Episode 41

92 4 0
                                    

👩‍🦰👩‍🦰👩‍🦰👩‍🦰👩‍🦰
KANKI KIKA CUTA
           👩‍🦰👩‍🦰👩‍🦰
             👩‍🦰👩‍🦰
               👩‍🦰
(Tsantsar cin amana)

Story and 🖊️written by
Khadeejaht Hydar
(Young Novelist)

From the experience writer of.
.*IHSAN
*UQUBAR UWAR MIJINA
*WATARANA SAI LABARI
*PRINCE AIRAN AND MAIMOON.

And now with the heart touching one.
KANKI KIKA  CUTA

  
Vote and follow me on wattpad
@YoungNovelist4

Blog:https://khadeejahthydaryoungnovelist.blogspot.com/?m=1

My Facebook Group
https://www.facebook.com/groups/228916361333651/

My twitter link
https://twitter.com/YoungNovelistII?s=09

My Instagram
Khadeejah Hydar Young Novelist.
Follow nd show love??

DEDICATED TO
All member of Hydar and Muhammad's Family.

SPECIAL GIFT TO
Anti Zainab Muhammad

Vote nd read via this link on wattpad
https://my.w.tt/ZxkqnOOO2bb

Like, join and comment to read this novel from page one.
https://www.facebook.com/Khadeejaht-Hydar-Hausa-Novels-YoungNovelist-101121485268631/

Episode Fourty One
Honeymoon I

Koda muka koma gida da kanshi ya share ko'ina sannan ya daura mana gorki,dukda naji sauƙi haka Saleem yahanani aiki,simple girki yamana,taliya fara da sauce ɗin hanta sai ƙamshi yake,sai coconut juice kofi ɗaya ya zubo,tunda naga haka nafara kumbura fuska da turo baki don nasan cewa zaiyi bazansha ba ina period,da kanshi yabani abinci bai damu da yadda fuskata takeba,saidana ƙoshi sosai tukun yabani ruwa nasha shima yafara ci,a maimakon dayagama ya kora da ruwa sai ya kifa kai akan juice ɗin mai sanyi da shiga rai ya shanye sai ɗan kaɗan daya rage,da murmushi yakai kofin bakina ,nikuwa na cire fuska cikin yanayin shagwaɓa nace"Yanzu Sahab saida kashanye zakabani,yace"kema fa kinsan ba kyau shan kayan sanyi ana period inbadon ina sonki bama ai bazan baki ba,ko kallon kofin ban sakeyiba na kwanta akan kujera ina turo ɗan ƙaramin bakina,shanyewa yayi sannan yakai kwanukan yadawo,cikin baccin dayafara ɗaukarta Saleema ya sunkuceta yana mata dariya ya nufo ɗakinsa da'ita, a hankali tace"Allah mutum ya sauƙeni banaso,yace"ni inaso Nuree,akan gadonsa yamata masauƙi sannan shima ya kwanta,mirginawa tayi ta haye jikinsa tayi lub kamar mage shima zagayeta yayi da hanneyensa ,nan danan bacci yayi gabs dasu sakamakon jiya da ciwon Saleema ya hanasu bacci.

Innalillahi wa inna ilahir rajioon Mama!Mama!!Mama!!!kizo yaron nan baya numfashi,Mama nashiga uku baya mosti,da sauri ta shigo ɗakin tace"ke Haleema meya samesane kike ta ihu,cikin kuka tace"Mama taɓasa jiki yadaina motsi,taɓasa Mummyn tayi tace"Innalillahi Haleema ai yaronnan ya ras...ai bata ƙarasaba Haleema tafaɗi sumammiya,kotakan ɗan batabiba tahau neman ceton ran ƴarta,dakyar tasamu   Haleema ta farfaɗo tana kuka,Mummy kuwa a ranta hamdala take akan gwara da yaron ya rasu a huta da musu gori,lallashin Haleema tahauyi,daga baya aka ƙirasu Daddy da Muhammad harda Abban su Saleema akakai yaron  gidan gaskiya.

Sanadiyyar mutuwar yaron Haleema tayi sanyi ta yadda duk wasu makaman yaƙinta ta koma ga Allah,ko fyaɗen da aka mata da haihuwar yaronnan kawai sun isheta ishara dasanin cewa ɗan Adam bai isa yayi ma wani abinda Allah bai rubuta masaba,taso cutar da Saleema amma Allah ya nunamata isa da ikonsa,wlh duk wanda Allah yaso kaikuma kakeƙi kana cikin babban tashin hankali dayin nadama mai yawa,wani gamin tayta kuka ita kaɗai,tasan ita sam batayi dacen uwa tagari ba,,uhm Allah yasa masu laifi suna gane laifinsu suna tuba.

A kwana a tashi ba wiya a gun Allah inda yau komawar Saleema gidan Saleem keda wata huɗu,soyayya da  shaƙuwa mai ƙarfi ce ke sake shiga tsakaninsu,inda ɗaya baya iya yin wani abun batare da ɗan uwan saba.

KANKI KIKA CUTAWhere stories live. Discover now