"Ina Kuma zamuje?"

"Wurin 'yar iskan da zaka aura, zanje Naga da me ta fini ne da ka Zabe ta a kaina"

" Ki saurare ni Haleesa, nifa wasa nake Miki"

Daga Masa hannu tayi tare da rufe idanun ta " bani son Jin komai ya Sa'ood, kawai ka wuce mu tafi muje na kashe Mata warning mayya kawai su Basu Isa suga mutum bayi da aure ba sai su liqe mishi ce musu akayi bandaro kayi? Basu San kana jiran Sarwa bane Kuma ai Ina raye ban mutu ba, Dan haka wuce muje ka kaini wurin ta"

Ganin Yanda Haleesa ke daka ma yayansu tsawa yasa Nabeela da Daya saurayin suka qaraso wurin su Idris Kan tsayawa yayi daga nesa ya zuba ma sarautan Allah idanu don yasan Kan zancen,

"Me yake faruwa ne Haleesa?"

Juyowa tayi kaman zatayi kuka tace "momyn dady kiji fa Wai ya Sa'ood aure zaiyi gashi har ya daga gini Amman bamu sani ba"

" Ih, wani irin rashin hankali ne wannan? Auren naku ne Baki sani ba ko Kuma me?"

" A..a..auren su wa? Ban gane ba"

Sosa qeya Sa'ood yayi yace "sorry Haleesa nayi niyyan fada Miki kawai..."

" To bana yi, bazan aureka ba sai kaje ka rushe ginin dan ban yarda ba, ko Kuma kaje ka Sami ita yarinyar da kace kana so ka aure ta Amman bani ba" tana fadan haka ta juya fuu ta koma dakinta,

Dafe goshi yayi ya juya wurin Idris, Nabeela da dayan sai dariya sukeyi duk gidan Babu Wanda zai iya yi ma Sa'ood wani wargi Amman ga Haleesa yau ta saka shi a missed call Babu Yanda ya iya,

"Brother akwai matsala fa, na tona ma kaina Ramin mutuwa wallahi da nasan haka Haleesa zata dauki abin Nan da banyi ba, ni tsoro na ma kada da gaske takeyi ta fasa aure na please ka taimaka ka lallaba min 'yar qanwar ka"

"Kada ka damu Babu abinda zai faru insha Allah zata sauqo Kuma ba zata fasa auren ka ba na sani, yanzu muje ana niman mu aikin gaggawa ya tashi Mana"

Tunda suka fita Sa'ood Bai Kira Haleesa ba kasancewar Idris ya kasa ya tsare ya rabu da ita kawai idan ta Gama fushinta da kanta zata neme shi, gaba daya bayi cikin nutsuwar sa yana son Jin halin da gimbiyar nashi take ciki daga qarshe da Idris yaga ya matsa sai ya dauke wayar shi ya ajiya a wani wuri daban,

Haleesa Kuma ta hakince a Kan gado ta saka wayar ta a gaba tana jiran a Kira ta a Bata amsa Amman shiru, tun tana fushi har ta fara sauqowa yanayin ta ya fara sauyawa zuwa na damuwa tana tambayar kanta ko wani Abu ne ya Sami Sa'ood din?

Sai ta daga waya zata Kira shi Kuma sai ta fasa Bata so ya Raina Mata aji yaga kaman wani tana son shi da yawa ne, ganin har magriba ta gabato tun fitar su day safe yasa kawai ta dauki wayar ta Kira shi Amman har ya Gama ringing no response, tsaki taja tayi wulli da wayar daman tasan was kawai yake son yi da hankalin ta Kuma yaci nasara wurin hakan,

**********
7:42pm

Driving yakeyi Yana Satan kallon ta, ta hada gabas da yamma jira kawai takeyi yayi wani magana ta sauqe fushin ta a kanshi,

"Mi princesa kinyi karatu kuwa?"

Juyowa tayi ta murguda mishi baki ta juya Bata ce komai ba,

"Haba novio(sweetheart) kiyi haquri Mana a Haka zamuyi auren kina fushi Dani?"

"Ni kada ka sake cemun wani novio ko Nivea ce? Ba ganewa nake yi ba, Kuma  Akan me zaka ce zaka auri wata Bayan ka fadamin ni zaka aura sannan kace ba zanyi fushi ba, tun kafin ma na Shiga gidan naka har kayi min kishiya? Haba Dan Allah"

"I'm very sorry sweetheart wasa nake Miki wallahi ni bani son kowa sai Sarwa, yanzu dai Ina kin amince Zaki aure nin?"

Kawar da kanta gefe tayi tace " eh!"

"Kin fasa sai Nan da shekaru 4 Kenan?"

A hasale ta juyo tace "so kakeyi na janye ne ko me?"

"Aa ranki ya dade ba haka nake nufi ba kiyi haquri dan Allah, Amman ba dan halina ba ki saki fuskar ki please, I always tell you to put a smile on your face Yana Miki kyau sosai idan Kika Shiga jarabawa ranki a bace bazaki tuna abinda Kika karanta ba, nafi so ki haye salum alum daga munyi aure na saka ki a makaranta Mai kyau"

Murmushi tayi tace " Dan Allah ya Sa'ood zaka saka ni a makaranta da kanka?"

"Saima Wanda Kika zaba gimbiya ta ko a Nan ko Mexico duk wurin da kike son karatu Zan barki kije indai haka ne burin ranki"

**********
Bayan wata 2 Sa'ood ya kammala komai da komai na gidan aka saka aure Nan da sati 3,

tare da Haleesa aka zabi komai na gidan cikin samples da uncle Ishaq ya turo musu za'a kawo daga Mexico, IV na musamman ta saka akayi mata Wanda zata rabawa mutanen da suka kasance familyn ta lokacin baya sannan tana so ta biya gidan su Ameerah taga lafiyar ta ta Kuma je gidan alhaji Habib ta ceto bilkisu,

Yau ta Kama Sunday tasan Babu Wanda ba zata samu a gida ba cikin su, tun da safe take shiri with over excitement yau zata hadu da mutanen da suke Mata kallon qasqanci, zata koma jigawa Bayan tsawon watannin da ta dauka Bata waiwayi garin ba, Sa'eed dai ya Hana Salee zuwa saboda itama tayi nauyi Kuma an koma gidan jiya, ba qaramin baqar wahala take Sha ba, dole Zarah ne ta miqe da nata cikin take dawainiya da ita,

Tun 6 ta hada duk abinda zata buqata lokacin Sa'ood nata sharan barci, tana jinta daban harta iskan safiyar yau daban take jinshi, yau zata je unguwar su a matsayin Mai daraja zata je a matsayin cikakkiyar Mai asali Kuma 'yar halal she is going with her husband to be,

Qofar dakin Sa'ood taje ta dinga knocking kaman zata balla shi, Jin yanayin Yanda ake buga qofar yayi tunanin ma ciwon mamanmu ne ya tashi yasa a birkice ya tashi ya bude qofar zallan three quarter ne a jikin shi,

Daga sama zuwa qasa tayi mishi kallo Daya tayi saurin juyawa tana rufe idanun ta murya na rawa tace
"I'm... I'm..s.. sorry nazo d...dubawa ne ..naga ko ..kka shirya"

Rufe qofar Sa'ood yayi ranshi a bace, Haleesa ta daga mishi hankali wallahi Kuma sai ya Rama, cikin qanqanin lokaci ya shirya cikin jamfa blue color sai qyalli yake, ya sauqo qasa sukayi breakfast a tare sannan suka fita,

10:30 suka Isa unguwar su tun a bakin layin tasa yayi parking red Nissan rogue dinshi daga nanfa kallo ya koma sama, kowa ya tsaya yaga suwaye zasu fito daga cikin motan da ba'a taba Koda wucewa da irinta cikin layin ba,

Ganin Haleesa yasa kowa ya bude Baki Yana kallon ta da tsananin mamaki, yaran da kullum take was sadaka da safe suka zo dan nesa da ita suna Kiran sunan ta idan ta juyo tana kallon su sai suce "aunty Haleesa nine wane, ko nice wance" amman tsoro ya Hana su qarasawa wurin ta suna ganin kaman ba zata so hakan ba tunda tayi kudi gashi tazo da wani balarabe,

Ware musu hannuwanta tayi tana musu oyoyo aikuwa da gudu suka shige jikinta suna ihu, Nan layin ya dauki kuwwar sunan ta ta ko Ina aunty Haleesa kakeji,

Saida ta caski kudi a hannun Sa'ood tayi musu sallaman da har abada ba zasu taba mantawa da ita ba, Yara da manya kafin ta Kama hanyar gidan su ta shortcut din da suke bi idan sun dawo daga makaranta,

Abinda ta fara ganin qofar gidan su, wani mutum ne yake dirkan Lateefa Yana finciko ta waje, dafe goshi tayi Dan tasan maganar Daya ce 'sata' ta ja hannun Sa'ood suka Shiga cikin lungu sannan ta dauki dutse..............🧚

#vote
#share
#comment

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now