Abun Alfahari Na✅

By teemahcutey72

19.4K 1.5K 537

🌹Abun Alfahari na labari ne wanda ya k'unshi abubuwa daban daban na rayuwa...... labarin wata yarinya mai su... More

Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
END✅
Fashin Bak'i
Life Goes On
Words of Comfort
Advertisement

Chapter 8

316 25 0
By teemahcutey72

Page 8

🧚🏻‍♀️Abun Alfahari na🧚🏻‍♀️
Na
💕Teemahcutey💕

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

Bayan ya gama binciken shi akan wannan d'akin ya dauki abunda yakeson dauka pics kawai ya rufe qofar ya nifi dayar wacce Meenah ke ciki.

Bayan ya gama 6alle qofar yasa kan shi a cikin d'akin bakomai ciki face katifar da yaga macce kwance a kai, ya tsaya ne yana nazari kamin  ya qarasa gurin ta, duk gashin ta a barbaje yake, wani ya rufe fuskar ta saboda l gurin kiciniyar kwatar kanta har hijab inta ya cire da hula.
Wayan shi ya dakko ya dauke ta pics a yadda  ya ganta kamin daga bisani ya sunkuce ta batare da duban fuskar taba ya sanya ta bayan motorn shi.

Dawowa yayi cikin gidan,  acan sama gurin wani qarfen cotton ya saka wani dan qaramin spying cam. Bawanda yake gane akwai abu ah laqe cox is black in colour just like qarfen Nd it contains magnet Wanda ya maqaleshi ah jikin qarfen.

Motor ya tada tare da fara tafiya yana neman shago, bayan ya d'anyi nisa ne ya hango shi,  parking yayi tareda fita ya nifi shago. Padlocks ne ya siya irin wa'enda ya balle ah gidan guda ukku, bayan ya karba a hanzarce yakoma dajin yaje gidan yah rufe qofofin da ya b'alla, ya dawo a qofar shiga gidan ya qara saka padlock in kamar baa shiga gidan ba, motan shi yaja ya wuce.
***************

Qarfe 10:30pm daidai.... mommah kam yanzu  jikinta yay la'asar.
Gashi gabanta se faduwa yake domin poppahn su Meenah baya garii ya tafi abuja gurin wasu yan harkokin, so  she can't call him kada ta tayar mishi da hankali, to amma ya xatayi?
Dole ta saka hijab takira Miemie akan suje neman Meenah koh da Allah zaisa a dace.
Houses na neighbors insu suka fara zuwa dik Inda sukaje se ace musu Meenah bata zo ba, abu wasa wasa har suka kusa kawowa gidan matarda Mommah ta aiketa can.

Iskane yake tashi da qarfi alamun hadarii da qarfi iskan ya dakko Hijab in Meenah sai gaban su, zatr ido Mommah tayi tare da d'aukar hijab tana kallo, tabbas wannan na Meenah ne. To mye hakan yake nufi? Ina Meenah? Myesa ta yada hijab? Abubuwan da Mommah ke fadi kennan kamar wata zautatta, Miemie ce tace Mommah kwantar da hankalin ki za'a ganta, batayi  aune ba kawai se taga Mommah ta fad'i ah some, ihu ta saki tare da dafe kai, gani tayi bakowa balle ah kawo musu d'auki, duqawa tayi tare da aza kan Mommah a cinyarta tana gunjin kuka, wayar Mommah ta hango gefe kadan hannu tasa ta dakko tare da latsa kiran Mmnsu Haidar.
.Batare da bata lokaci bah hajia ramatu tayi picking kukan da taji ana yi ne ah dayan bangaren ya saka ta miqewa.

"Miemie lpianki kuwa ? Mye faru kike kuka? Ina mamanki? Ajere tayi waennan tambayoyi ..,

Miemie koh daya bata amsabah....
daga bisani tace dan Allah mama ki taimakamin bayan tayi mata taqaitaccen bayani akan inda suke.. atake ta kira haidar akan ya fidda motanshi cikin gaggawa zasu fita kasancewar tata motar ta lalace..
Batare da bata lokaci bah tayiwa haidar taqaitaccen bayani akan inda xasu tafi...

Koh da suka isa gurin su Miemie har an fara yayyafi, kasan cewar dare yayi sossai shiasa daidai kun mutane ne kawai ke bi a hanyar saboda lalacewar zamani ba wanda ya kalle su bale ayi maganar wani abu wai shi TAIMAKO!!

Dagudu hajia ramatu tafito a motor tare da taimakon ya haidar aka saka Mommah a motor se hospital..

Bayan y'an gwaje gwaje da aka yimata aka tabbatar da ba wani problem kawai faduwar gabane yasameta har ta suma, sukace zasu mata allurar bacci sbd tasamu relief....
Bayan anyi administering inta se akayi transferring nasu to Aminity.

Baccine takeyi hankali kwance dagannan haj. Ramatu ta tambayi Miemie asalin abunda yafaru, ta kwashe komai ta gayamata, salati mama ta buga ita da ya haidar....

Mama tace kenan kina nufin ba'aga Meenah bah? This is serious ya haidar yace, Miemie bata qara cewa komai bah kuka take kawai,...

Ajiar xucia mama ta sauke tace to Allah ya bayyana ta.

Umarni tabawa haidar akan ya dauki Miemie yakaita gdansu ta tada maneer dayake yayi bacci shiasa suka rufeshi... ta tadashi ta rufe gida se yawuce dasu gidan su.. acewarta ita xata kwana da Mommah dan haka Miemie da maneer ah gidansu xasu kwana coz is not safe su kwana su kadai batare da wani babba bah... haka su ka tafi jugumm ba walwala...

***************

Gudu yake tsalawa kasantuwar baya son driving in dare, in horn, yay aka bud'e mishi gate, shigewa yay, horn yaqarayi ah d'ayan gate na b'angaren shi aka bude ya danna hancin motanshi ciki, faka motar yay tare da za gayawa gidan baya ya d'auki Meenah kamar yar teddy bear.
Sanadiyar daren da ya tsala gashi kuma ana yayyafi shiyasa bai qarasa b'angaren Ammie ya kai yarinyar ba. Ya wuce nashi direct.

Wani abu ya latsa qofar ta wangale  ya shige, wani dan siririn corridor ne mai d'auke da tangamemen pic inshi da Ammie wanda suka d'auka saudiya, idan baka san su ba tabbas zaka iya cewa larabawn usul ne.

Wasu 4steps ya haura se gashi a wani haddaden qayataccen parlour, qamshi ne ne tare da sanyi AC ya bugi hanci na take na lumshe ido, a sannu nake bin bayan su, koh da ya iso tsakar d'akin wani Hadden pool ne Ah ciki da wasu kifaye sunata yawo multicolours abun ya matuqar bani mamaki, gabaki daya parloun farine qalll, kumai rashin imaninka da rashin adalci ka shiga wannan parloun seka yaba.

Abunda ya qara firgitani shine ganin ya taka wannan pool in batare da yafada cikin ruwanbah.... mamakine sosai nake, kawai se nayanke hukuncin qarasawa naga menene,?

Qarasowa nai naduba da kyau lallai tabbas wannan dan qaramin pool ne daidai inda ake aza centre carpet ...... gashi qananan kifayen se yawo suke ga ruwan blue colour mai haske se daukar ido suke....

Nayi tunanin May be Mahmoud tsafi yake shiasa bai tsumbula ciki bah.

Shahada nayi tare da runtse ido na aza qafana... nayi tunanin najini tsumbul cikin ruwa amma senaji akasin haka...
Wani irin smooth abu naji nataka mai matuqar sanyi gashi dai na taka shi glass,
haka naci gaba da tafiya akanshi har nakai qarshe, aikuwa nadawo na qara komawa, qauyancin dai qarara 🤣🤣🤣🤣..
Ananne na tabbatar da cewa wannan labarin da najia akan anyi wani abu kamar swimming pool da fishes ahciki kamar tiles kuma ah cikin gida ake sakashi na tabbatar....
komai wayewarka ka shigo bangaren capt. Mahmoud sekayi qauyanci koda na second d'ayane.

Qofofi ne guda ukku reras a cikin parlour, d'ayan na fara nufah domin nagane wa idona kuma na baku labari, wani had'adden small room ne mai qunshe da smalls round chairs kamar qwarya... se computers, da tapses da laptops ne jere aqalla zasu kai 4 aciki, da CCTV camera, waccee yake storing duk abunda ke faru a gidan ga baki d'aya for security purposes.
Acan b'angare d'aya wasu yan drawers ne masu qunshe da tangama tangaman littafai masu girma.....
Ah gefen laps inkuwa wani green coffee dispenser ne dakin gabaki daya komai green ne gwanin shaawa.. ko anan aka ajiye mutum ze iya qarasa rayuwarshi, ga standard AC kai gskia duk yanda nai muku bayani had'uwan ya wuce hakan.

D'ayan d'akin kuwa simple ne domin suma complete set ne between chairs wardrobe and Murphy bed dika iri dayane ga tV ah ciki da split AC. Sai yar qaramar glass door da alamar toilet ne.

Babban d'akin shi ya nufa da Meenah tare da ajiye ta akan panel bed inshi, har yanzu dai bai duba fuskar ta ba, kawai ya fad'a band'aki yay wanka tare da Alwala,
Fitowa yayi ya shirya cikin jammies,
yau ko shafe shafen da ya saba beyi ba, kachokam hankalinshi ya koma kan yarinyar, a hankali yaxo gaban ta yana kallon ta, qureta da ido yayi dan kamar yaga fuskar saniz

Se daga bisani ya gane itace yarinyar da ya gani akan Babur dsame wacce tace mishi mai motar aro daya watsamata chabi... daria yay da ya tuno da rshin kunyar yrinyar...
ahankali yake bin gashinta da kallo ya gangaro kan lulu eyes inta zuwa zara zaran eyelash's inta kamar tayi fixing tabe baki yayi yace wannan yar yarinyar hadda fixing lashes? Ai kuwa se na ciresu...

Hannunsa yakai kan lashes inta yajaa kawai seyaga har naman idonta yaja... xare ido yay yace ahh wato wnn natane kenan.... tabe baki yay yace koda yake idan kayi la'akari da gashin kan ta, gefe yaja yana kallon ta, yace da ganin wannan qaramace amma se girman jiki.... da ka kalli fuskar ta xakaga yarinta da masifah da wauta qarara .

Bacci yakeji hakan yasa ya ragemata qarfin AC yay mata rufah tare da tofeta da addua dan shi gani yake inda yayi saurin aure da ya haifeta.
D'ayan dakin ya nufah domin bacci.....

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
Mahmood ya kasance mara girman kai, kuma ba ruwan shi da rawar kai irin na masu kud'i ko wanda y'ay'an masu kud'i keyi.

Duk da ya kasance mai farinjini ga mata amma wannan bai zama sanadin lalace rayuwar shi bah, bai tab'a soyayya bah, amma ba zaice baya mu'amala da mata ba, kuma kosu sun san limit inshi akan mace, baya wuce hello Hii,baya d'aukar raini, baya wasa da Mace, abunda ya had'asu da sungama shikenann and nothing else....

Ya tsani namiji womanizer shiasa ba wasu frnds bane dashi, mafi akasarin abokanan shi basa nan, babban abokin shi dan Ambassadorn Ne amma yana Kuwait gurin qaro karatu.
Tare sukayi a Sri Lanka amma ba course daya suka karanta bah....
Wannan ne yasa wasu mazan suke mishi kallon mai girman kai sbd ba ya shiga harkan kowa..

Ba girma kai bane sbda aikinda yake anriga anyi musu training not to mingle with people because suna buqatar privacy sossai akan aikin su.....
So shiyasa yana gaisawa da mutane amma ba ruwanshi da personal life inmutum coz shima baya son ayi interrupting cikin nashi p.life...

Yana living life inshi with full of happiness and cheerful, abunda yake d'auke mishi hankali da yasa ba yada lokacin soyya shine aikin shi da yake tsawaita yawan bincike, amma har ga Allah yana son ya samu mata yay aure kawai ya huta da mgnr Ammie shii da kuma dadynshi, shiyasa kullum adduar shi Allah ya bashi mata ta gari wacce ke sonshi tsakani da Allah badan komai nashi ba. Wannan kenan
************

Misalin qarfe ukkun dare mommah ta farka, kan tane taji yayi nauyi matuqa..
Da kyar ta tashi zaune tana dafe kanta...
zumut ta miqe saboda tunowa da tayi yar su ta bace, sosai hankalinta ke qara tashi... ahankali ta shiga duban inda take, a nan tagano cewa ah hospital take.
Wayarta ta jawo tare da turawa poppahn su SMS akan yadawo gida da yar matsala, tayi mishi hakane Domin kada ya wani tada hankalin shi though tasan hankalinshi ze tashi,
Sheshshekar kukanta ne ya tada hajia ramatu... qarasowa gurinta tayi tana mai bata baki.
Da qyar da sudin goshi tasamu ta komah bacci koh shi ma saboda allurar da akay matane.

Misalin qarfe 8:00am ne poppah yakira qanin shi Omar akan yay sauri yaje gidanshi kamar da akwai matsala, dayake yana gidan gwamma jin hakane yasa tasaka hijab inta suka fito tare.
Koda suka isa se sukaga gate in gdan ah qargame. Uncle Omar wayarshi ya fidda yashiga neman layin Mommah a can cikin barci ta dakko wayan ta daga
Bayan ya gaidata ya tambayeta Ina suka tafi da safiya nan haka yaxo shida gwamma amma ba sannan?
Gayamishi tayi suna privet hospital Ta Namadina dake mabera.
Ahanzarce kuwa ya'isah ahcan din.

Shiga sukayi aka kaisu dakinda take.
Tambayanta yay myeke faruwane?
Anan ne ta kwashe komai ta gayamai salati gwamma ta dauka tana taba hannu...
Karkace baki tayi tace; "kee hwarida (fareedah) yanzu kina nufin Aminatou ta bace kenan?
Nashiga ukku ohni 'yasu.. aiko yau bamuga ta zama bah.
Tunda dai kinji sauqi ai se ah sallameki mutashi xuwa neman yarinya... habaaa ace yarinya budurwa ta bace kacokam..?
Kaii Ni wannan duniya ina xaki damu? Duka gwamma ce ke wannan salallamin.

Booking flight poppah yayi na 12:30 from Abuja to sokoto.

Flight insu poppah yayi landing kasan tuwar Abj to Skt is just 40-50mints.
A hanzarce ya wuce gidansu gwamma sbda Omar yayi mishi bayani da aka sallame fareedah chan suka wuce kawai.

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
Manage this please......

I really appreciate your love and prayers thank you so much
Allah ya barqauna

🧚🏻‍♀️Abun Alfahari na🧚🏻‍♀️
         Na
💕Teemahcutey💕

Ina miqa miqa tarin dubun gaisuwana gareku
@shamsiya Muhammad (ammyn khairat)
Saliha (smarty)
Lipton gal
Aisha humaira (yar guzuma)🤣😜
Teemah Yola ( uwar rigima🤣👊🏿)
And others I love you alll😍😍❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
😍😍😍😍😍😍😍😍
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
😍😍😍😍😍😍
❤️❤️❤️❤️❤️
😍😍😍😍
❤️❤️❤️
😍😍
❤️

Continue Reading

You'll Also Like

12K 564 20
Labari ne dake dauke da darussa kala kala na rayuwa, Mai dauke da tausayi, Al'ajabi ga kuma kauna agefe d'aya.. shin wacece UMMI_A'ISHA?
141K 8.9K 55
Kallon kitse ba litaffina bane na marubuciyar nan ne Halima Abdullahi k/mashi
1.9M 60.2K 76
Alexander, James and Skye were triplets. They were stolen from their family at the age of 4. The family searched for them day and night never giving...
143K 7K 124
#FOR OFFLINE READING PURPOSE ONLY *I'm not that good at translating and most chapters are Google translated. In the Future, My Whole Body is a Treasu...