chapter 2

387 47 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
  🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
                          BATA WANE👩🏻‍🦱
   💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *Na*
        *UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
       *And Fenarh matar Soja*

02👯

"Haba Dan Allah! Wannan wani irin rayuwa ce talauci yaqi ci yaqi cinyewa kullum Abu gaba gaba yake yi Allah ya tsine tsiya inji arziqi, wallahi ba don qaddara ba babu abinda zai kawo ni gidan ka Sa'eed"

Murmushin yayi Jin maganar ta na qarshe ya daga al'amin ya karkade mishi jikinshi ya maida mishi glasses dinshi sannan ya wuce dashi dakin sa,

Yana tuna lokacin da yake a matsayin DOCTOR SA'EED KHALIFA MAILAFIYA a wannan lokacin Zarah har gida take binshi ba tare da taji nauyin iyayenshi ko kunyar su ba zata shige har cikin bedroom dinshi tayi abinda ya kawo ta tafice wani lokacin wuni takeyi ta kwana a MAILAFIYA mansion babu Wanda zai nemi sanin inda take a lokacin ko Kara yace kada ta tsallake ba zata tsallake ba Amman halin rayuwa yasa yau Zara tana bude bakin ta tana Kiran shi da matsiyaci, da yasani da yaji maganar SA'OOD lokacin da yake fada mishi Zarah ba matar aure bace.

Kwantar da al'amin yayi don kukan da yayi ya saka shi barci ya bude wata Yar qaramar drawer ya dauko wani enlargement Yana kallon su Daya Bayan Daya.

Kusan mutane 20 ne a jikin picturen daga kan tsofaffi har zuwa qananun yara kowa cikin shiga ta alfarma sunci ado sunyi matuqar kyau fuskar su dauke da qayatatten Murmushi a qasan pic din an rubuta MAILAFIYA FAMILY in itallic saidai abun mamakin shine Sa'eed guda biyu ne a jikin pic din (wait! Guda biyu Kuma?) Ohh that's his Twin brother SA'OOD.

Shafa fuskokin su yake yi yana zubar qolla
"Why Sa'ood? Me nayi maka ka tsaneni da yawa da har ka manta cewa ni Dan uwan ka ne na jini kake cutar dani da hannun ka? What have I done wrong? Wani laifi mukayi ne har muka cancanci irin wannan jarrabawan qaddara yazo ya raba kawunan mu ya jefa mu cikin musiba ni menene laifi na Akan abin da ya faru?"

Saida ya gama qare musu kallo sannan ya miqe ya ciro yar baby nokia dinshi ya kira wani number ya fita daga gidan gaba daya don yasan idan sukaci gaba da zama zarah zata fito da wani rigiman da dole sai sunyi fada.

***********

3:40pm
Suka fito daga gidan sanye da uniform din islamiya light blue hijab dinsu har guiwa qafafuwqn su sanye da sandal da black socks Saida Salee tabi shago ta sayi big bom kafin suka fara takawa zuwa makaranta.

Suna shiga aji dalibai suka fara darewa suna Basu wuri saboda basusan zama tare da karuwai, abun ya riga yabi ma Salee jiki bata damu ba ta nemi seat din gaba ta zauna ta fara fiddo da qur'anin ta da sauran littatafan da ake musu,

Leesa kuwa tana tsaye tana kallon su yanda suke nuna ta da yatsa suna magana qasa qasa, Allah ya Isa ta qara ja was iyayen ta domin su suka jawo musu wannan wulaqancin duk inda suka shiga ana qyamatar su da laqana musu laifin da Basu aikata ba, badon Salee ba da ta dade da shiga duniya tasan ko aikatau ta samu zai ishata rayuwa Amman idan ta tuna futuren Salee sai ta fasa babu inda zasu je su sake kaman gidan Shugaba.

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now