chapter 12

247 36 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
  🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
                          BATA WANE👩🏻‍🦱
   💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *Na*
        *UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
       *And Fenarh matar Soja*

12👯

Qofar dakin Zarah taje tayi sallama, tana fitowa ta miqa Mata laidan hannun ta tace
"Momyn al'amin ga cefanen rana Nan an kawo"

Har laidan hannun ta Saida Zarah ta harara sannan taja dogon tsaki ta koma ciki Bata ce Mata komai ba, tafi so sai Sa'eed bayi gida tana cin qaniyan ta a hankali Yanda cikin sauqi zata rabu da mijinta,

**********

Yau da shirye shiryen dawowar alhaji Wanda zai sauqa gobe su Leesa suka tashi tun safe suke faman aiki har 10 na dare kafin suka samu hutawa,

Gyara kwanciya bilkisu tayi tace "daga gobe gidan Nan zai cika ayyuka su qara Mana yawa babu kalan mutanen da ba Zamu ci Karo dasu ba, saidai Dadi na da alhaji akwai kyauta ma 'yammata, Leesa kema Zaki samu naki rabon gaki Allah yayi ki fara Allah idan kina da wayo Zaki kwashi maqudan kudade a aljihun alhaji "

Tabe Baki Leesa tayi
" Allah ya kiyaye ni babu abinda zanyi da kudin shi haka siddin na shiga uqubar wannan masifaffiyar matar tashi, ba dani ba gada a kotu"

" Ke da'alla madam wawiya ce wallahi Banda gwada izza babu abinda ta iya, Haka alhaji yake badaqalar shi cikin gidan Nan yaci ya cinye Bata iya cewa komai, kede ki zuba Ido daga gobe Zaki fara kallo"

Miqewa Leesa tayi ta nufi hanyar toilet tana fadin "Allah ya kaimu goben da Rai da Lafiya"

Washe gari tun asuba suka fara dafe_dafe da soye_soye zuwa 10 suka Jin jiniyan motoci, da sauri bilkisu taja Leesa suka hau sama suna leqa mutanen waje, cikin jerin motocin dake parke a haraban gidan aka bude mishi na tsakiya ya fito,

Cikin girmamawa mutane ke miqa mishi hannu suna gaisawa, dago Kai da zaiyi sai idon shi karaf ya sauqa a Kan Leesa, ya kashe Mata Ido daya Yana murmushi, da Sauri Leesa ta ja da baya ta dafe qirji,

"Na shiga magana bilki Ashe abun nashi babba ne ba sauqi, Kinga muyi sauri mu sauqa kafin ya gane mu"

" Daga baya Kuma Kenan wallahi yau dinnan Zaki ganshi yazo wurin ki kede kada kiyi wasa da damar ki Allah ne ya baki"

Bata kula bilkisu ba suka koma wurin aikin su, tana Allah wadai da halin irin na wannan mutumin,

1:34pm
Tana tsaye tana chopping albasa idanun ta na zubar da hawaye, qamshin turaren da taji ya cika Mata hanci ne ya sakata Juyowa tana kallon alhaji da ya jingina da garu hannun shi nade a qirjin shi ya zuba Mata na mujiya,

Dakewa tayi ta juya taci gaba da aikin ta, ta lura wannan alhajin babban 'dan iska ne aikuwa zatayi maganin shi, takowa yayi a hankali ya saka hannu ya cire 'yar qaramin hijab dinta, a rikice ta juyo tare da zaro idanun ta da hawaye ke kwance a ciki sai shining sukeyi,

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now