chapter 47

196 34 7
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
  🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
                          BATA WANE👩🏻‍🦱
   💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *Na*
        *UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
       *And Fenarh matar Soja*

47👯
Ko wani 'dan Adam da kike gani Cikin duniyar Nan da tashi kalan qaddarar, Kuma Bayan wuya sai Dadi tun lokacin da nasan labarin ku na gane akwai wata babbar qaddarar dake bibiyar rayuwar ku, Allah yasa ayi a sa'a ya Baku zaman lafiya na Taya ki murna sosai Haleesa Kuma insha Allah zamu zo gaba dayanmu har gida mu gaisa da iyayen ku"

"Na gode sosai mama Kuma Dan Allah kuyi haquri da matsalar da na saka ku ciki ban samu damar dawowa na cece ku ba saboda Nima Ina cikin tsaka Mai wuya a lokacin, alhaji Habib ba mutumin kirki bane kwata_kwata ya nemi keta min haddi shiyasa ni Kuma nayi amfani da dama ta na ceci kaina na tsere daga gidan, ban taba tunanin abin zai dawo kanku ba Amman ku yarda dani wallahi banzo gidan Nan da niyar cutar daku ba"

Gwada Mata hanyar daki maman Ameerah tayi da hannun ta tace " hirar namu a bakin qofa zamu qarashe ta ne ba Zaki Shiga ciki ba?"

Murmushi Wanda ya bayyana haqwaran ta Leesa tayi ta Gane Bata qullace ta da komai ba, taja hannun Ameerah suka Shiga ciki Amman Bata zauna ba ta ajiye handbag dinta ta fito tayi alwala tayi Sallah Saida suka zuba Mata tuwon masara da miyan kuka ta zauna taci Tama manta da zancen oga Sa'ood a waje,

Bangaren baba kuwa ya zage sai zuba ma Sa'ood fadanci yake yi saboda tsan_tsan ladabi ko hada Ido yaqi suyi, yasan tunda wannan alhajin yazo qofar gidan shi shida sana'ar tuqi sunyi hannun riga arziqi ne yayi mishi sallama dolen shi ya amsa,

Dan dolen shi a tare sukaje sukayi sallan la'asar suka dawo ya shimfida musu tabarma Yana Masa hiran duniya dukda Sa'ood ba wani saurara yakeyi ba ballantana ya amsa don har yanzu Bai manta irin Koran Karen da baban Ameeran yayi ma Haleesa ba ranar da Saleeha tayi 'bari,

Ganin ta dauki lokaci Bata fito ba yasa ya fara Kiran ta a waya Amman tana gani tayi biris abinta ta saka kwanon tuwo a gaba sai narka takeyi Tama manta da sunyi yarjejeniya ba zata ci abinci a waje ba,

Saida Haleesa tayi tamm sannan ta wanke hannunta ta Sabi jakar ta su maman Ameerah sukayi Mata rakiya har waje, da fitar su Sa'ood ya qaraso inda suke tsaye har qasa ya tsunguna ya gaida maman Ameerah cikin girmamawa irin tsungunon da baban Ameerah yayi mishi, sannan yayi musu kyauta ta ban mamaki kusan irin Wanda yayi ma shugaba ya dauki amaryar San suka Kama hanyar gidan Dan gaba daya ya gaji,

Rage speed din motar yayi Yana qare Mata kallo Yanda take ta faman murmushi ita daya, dukda ta wahala da tafiyar da sukayi a tsatsatsaye Amman yau tana cikin annashuwa sosai,

"Novio shi wannan farin cikin Kuma na menene?"

Dan Juyowa tayi ta kalle shi sannan ta juya tana qara fadada murumushin ta
"Ya Sa'ood yau ji nakeyi kaman an sauqe min wani nauyi dake Kan qirji na tunda na rabu da mutanen Nan, they owe me a lot dukkan su na Shiga cikin rayuwar su kuma na fita lokaci Daya ba tare da wata qwaqqwaran sallama ba sai yau Allah ya dawo Dani na gyara kura kuraina mukayi sallama suna murmushi, I feel relieved, and all the credits goes to you thank you so much ya Sa'ood"

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now