Bai tsaya sauraran sauran bayanin ba ya fita da sauri har Yana hadawa da 'dan gudu ya nufi part din Sa'eed, Haleesa ma da taji abida Ummi ta fada ko dankwalin ta Bata tsaya daurawa ba ta zurma hijab ta fita itama da gudu,

Shigar Sa'ood yayi dai_dai da fitowar Sa'eed gaba daya jikin shi a mace ya nemi wuri a qasa ya zauna hade da dafe kanshi, yuuu mutane suka haura wurin shi suna tambayar halinda Saleeha take ciki Amman abin mamaki a maimakon ya Basu amsa saiga hawaye sharr a idon Sa'eed kowa Saida gaban shi ya fadi dan tunda sukaga Yana kuka sun riga sun saka ma ransu kawai Salee ta mutu,

Tsunguna a gaban shi Zara tayi tana Dan jijjiga hannun shi itama taci kuka har ta gaji murya ciki_ciki tace
"Miel Yaya Salee da babyn ta?"

Fashewa da kuka yayi Bai damu da yawa da Kuma yanayin mutanen dake wurin ba yace
"Na kasa yin komai a Kai har yanzu zubar da jini takeyi, bansan ko zata iya tashi ba na kasa ceton Saleeha she is paying for my crimes after all, na cutar da rayuwar ta ki taimaka Mata Dan Allah"

Su Nabeela suna Jin Haka suka duru cikin dakin ita da Shugaba da momy, Saida suka saka Mata sutura sannan suka ciccibo ta ruwa_ruwa suka nufi waje da ita already Idris ya fito da mota shi da Sa'ood suna ciki aka saka ta a baya, shugaba da Nabeela suka Shiga aka jaa mota sai Mailafiya hospital,

Suna tafiya driver yazo da mota ya tattari su Haleesa da mamanmu da Zarah, har zasu tafi Sa'eed yayi qarfin halin tashi ya Shiga gaban mitan suke tafi tare,

Shugaba ita kadai ta ciccibi Salee ta daura ta a kan gado aka tura ta cikin ICU,

2 hours later

Kallon wall clock Haleesa tayi ta sake fashewa da kuka Sa'ood sai aikin lallashi take dukda shima zuciyar shi ta karye Yana ji kaman ya Taya mamanmu da Haleesa harma da 'dan uwan shi kuka,

Sa'eed kanma zaman kujera ya gagare shi, neman wuri yayi a qasa ya zauna dabas ya zabga uban tagumi hawaye na sintiri a kan fuskar shi lokaci daya ya canza kaman ba Dr Sa'eed ba duk ma'aikatan asibitin Saida hankalin su ya tashi ganin shi cikin wannan yanayin, shiyasa suka rufu a Kan Salee suna fafutukar ceto rayuwar ta da na abin cikin ta,

Bayan dogon jira doctors din suka fito daga dakin fuskar su Babu yabo ba fallasa, Sa'eed har Yana neman zamewa ya qarasa wurin su yaji sakamako Mai kyau ko akasin haka,

"Alhamdulillah Dr Sa'eed matar ka tana lafiya Kuma munyi nasara wurin ceto abin cikin ta da yardan ubangiji, yanzu Mun tura ta dakin hutu saidai a qara kula dan Allah nasan ka Riga kasan komai ba sai nayi maka dogon bayani ba, Allah ya sawwaqe ya qara lafiya"

Zubewa yayi yayi sujjada sannan ya dago Yana godewa Allah, Bai tsaya wani Abu ba ya shige cikin dakin da aka kwantar da ita,

Kwance ya hangota sun daura Mata drip tana shaqar baccin wahala qarasawa yayi ya Mata peck a goshi baice komai ba ya tsaya Yana qare Mata kallo, kaman lokacin farko wannan karon ma ta lalace ta jeme tayi baqi,

Ya zauna na kusan 20 minutes kafin yayi addu'a ya today Mata ya fita daga dakin, mutane daddaya suka dinga shigowa suna duba ta har suka bar asibitin Bata farka ba sai Bayan sallan la'asar,

Mahaifiyarta ta fara gani Bayan ta bude idonta tana tsaye a Kan qafafunta Amman da sanda a hannun ta tana dogarawa, kaman a mafarki take ganin abun koma a mafarkin ne ta gode ma Allah da ya nuna Mata mamanmu ta warke,

Qoqarin tashi tayi tana dariya da sauri Haleesa da Sa'eed suka tare ta suka maida ita suka kwantar
"Kiyi a hankali sister Baki da lafiya fah"

Riqe hannun Haleesa tayi tana dariya tace "Leesa mama ne na gani a tsaye? Tana tafiya kuwa?"

Itama murmushi Mai qayatarwa Haleesa tayi tace " itace Salee mama ta warke Kuma kema kin warke babyn ki na lafiya Babu abinda ya same shi"

Kwanciya Salee tayi ta daura hannuwan ta a Kan fiskarta tana "alhamdulillah, alhamdulillah, Allah na gode maka, ka min ni'imomi da yawa Allah ka qara jaddada rahamar ka a bisa Annabi Muhammad" duka dakin suka amsa da "s.a.w"

Sai Kuma ta dawo tace ma leesa "yanzu ke ya batun liyafan Kun? Ba Zaku je ku shirya bane sai lokaci ya qure Muku?"

" Haba Salee kina cikin wannan yanayin was yake maganar liyafa Kuma? Mu da muke nemar yardan Allah muke gode Masa ya Raya Mana ke da abin cikin ki Kuma muzo mu Saba mishi ta wani liyafa?"

Sa'ood ne ya amshe da haka ne Kam, Nima na fasa Kuma ko munce zamuyi ma lokaci ya riga da ya qure Mana flight dinmu 8 zai tashi so Banga amfanin yi yanzu ba,

Da haka Salee ta tursasa Leesa da sauran mutane suka koma gida aka fara Shirin Kai amarya airport, oga Sa'ood kuwa shegen zumudi tun magriba ya Gama shirya komai na tafiya, Sa'eed na asibiti maqale da Salee, barrister Adam kuwa Banda zuban zance da neman magana Babu abinda yake you haka ya tunzura Ameer ya koma KD Babu shiri saboda tsantsan habaici,

Bangaren amarya kuwa Bayan mamanmu da sauran iyaye sun Gama Mata nasiha shugaba ta nitsar da ita ta fara Bata lectures irin tasu na bariki, Saida ta tabbatar Haleesa ta kwashi darasi kafin suka rufa ta aka dauke ta sai airport tana kuka kaman ranta zai fita har suka Shiga cikin jirgi,

Lallashin ta Sa'ood ya dinga yi yana jaddada Mata zata dawo wurin maman ta tunda gida daya suke da haka tayi barci,

11:37pm

Bayan sun idar da sallah Sa'ood yayi Mata addu'an da manzon Allah ya koyar, sunci sun Sha anyi Shirin barci, Haleesa tace

"Ya Sa'ood nikam ko zamu koma gida ne? Inason ganin halinda 'yar uwata take ciki"

Zaro Ido yayi tare da rage hasken dakin ya qarasa wurin ta Yana fadin "mu koma gida nayi asaran kudin da nayi booking hotel da sauran abubuwa Bayan Wanda nayi na liyafa, hhh impossible yarinya"

Wannan karon fa ummu Najma ta zage tana so ta kawo Muku komai kaman Yanda kuka buqata harda neman wurin zama saboda kada su maman sadeeq suce tayi cogel Amman zaman da zanyi yayi daidai da daukewar witar nepa🤦🏻‍♀️

Kuma wallahi naji wata ta zagi nepa ta gani sai Bayan shekara 5 zamu koma gidan😤

*Ummu Najma ce 😘*

KAMA DA WANE....(Completed)Où les histoires vivent. Découvrez maintenant