chapter 48

238 36 5
                                    


(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
BATA WANE👩🏻‍🦱
💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*Na*
*UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
*And Fenarh matar Soja*

48👯
"In dai haka ne to fa saide kaje ka Sami iyayena su fasa auren da suke Shirin Mun, Amman muddin yarinya tayi min wani abun da bai gamshe ni sai ta karbi hukunci Mai tsanani inyaso daga lokacin itama ta tafi gidan su I don't care, daga baya zanyi karamcin binta da takardan saki"

Tagumi Adam yayi Yana kallon Ameer shifa har cikin zuciyar shi wannan Maganar yake fitowa,
"Ai hakan ba shi bane mafita kawai guduwa zakayi daga gida kaga de babu Yanda za'ayi auren dole babu ango 'dan rainin hankali kawai"

" Barshi barrister zuri'a ne bayi so, bayi buqatar Nan gaba ya samu magaji ya samu yaran da idan tsufa ta kama shi zasu tallafa mishi, ni koma lafiya ne baka dashi?" Sa'eed ya tambaya

Kafin yayi magana caraf Sa'ood ya karbe "wallahi lafiyan shi qalau garas yake harma ya fika lafiya, kana kallon shi ko wani lokaci ranshi a bace Yana zuru_zuru da Ido baqin jaraba ne take cin shi ba komai ba, nidai fata na daya kada Nan gaba idan ka kasa jurewa kana danne 'ya'yan jama'a don itama matar taka na farko Allah yayi Babu rabo a tsakanin ku ne amman kwana daya da tayi a gidan shi Saida ya moreta sosai kafin ya sake ta, Allah dai ya shiryeka kawai"

Miqewa Sa'eed yayi Yana zura takalmin shi yace " ameen fah, nikam kunga tafiya ta zanje na farantawa iyalina, har biyu nake dashi nayi ma gwabraye zarra sai na gayyace ku sunan 'yan uku_uku, future governor a daiyi zuciya ayi aure kada ayi abun kunya"

Sa'eed na fita Sa'ood yayi sauri ya canza kayan jikin shi zuwa irin na Sa'eed sak harda hulan da takalmi saboda tare sukayi dinkin yayi hanyar fita da sauri Adam ya dakatar dashi,
"Bawan Allah Ina zuwa? Ka zauna ka huta saboda ka samu qarfin girgijewa a wurin liyafa Amman ka shirya zaka fita kaje Ina?"

" Nima wurin amarya ta zani na faranta Mata wallahi bazan iya jira ba gaba daya na matsu na ganta"

" Eh to! Kuma kana da gaskiya ta wannan fannin, Nima kaga Bari na bika na samu ganin tawa matar Mubar gwabro da gadin daki" ya juya wurin Ameer yace " gwabro a rungumi pillow a hankali kada kaji ma kanka rauni" da fadan haka suka saka dariya suka fita,

**********
Qara riqo kafadan Zarah Salee tayi tana girgiza ta tace "momyn al'amin I'm over excited Naga suprise din da dadyn al'amin yace zai bamu Kuma gashi fa har yanzu Bai shigo ba"

Bata rufe bakin ta ba Sa'eed ya shigo dakin bayan shi samaruka ne dauke da manya manyan akwatuna, sake Baki sukayi suka bisu da Ido ya nemi wuri ya zauna sannan aka jere mishi akwatunan guda 36 a parlorn,

"Miel wannan Kuma na wane ne?"

"Akwatin auren Saleeha ne da Kuma kayan fadan kishiya Wanda kuke Bina bashi ban samu damar yi Muku ba tun lokacin baya"

Gyara zama Salee tayi tana qarewa akwatunan kallo sannan ta girgiza Kai tace "ni bani buqata inada kayan sawa nasu tarin yawa wasu kanma har nakan manta dasu a cikin closet"

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now