chapter 38

216 39 7
                                    


(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
BATA WANE👩🏻‍🦱
💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*Na*
*UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
*And Fenarh matar Soja*

38👯
Da sallama Sa'eed ya Shiga parlorn har lokacin Leesa tana tsaye tana tsiyayar hawayen rashin gaskiya ita a Kan me Sa'ood zaiyi Mata fada? Bai bi ta kanta ba Dan baisan Mai ya same ta ba ya qarasa wurin mamanmu ya tsunguna Kan guiwowin shi sannan ya gaidata, fuskar ta a sake ta amsa tana shafa gashin kanshi hade da yi Masa addu'a sosai dan tun suna yara Haka take musu musamman ma idan tasan zasu fita,

Tsaki Leesa taja tana hararar su ta wuce bedroom dinta sukayi Mata rakiyan idanu, girgiza Kai kawai Sa'eed yayi ya dawo da hankalin sa Kan mamanmu tare da sunkuyar da kanshi qasa ya fara neman afuwan ta Akan abinda yayi ma Idris jiya da dare,

Bai qarasa magana ba tayi saurin dakatar dashi, "look up son"

Ta fada tana dago kanshi don ta bashi Daman kallon cikin idon ta tace "abinda kayi dai_dai ne Sa'eed duk wani me laifi ya cancanci hukunci, da ace ka boye fushin ka a zuciya da shine Raina zai baci matuqa Kai da Idris da Sa'ood duk daya kuke a wurina so iri daya nake Muku kuma har abada matsayin ku cikin zuciyata ba zai ban_banta ba, Kuma insha Allah ni da kaina zansa ya miqa kanshi wa hukuma dan ya dawo Mana da abinda muka rasa ya wanke baqin fentin da yayi maka no te molestes (kada ka damu kanka) okay?"

Murmushi yayi Yana Jin sanyi a zuciyar shi daman yasan wurin mama da Salee ba zai samu matsala ba, itama tun da safe da ta tashi ta koma kamar ba'ayi komai ba tana abubuwa normal shidai fa alhamdulillah Dan sa'a a ma har Yana neman yi mishi yawa,

Miqewa tsaye yayi yadan rage tsayin sa sannan ya riqo hannunta na dama yayi Mata peck a jiki Yana fitar da qayatatten Murmushi irin Wanda Sa'ood sai yayi wata baiyi irinshi ba yace

"Thanks cariño you are the world best mother and mother in-law muna sonki sosai"

Dariya tayi cikin jin dadi ta yarfe hannu gefe tana fadin "don't mind Chéri, Ina yarana da jikoki na? Matan ka sunmin qaura tun shekaran jiya rabon su da su shigo part dinnan"

" Zasu shigo cariño, kinsan ba'a son sarwa tana zirga_zirga da yawa ne saboda ta dada samun qarfin jikinta shiyasa Kuma idan suka fito gaba Daya gidan Nan kaf sai sun karade shi, Amman insha Allah anjima zan turo su"

Riqe baki mamanmu tayi cike da mamaki "Allah ya hada ni da surakanan zamani yanzu yaran nawa ma idan inason gani sai na nemi Izininka ka turo min su? Kuma yarinyar nan ta samu lafiya Amman saboda Yanda kake sakalta ta sai wani lanjanewa takeyi"

Yana dariya yace " Aa cariño ba abinda nake nufi ba Kenan, idan kina so ma ai sai su dawo Nan part din gaba Daya da zama, brother ya sauqa ya basu dakunan sama"

"Yanda kaima zaka dawo Nan ka tare min Ina kallon rashin kunyar ku ciwon zuciya ya Kama ni ko? Rabani dan Allah, ku qarata can Nima ba son ganin su nake ba"

Suna cikin hira Nabila ta shigo da yaran ta da yaran Zarah da na Sumayya (tsohuwar budurwan Sa'ood) kowa da uniform din makaranta a jikin shi suka gaishe da mamanmu, sannan tayi musu rakiya suka Shiga motocin da ake kaisu makaranta suka tafi itama ta koma part dinta, Sa'eed na zaune Idris ya shigo ya qarasa wurin mahaifiyar shi cike da ladabi ya tsuguna har qasa ya gaidata,

Lokaci Daya annurin dake fuskar ta ya kau, bata amsa gaisuwar shi ba ta kawar da kanta gefe Dan har cikin zuciyar ta taji zafin abinda Idris yayi ma Sa'eed ya zamo tamkar wani cin fuska ne a gareta,

Daga sama ya jiyo muryar ta tana fadin " yaushe ka shirya girban abinda ka shuka?"

Dagowa yayi Yana kallon ta a darare yace "afuwan mama Amman ban fahimci abinda kike nufi ba"

" Ko kayi tunanin Mun manta ne ko bazamu dauki mataki a Kai ba? Ko ka shirya kaje police station and get yourself arrested ko Kuma har cikin gidan nan zamu Kira su suzo su dauke ka sai ka zabi Wanda yafi maka sauqi a ciki"

Hadiye wani abu Mai daci Idris yayi, he already see this day coming daman yasan da sannu idan sirrikan shi suka bayyana ko matar shi da mahaifiyar shi ba zasu goya mishi baya ba
"I will go straight from here, insha Allah yau dinnan Zan bayyana ma duniya duk wani aikin barnan da na aikata Amman Dan Allah kafin Nan ki yafe min ki daina fushi dani ko zan samu sauqi ta wani wurin"

"hakan zai faru ne kawai bayan an hukunta ka, sai shari'a ta wanke laifin ka Tass kafin ka samu fuska daga gareni, tashi ka bani wuri"

Roqonta yayi ya fara Mata maqiya Amman ta daga kanta kaman ba da ita yakeyi ba, da taga zai dameta ta juya da Kan keken ta tayi ciki har zata shige bedroom dinta Sa'eed yace
"Ba sai yayi surrender ba mama na yafe mishi kema kiyi haquri ki....."

" Kul da wasa idan Ina magana ba da Kai ba kada ka sake shiga ban nemi ra'ayin ka a Kai ba Kuma idan Kai ka yafe mishi ni ban yafe mishi ha'inta ta da yayi ba Kuma saboda shi ba zamuyi asaran hospital ba, Mailafiya orphanage is like my home 'yan uwana suna cikin wahala suna buqatar ceton mu Kuma hakan zai faru ne kawai idan ya miqa wuya"

Tana Gama fadan haka ta shige ciki hade da rufo qofa, juyawa Idris yayi wurin Sa'eed da nufin zaiyi Masa godiya da sauri ya tashi ya fita Dan bayi Jin zai iya sauraran wani kalma daga gareshi,

**********

Zaune yake Yana lilo a Kan kujera hannun shi riqe da pen drawing circles on a paper yayi nisa a cikin tunani tun da yazo ya kasa tabuka komai Bayan tunani ya saqa wannan ya warware wannan,

He is not even sure if he really loves Haleesa but he feels something deep inside for her, ko shine soyayyan? Amman fa bai taba samun kusanci da wata yarinya har yaji ya shirya ma auren ta lokaci daya ba Bayan Haleesa, saidai bayi da tabbacin zai iya zama da ita da wannan dabi'un nata ba zai jura ba,

Ringing din da wayar shi yakeyi ya dawo da hankalin shi Yana dubawa yaga unknown number Bai Bata lokaci ba ya dauka ya saka a kunnen shi hade da fadin "yess"

"Hi Mr Sa'ood I'm inspector Patrick calling from the police headquarter, we have arrested your brother Idris for the use of harmful and banned drugs that led to close down of Mailafiya hospital, and we will like to have you here as you are one of the witnesses we have"

Bai ce komai ba cikin tashin hankali ya katse Kiran ya fara neman numbern Adam, ganin zama ya gagare shi yasa ya miqe Yana rangada mishi Kira a Kai a Kai Saida yayi mishi 3 missed calls kafin a na hudun ya dauka"

" Hello SD Mai ya faru muna meeting ne nabar wayan a office "

Kaman zai zunduma ihu yace " Adam zasu haukata ni, Idris yayi surrender sun tsare shi yanzu Kam bansan ta Ina zan bullo was al'amarin nan ba, I told him Zan samo wani hanyar da zanyi gyara komai Amman yaje ya miqa kanshi ba tare da ya tuntube ni ba yanzu Yaya zanyi?"

" I know it, daman nasan kasan Wanda ya aikata abin Nan Amman kaqi fadamin you never told me it was Idris, yanzu Allah kadai yasan abun da zai faru takardan da nace zan tura ko fita daga office dina baiyi"

" Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, do something please Adam bani son ko kwana daya Idris yayi a wurin Nan idan asirin shi ya tonu kaman namu ya tonu ne me zamuyi Adam?"

"mu jarraba neman taimako wurin dadyn Ameer shine governor na KD nikuma partyn su daya da governorn garin Nan they are friends maybe zai iya taimakon mu mu jarraba mu gani"

"Kayi Mana booking flights yanzun Nan Dan Allah jirgin gaba da zai tashi zuwa KD zamu bi, I need to save my brother dan Allah kayi sauri dole muje government house yau dinnan"

Kashe wayan yayi ya tattari wayoyin shi da key dinshi ya fita daga office din, Bai qi yanzun Nan ya ganshi a kaduna ba,

_manage please🤒🤕😪_

*Ummu najma ce*😘

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now