Episode 2

185 10 0
                                    

.👩‍🦰👩‍🦰👩‍🦰👩‍🦰
KANKI KIKA CUTA
👩‍🦰👩‍🦰👩‍🦰👩‍🦰
👩‍🦰👩‍🦰
👩‍🦰
(Tsantar cin amana)

Story and ✍️Writte by
KHADEEJAHT HYDAR
(Young Novelist)

From the experience writer of

*IHSAN.
*UQUBAR UWAR MIJINA.
*WATARANA SAI LABARI.
*PRINCE AIRAN AND MAIMOON.

AND NOW
*KANKI KIKA CUTA*

Dedicated to My Future.

Free Pages.
Episode Two
(My Story)

Wacece SALEEMA TAMEER kuma miye dangantakarsu da SALEEM TAMEER?

ALHAJI TAMEER KHALID ADAM babban malamine acikin garin jigawa a wani ƙauye da'ake cema ku'it,fatauci da almajirancine yakawo shi Nigeria amma shi ɗan asalin ƙasar YAMAL ne,yanzu haka kuma shine mai garin garinnasu.

Alhaji Tameer yazo da matarsa ɗaya balarabiya kuma ƴar uwarsa mai suna Khairat da ƴaƴansu huɗu biyu maza biyu mata.

Babbansu sunansa Sufyan sai Naseer ,Hafsa se auta Saleema.

Suntaso cikin so da ƙaunar juna gasu kyawawa abin sha'awa,tsabar kyawunsu yasa makwabtansu ke cema ƙauyen garin kyawawa.

Hafsa da Auta Saleema sunyi aure acikin garin dutse inda rana ɗaya aka musu aure.

Bayan aurensun su Hafsat ne Alhaji Tameer ya auri wata bafulatana mai suna Hajara inda suke zaman lafiya da mutunta juna da Khairat ba fada.

Gashi ɗan kasuwa arzikinaa sai ɓunƙasa yake don yanzu yana cikin manƴan jahar jigawa,ga masha Allah ya tara iyali masu haɗin kai da ƙaunar juna.

Bayan su sufyan da ƙaninsa Naseer sungana makaranta ne suka ziyarci danginsu na yamal,sunsamu tarba mekyau inda suka zaga dangin Mamansu da Babansu saboda suma duk haɗin gidane.

A yawon ganin dangine Sufyan yasamu matarsa mai suna Aisha,hakama ɗ'anuwansa Naseer yasamu tasu mai suna Zainaba.

Bayan aurennasu suka dawo Nigeria da iyalinsu suka kuma kama kasuwanci gadan-gadan,inda Allah yasa musu albarka aciki.

Sannu a hankali Sufyan yafara zuwa lagos kasuwanci,kadan-kadan har Allah yazaunar dashi acan saboda kowa de yasan a Africa lagos yafi koina harkar kasuwanci,inda shi kuma Naseer yana jigawa cikin garin dutse .

Saida aurensu yacika shekaru goma tukun Allah ya azurta Alhaji sufyan da Aisha da ɗa namiji suka sa masa Saleem,Alhaji Naseer kuwa saida Saleem ya shekaru goma a duniya tukun sukasamu haihuwar ƴa mace suka sa mata Saleema sunan ƙanwarsa.

Cikin ikon Allah Naseer ya dawo lagos da zama kusa da ɗanuwansa suka siya gida mai part biyu acikin garin lagos Eko wanda ake musu laƙabi da Ikko ikon Allah,unguwace kamar estate ba hayaniya,anan suka tare da matansu suna zaman lafiya.

Dawowarsu lagos yasa Saleema yakoma gidan Uncle ɗinsa wato mahaifin Saleema saboda yanason yara kuma ga Saleema a gidan ,gata da shiga rai ga kyau.

Tun tasowarta da Saleem tafara wayo ko kuka take tana ganinsa saitafara dariya kullum tana gunsa,lokacin daza'a yayeta aka kaita gun Mummyn Saleem ,tundaga lokacin har yanzu datake shekaru sha biyar bata sake komawa gun Mummyntaba iyakacinta da'ita taje tagaisheta,shima Saleema haka shida Mummynsa saide yaje ƴagaidata kenan sunyi musanyan yara,amma fa dukda haka kulljm suna tare inbaije ganintaba ita taje gunsa,shaƙuwace sosai a tsakaninsu saboda ko abundayashefetane kafin tagayawa su Mama sai Saleem yaji,batajin kunyarsa saboda komai ma faɗamasa takeyi,dukda ba zama na dindindinba yake a lagos yana karatune a universiry sule lamiɗo dake jigawa yana karantar accountant,kuma yanzu haka shekarunsa ashirin da uku,kenan tsakaninsa da Saleema Eight years kenan,yakanzo lagos hutune,kuma duk lokacin daya tashi komawa sai anyi drama da Saleema wacce take JSS 3 .

Yanzu haka yazo hutune inda next weeƙ zai koma kuma ya rasa yadda zai faɗamata zai koma,don yasa ranar akwai daru.

Zaune take akan motar abbanta fuskarta a murtuƙe ,tana sanye da riga da wando rigar har knee ɗinta ,tsayuwar mota ce tasata ɗagowa wanda hakan yabani damar kyaremata kallo.

Saleema yarinyace kyekkyawa ajin farko,batada haske sosai tanada madaidaicin baki da manyan idanuwa wanda cikinsu yakeda launin brown,saman lips ɗinta pink ne ƙasan kuma baƙine kamar de wacce tashafa janbaki,haƙan ya ƙara mata kyau, ga goshinta gashine akwance lub-lub ga sajenta kamar na maza ga girarta kamar anmata carving,ga hancinta dogo dai-dai da siririyar dogon fuskarta,tana da tsayi sosai ga batada jiki sai shape me kyau,infact fan kunsan jinin larabawa ba bayawa ba gun kyau,Saleema is attractive,duk inda tashiga ana sonta sosai, hakan kesa aminiƴarta wacce tayarda da'ita yimata hassada da kyashi ,da kuma mugun ƙudiri akanta.

Haleema ƙawar Saleema ce wacce suke unguwa ɗaya da'ita,sun shaku sosai ƙomai tare sukeyi wanda haƙan yasa har iyayensu suke zumunci.

Saleema matashin saurayine ɗan shekara 23,kyekkyawane sosai suna kama da saleema sosai,yanada tsayi shima ga dogon hanci da dogon fuska mai kyau,ga sajensa sirieiyi dai-dai da fuskarsa gashin kansa kuwa lub irinna larabawa,kana ganinsu kaga TAMEER FAMILY a koina kagansu zaka ganesu,kuma suna anfani generally da sunan kakansu ne wato TAMEER.

Ɓangaren halayya kuma duk sunada fara'a ɗukda kasancewar Saleema miskili shi fara'arsa to a gidane ko kuma agun saleema,itakuwa Saleema akwai son mutane saurin yadda,akwata da saurin fushi da saurin sauƙa amma fa in abu yabata mata rai sosai akwai wahala,shikuwa Saleem baicika fushiba amma inyayi ba kyau,inkanason kaga ɓacin ransa to kataɓa Saleema.

Ƙawar Saleema ɗaya wato Haleema,shikuwa abokinsa ɗaya Muhammad yayan Haleema,ajinsu ɗaya da Haleema har seat ɗinsu ,zuciya ɗaya take zaune da Haleema amma itakam akwai wata aƙasa.

Ana gobe zai koma yasamu Mumynsa yace"...dan Allah mum kitayani faɗawa Little zankoma makaranta jigawa gobe,baki ta riƙe tace"....lalle nice zan faɗawa Saleema tafiyarka taɓ badainiba kajira tana ciki inta fito kwayi magana,tashi yayi yana cewa a'a ni banda wannan ƙarfin halin,haryakai ɓakin ƙofa yaji muryar saleema cikin sanyi tana cewa Yaya tafiya zakayi kabarni?,murmushi yayi yace"...a'a Little batafiya zanyiba nazo gaida Mama ne,batace komai ba ta juya tanufi ɗakinta tafaɗa gado sai kuka"...

Mama tace"...yau fa antaɓota ba bacci ai saikaje ka lallaɓata kafin tayi kuka yasamata zazzaɓi,ɗakinta yashiga yasameta tana aikinta wato kuka,a hankali yace"...Saleema please tashi muyi magana dan Allah don't cry bazan daɗeba zan dawo kinji,tashi tayi harda shasheƙa tace"...Yaya banaso katafi don Allah ka zauna ko kuma ni inbika,hannunta yakama yace"....haba little u are not a baby fa,ko yaushe inzan tafi saikinyi kuka kisama kanki ciwo,u don't really know how i feel leaving you here,it hurt me and u know i will like to spend lifetime with you"..

Tana shashsheƙa tace"...to yaya nadaina kuka promise me zakana ƙirana kullum harda vidio call,murmushi yayi yace"...that's why i bring this for you,ya miƙa mata wata sabuwar iphone 11 pro yace"...take this and promise me u will concentrate on your study banda kai waya school and again karki bar waya taɗauke miki hankali"...

To ta amsa amma still fuskarta ba walwala,fuska ya shagwabe yace"...haba Little love yimin dariya mana,murmushi tayi tayi hugging ɗinsa tace"...i love and will miss u ya Saleem ,youe little Mrs Saleem will miss u,yana murmushi yace"...yes Mrs Saleem surely i will miss you,don yasan tana bala'in son ace mata Mrs Saleem"...

Washegari Saleem yayi shirinsa tsaf Mrs Saleem tasasa a gaba tana kallo,kallonta yake yana kissima irin son dayake mata,jakarsa ya ɗauka yafara ja,ita kuma tana biye a bayansa,a bakin motar dazai kaisa park suka tsaya hardasu Mum.

Kamar ta dake har yashiga mota har motar tafara ja kawai tasa kukan da take ta riƙewa ,dama nasan za'a rina cewar Mamanta,tsayar da driver yayi Mama tace"...Saleem karka fito kayi tafiyarka,inaa bazai iya tafiyaba fitowa yayi shima kanar zaiyi kuka yace"....please kidaina kukan nafasa tafiyar yau sai next week,da mamaki suke kallonsa Mama tace"...banson shashanci maza shige kuje,kamar yayi kuka yace"...dan Allah mama kibari nafasa tafiyar kallifa kuka takeyi,dakyar yashiga motar bayan su Baba sun saɓawa dagashi har Mrs Saleem ɗin.

Kudai kuci gaba da bin Young Novelist.
This novel is not for free,,pay and read.
Musa Khadijat Nana
0029001824
Unity bank
Then kanuna shaidar biyanka ta whatsapp ɗina,,07069688588
Ko kuma katiɓ MTN ta wannan number,,07061651640
🔥🔥🔥🔥
Young Novelist
🌼🌼🌼
Royalty
👩‍🦰👩‍🦰👩‍🦰
Autarsu.

Vote and follow as u read

KANKI KIKA CUTAWhere stories live. Discover now