Abun Alfahari Na✅

By teemahcutey72

18.6K 1.5K 537

🌹Abun Alfahari na labari ne wanda ya k'unshi abubuwa daban daban na rayuwa...... labarin wata yarinya mai su... More

Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
END✅
Fashin Bak'i
Life Goes On
Words of Comfort
Advertisement

Chapter 35

276 20 2
By teemahcutey72




🧚🏻‍♀Abun Alfahari Na🧚🏻‍♀
           By
🌹Teemahcutey 🌹

Page 35.
*

*~DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI~*

::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Zaune take tana tinani tare da juya wayar da ke hanun ta, a ranta take fad'ar to wannan wacece da tasan sirrin ta haka? Tambayar da take yiwa zuciyar ta kenan ba mai amsa mata.

Murmushi tayi kawai tare da danna wa number kira, ai kuwa cikin sa'a wayar ta shiga, amma kashhh!! Wayar har ta gama ringing ba'a d'aga ba.
A b'angaren Abrar kuwa wanka take shiyasa bata d'aga kiran ba, jin k'arar wayar tata ne yasaka a gurguje ta fito daga wankan.

Ganin number da ta kira ta seda taji wani irin dad'i. Batare da 6ata lokaci ba ta danna wa wannan number kira.
Bayan Zeenatu ta d'aga ne suka gaisa kowanen su cikin isa da izza... y'ar magana sukayi daga nan suka yanke hukuncin had'uwa kawai dan tattaunan wannan lamarin.. nace hmmmm.

A gaggauce Abrar ta shirya domin a yau ne suka aje zasu had'u saboda tsananin zumud'i da rashin hak'uri, da son tarwatsa rayuwar wasu.

Bayan ta fito ne though a yanzu Mommah bata cika zama gida ba, saboda kusan ita ke jinyar gwammah..

daga Meemee se Abrar ne a gidan.
Futowa tayi a shirye tsafff....

(Dama Mommah takan arawa Abrar motar ta sometimes saboda kada taji wani abu tunda Meemee nada motor.. sosai Mommah take k'ok'arin sakata ajiki saboda ta d'auka da gidan su da nan ba banbanci,so 2days inan Mommah bata zuwa da motar ta a asibiti sedai Poppah ya kaita. Ta na nan ajiye gida)

Direct key in motar ta d'akko tacewa Meemee zata d'anje unguwa, "ummm" kawai Meemee tace domin gani take dai a yanzu kamar bata ra'ayin ta, so bata son tana shiga lamarin ta kwata kwata.

Parking lot ta nufa tare da tada motar, me gadi ya bud'e mata gate ta cillah ta kan titi..

Kasan cewar Ammie bata nan taje gidan marayu kai taimako shiyasa Meenah ta fito a parlour a bunta ta kunna TV ta saka ST NOVELLA tana kallan series inan BLOOD SISTERS, sosai ta shagala gurin kallan series in tana yi tana cin popcorn, bata san da zuwan Captain ba kawai taji mutum a tsaye kanta, aikuwa wani irin super tayi ta koma d'aya b'angaren domin tasan Allah ne ya cece ta ya gwada mata shi da tuni taji rankwashi a kai.

" wayo Allah nikam Allah ya jarabeni"

Captain da ke tsaye yace "mye kika ce?

" cewa nayi Allah ya jarabeni ya baby nikam ban da shak'at? Wlh fa duba ka gani ga hular nan a kan hanun kujera fa kwanta wa nayi shiyasa ta zame, kuma shikenan mutum ba yada ikon sakewa ya bud'e kan shi ya sha iska? Ni Allah ma ya taimake ni nayi kitso, nasan da a banye yake da tuni ka chafko wutsiyar gashin"

Shikam Captain a yanzu he's already use to irin yawan zancen da take zubawa cikin k'ank'anin lokaci.

Kwafa yayi tare da d'an takawa, ai kuwa tashi tayi ta k'ara matsawa domin bata yadda da shiba.

Dariya Fahad yayi tare da fad'ar "oya baby come here kyaleshi"

Meenah kam tsayawa tayi kamar gauluwa tana kallan Fahad.

Kwai kwayon muryan shi tayi ta fad'i abunda ya fad'a,.. daga bisani se ta kwashe da dariya tana nunashi.
"Wai baby come here kyaleshi... kamar wata k'aramar yarinya..... dariya ta k'arayi tana nuna shi tace "lallai kana ruwaa"🤣

Shima kallan ta yake yana 'yar dariyar yak'e domin kuwa yasan ta sakammai shi.😂

"Kee!! Ashe bayan duka rashin kunyar da kikeyi ashe hadda raina mutane kikayi? Ki kama kanki fa baby Allah zanyi maganin ki, dan kawai kinga banasan miki fad'a koh? Zan..

Fahad ya katseshi ta hanyar fad'ar " come on buddy ai wasa ce take ya fad'a yana dariya domin duk da haka ta bashi dariya"

"Wallahi nikam ai ya baby ba raina shi nayi ba ai, kaima abun ai ya baka dariya ko?

"Kauda kanshi yayi yace oya get lost yanuna mata hanyar stairs"

"Chabbbb Yaseen ba inda zani... haka kawai ina kallo na a kore ni ? Yo ai mutum ba nan ne side inshi ba aii, kuma wollah mutum ya koran ta k'arfi Ammie ta dawo gidanan hmmmmmm base na fad'aba"

Shikam mamaki ya cika shi domin a yanda yake hasashen sauran halayen ta tsaffff zata iya aikata dik abunda ta fad'a

Be ce mata komai ba kawai ya zauna.

Dawo wa tayi safff safff ta zauna inda ta tashi.
D'aukar hular ta tayi ta saka tare da k'ara Volume.

Afrah data kammala k'ure wanka tayi makeup tayi kyau matuk'a. Sashen su Ammie ta nufa tana wata tafiya kamar wata shu'uma.

Shigowa tayi a parlour ba tare da tayi sallama ba, Meenah da ta riga ta hango ta tana tunkaro gurin su, d'aga murya tayi tace;
"Malama ya zaki shigo mana haka zak'au ba sallama?

Su Captain da basu kai da ganin shigowar ta ba hankalin su ya koma inda Meenah ke kallo.

Shikam Captain ya d'auka ma Ammie ce domin yanzu tsoron ta yake akan komai zata iya🤣 ( nace anya kuwa zata iya yiwa Ammie haka?)

Ganin irin kallan da Captain ya tsareta dashi yasa ta koma domin yin sallama.

Sallamar tayi suka amsa tare da k'araso wa gunsu.
Ita kam Meenah anyi abunda takeso. D'auke kanta tayi daga gare su ta cigaba da kallon ta.

Ta kujerar su Captain tabi tare da lankwasa murya ta gaida shi.
Amsawa yayi tare da kallan ta, 4eyes sukayi a take gaban shi ya fad'i.. be d'auke idanun shi daga gare ta ba hakan yasa tayi wani shu'umin murmushi.
Zagaya wa tayi ta zauna a d'ayar kujera..

Dumm dumm!! shine sautin da gaban Meenah ya bayar alamun fad'uwar gaba, juyowa tayi ta kalle Captain da ya tsare Afrah da kallo, haka ma ta juya ta kalle Afrah da take wani mugun murmushi.
tashi tayi zumut taje gun Captain, kusa dashi ta zaune ta rik'o hanun shi, launin idanun ta ya kallah sun sauya kala sosai.

"Baby me same ka? Gaskia akwai abunda.... difff taji ta kasa fad'ar abunda take son fad'a.... kuka ta aza tana rik'e mishi hannu.... babyyy please...... waii!!! Shin mye ma zance??????? Dariya tayi tare da fad'ar bakomai.... tana hawaye😭tana dariaa😅...." wani abu take son fad'a Amma ji take kamar an aza mata wani dutse a zuciya ......Abun gwanin tausayi 😢
"Ke bana san shashanci"

Besan lokacin da bakin shi ya kufce yace haka ba.
Ya na son ya rarrshe ta but abunda ya ke ji yafi k'arfin zuciyan shi... haka ya dinga binta da ido kamar zautacce.

Keee!! Shine abunda Afra ta fad'a a tsawace.

"Mye kike wani tatta6a shi? Jarababba! Jarabar taki har takai ki dinga kai kan ki da kanki? Anyi asarar haihuwa anan.

"Keeeeeee...!!!!! Dan ubanki wa kike cewa jarababbe? Wallahi kishiga hankalinki dani, uban wa yace miki kowa irinki ne har kike wani ik'irari akan jaraba? Ko kin d'auka ban san abunda kike ba? Ki kama kanki saboda baki sanni ba tukunnah...." Meenah ce take wannan maganar gabaki d'aya se tsuma jikinta yake, gumi se tsatsafo mata yake, inda idanun ta har wani yalalo sukayi saboda masifa... da ganin kalar idanun nata kasan da kamar akwai wa'enda ke taimaka mata gurin masifa wato mutanen ta.
Duk iya kalar iskancin Afrah har ga Allah tana tsoron Meenah matuk'a domin kuwa hadda ita taso ta had'a duka har Ammien ta magan ce su, amma bokan nata ya shaida mata da cewa koshi karan kanshi tsoron Meenah da Ammien yakai kawai abar maganar su, yace mata kuma ko Shi Captain in ba wani mugun kamu irin yadda takeso maganin ze mishi ba, kawai dai tayi a sannu.

Wani kumfar baki kawai take tana masifa tana kallan idon Captain domin taga reaction inshi.
Zumud Captain ya tashi yana bata hak'uri akan ta daina baya san masifa,

Meenah kuwa kasakee tayi tana kallan su, dogon tsaki tajaa tare da hayewa upstairs because she's lost.

Captain kuwa har yayi yunk'urin bin Meenahr amma se yaji kamar dutse ya danne mishi zuciya, sosai yake jin wani abu can k'asan ranshi amma ya kasa tab'uka komai akai.
Duk wannan drama da ake Fahad ya dad'e da fita daga falon.

********************
Dai Dai wani d'an k'aramin restaurant ta Parker motar ta.
Zeenatu tayi mata misali har ta k'araso gun.
Shiga tayi daga can baya inda tayi mata kwatan ce gurin wasu y'an kujeri.
Hango ta tayi a take ta isa gurin duk da ba tada tabbaci ko itace.
"Zeenatu" shine abunda Abrar ta fad'a tare da cire glases inta.

"Abrar right? Please have a seat"

Gaisawa sukayi, shiru ne ya ratsa gurin kamun Abrar tace;

"Like kamar na sanki somewhere around gidan su Haidar koh?

"Yeah, nima na sanki somewhere around gidan su Meemee?

"Ehh hakane"

"Ni y'ar yayar baban su Meenah ce nazo daga Kaduna.

"Ni y'ar yayan Maman su Haidar ce, na kasance 'ya d'aya tal agurin iyaye na, tin ina y'ar shekara takwas iyaye na wata k'addara ta nutsa dasu, a yanda aka bani labari sun je garin Borno gurin y'an uwan mahaifiya ta anan ne k'addara ta afka dasu sanadiyar yan tagwayen boko haram, shine MAFARIN HARGITSI (by Ummuazamm ) tartsawa rayuwar iyaye na da duka dangin mahaifiya ta. Shine dalilin da yasa na cigaba da zama anan gun k'anuwar mahaifina wannan shine tak'aitaccen tarihina" shine abunda Zeenatu ta fad'a tare da d'orawa da "tun tasowa ta, tun da na fara wayo, tin bansan menene soyayya ba na fara son Haidar, tin ina 6oyewa har nakai bana iya 6oyewa, da na d'auka shima ze so ni daga baya amma se naga kwata kwata hankalin shi baya kaina, nayi k'ok'ari gurin ganin na yakiche shi daga raina amma abun yaci tura, bazan iya ba, soyayyar shi ta zame min gishirin rayuwa, bana tinanin zan iya rayuwa da wani d'a namiji in ba shi ba, soyayyar shi ta d'akusa dik wata k'ofa ta zuciya ta wanda bana ganin sha'awar kowane d'a namiji face shi.
Rashin so, da d'aukar matsayin y'ar uwa kawai da yayi mun yasa na k'udurci duk wacce ze aura se na zamu mata masifa a rayuwa, na buga na duba acikin zuciyar shi inda na gano cewa soyayyar k'anuwa kawai yake mun,, Na shiga mawuyacin hali a lokacin da na gane cewa baya ganin kowa a rayuwar shi face wannan tsinanniyar yarinya Maryam," anan taja fasali tare da kallan Abrar.

Tun da ta fara zancen Abrar ke kallan ta, domin kuwa batai tunanin alak'ar da ke tsakanin su da Haidar ba. Sosai zufa ta shiga tsiyayo mata a lokacin da taji ta ambaci kalmar so ga wanda take ganin tafi so fiye da kowa.

Wauta da rashin hankalin kanta ta gani k'arara ... tambaya ta shiga jerowa kan ta kamar haka;

— Mye sa tun farko banyi tinanin ita sonshi take ba?

— Mye sa tun farko banyi dogon tunani da nazari ba a lokacin da nake ganin messages inta a wayar Meemee?

— Mye yasa na kasa gano cewa tana son na taimaka mata ne gurin samun abu mafi soyuwa agareni?

— Anya kuwa tafiyar mu zata yi kuwa?
— Anya kuwa ban tafka kuskure ba?
— Taya zan taimaka mata gurin samun abunda nake so?

— lallai muna da k'aramar kwakwalwa dani har ita na saurin aminta da juna ba tare da sanin k'udurin ko wanne daga cikin mu ba.

— Ya zama dole na sauya tako nayi wasa da kwakwalwar ta.

Tafawa Zeenatu tayi gurin fuskar Abrar ganin tana dogon tunani.

Firgigit Abrar ta zabura tayi tana wata dariyar yak'e.

"Mye kike tunani haka?
Ta fad'a tana tsare ta da ido.

In inaa ta fara yi kamun ta fauze tace:
"Kawai ina tunanin labarin ki ne, kin bani tausayi ainun, Allah ya gafarta wa iyayen ki, kuma kisa a ranki Haidar naki ne ke kad'ai" ta fad'a tare da murmushi.

Murmushi Zeenatu tayi taji sanyi cikin ranta na wannan kalamai na Abrar.

Murmushin nata naga ya gushe lokaci d'aya, ta shiga yin magana cikin ran ta kamar haka:

— Kaii!!! Anya kuwa ina da hankali?
— Taya zanyi saurin gayama ta nawa k'uduri ba tare da nasan nata ba??
— Anya kuwa ban tafka kuskure ba??

Saurin katse zancen zucin da take tayi tare da fad'ar "tau ke fa? Gayamin naki k'uduri da kikeso a cutar da 'yar uwarki.

"Lol... ai kamar yadda kika fad'a inaso na cutar da 'yar uwata haka kema kikeso ki cutar da d'an uwan ki" shine abunda Abrar ta fad'a.

"Ai ba cutar da shi zanyi ba, kawai inaso na cika k'udurin auren shi ne,"

"A'a fah! Cutar dashi zakiyi tinda zaki raba shi da abunda yake so"
"Anyway... mubar wannan zance gayamin naki, kinga time is going shine abunda Zeenatu ta fad'a tana binta da wani k'ayataccen murmushi irin na shu'uman ci.

Abrar ma mayar mata da martanin murmushin tayi tare da fara fad'ar..........






(Nace hmmmmmm lallai akwai badak'ala ana.... koya zata kayawa wa'ennan 'yan duniyar ? Ohow)



Typing..............

Continue Reading

You'll Also Like

55.1K 2.6K 58
[ various! tower of god × reader ] Under the moon's omniscient watch, she dipped her hand into the waters where fishes swam around, across a thousand...
519K 33.1K 41
Let's see how different personalities mends with each other to form a beautifull bond together. Where the Eldest is calm and cold, Second is aggress...
19.7K 274 5
Gibbs adopted a troubled girl 8 years ago. He didn't tell anyone since she never did really good with a lot of people around. She was a foster kid si...
494K 17.3K 195
(Fan TL) Won Yoo-ha, a trainee unfairly deprived of the opportunity to appear on a survival program scheduled to hit the jackpot, became a failure of...