirya Fadin Hakan ba ganin Nazifin yayi Shuru yaki Cewa komai.

MASIFAFFAN NAMIJI..!Where stories live. Discover now