chapter 23

221 33 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
  🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
                          BATA WANE👩🏻‍🦱
   💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *Na*
        *UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
       *And Fenarh matar Soja*

23👯
Da sauri Sa'eed yayi ciki hankalin shi a tashe Zarah ma tabi Bayan shi suka Shiga dakin Salee, hango ta sukayi kwance a qasa shame_shame cikin amai a hakan ma sai qaqari takeyi Amman Bata iya fitar da komai sai ruwa,

Da azama Sa'eed yayi kanta Yana taba jikin ta yaji da zafi sosai ya dagata Zarah Kuma ta fita dauko abinda zata goge Aman dashi, juyawa yayi ya kalli al'amin dake tsaye a bakin qofa yace yaje ya kwanta, yana tafiya ya cire mata rigan jikinta ya dauko wata 'yar qaramar dogon riga,

Yana cikin saka Mata Zarah ta daga labule ta shigo,tayi sauri ta koma ganin abinda yake faruwa ta jingina da garu hade da dafe qirji tana Jin ranta na suya koma wani abun sukeyi da bazasu jira ta tafi ba,

Saida ta tabbatar ya gama kintsa ta sannan ta Shiga ta samu ya kwantar da ita Akan gado Yana goge Mata jikinta da ruwan sanyi dan ya samu zazzabin ya sauqa kafin yaje nimo Mata magani,

Zarah tana gamawa ta qaraso wurin shi ta karbi towel din yake danna mata jiki dashi
"Ka bari na qarasa miel sai kaje ka Nemo alluran da za'ayi Mata kaga dare Yana dada yi"

'dan murmushi yayi yace " thanks mi Alma dole ma sai na saka Mata ruwa so ki dan zauna tare da ita yanzu zanje na dawo"

Saida yaje pharmacy na asibiti kafin ya samo abin da take buqata dan yanzu dare ya raba 12 har da 'yan mintuna shiyasa yawancin shaguna sun rufe,

Zarah na zaune tana bin Salee da kallo gaba daya kamannin ta ya sauya, ta jeme tayi duhu, ba qaramin wahala cikin Nan yake Bata ba ko dan shekarun ta yayi kadan ne oho dan itama batayi irin wahalan ta a cikin fari ba,

Sa'eed na dawowa Zarah tayi musu sallama ta tafi dakin ta, tana kwance sai juyi takeyi tana kallon haske ta windown dakin su har wurin 1:30am, haka kawai taji zuciyar ta Yana raya Mata fakewa da ciwo Salee tayi dan kawai ta karbi kwanan ta shiyasa har yanzu basuyi barci ba,

Runtse idanuwan ta tayi ta juya ta Yanda ba zata dinga hango dakin ba tana mainata a'uzu billahi minal shaidanir rajim, dan tasan tabbas shaidan ne yake son janye hankalin ta daga zaman lafiyar da take son su samu kuma yake Sanya Mata waswasi a cikin zuciyar ta, da qyar ta samu barci yayi awon gaba da ita,

**********

Sa'ood na cikin barci yaji qaran faduwan Abu da sauri ya miqe ya fito parlo Yanda yake ganin haske, yaga Leesa kwance a qasa sai mutsu_mutsu takeyi,

A rude ya qarasa wurin ta ya tsunguna Yana tambayar ta lafiya itakuwa Bata ma San Yana yi ba sai juyi take tana faman cize Baki hannun ta riqe da cikin ta, zama yayi ya fara lissafi Nan ya gano matsalar ta ya tashi ya Shiga bedroom dinshi ya dauko Mata ruwa hade da magani sannan ya dawo parlor,

Miqa Mata yayi hade da fadin tashi ki Sha, da qyar ta iya daddafawa ta zauna sannan ya karbi maganin Tasha still ciwon Bai Bari ba, haka Sa'ood ya nemi wuri zauna Yana kallonta sai faman juyi take tana fitar da wani sauti cikin zafin ciwo  Amman bayi da damar taimaka Mata,

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now