Kuka Haleesa ta saka tana bin wayan da kisses Bata taba tsammanin akwai ranar da zata zo wani yaso ta tsakani da Allah Kuma ya dauke ta da daraja ba, and that too an honoured man like Sa'ood, idan ta tuna rayuwar su ta baya sai taga kaman qarya ne Bai faru ba, those pain, those loneliness are all gone, itama yanzu tana da family kaman kowa yanzu suna da masoya Wanda rayuwar su ba zatayi inganci ba idan Babu ita da twin sistern ta a ciki,

Hawayen farin ciki ya kasa daina sauqo mata, sai Jin wani zafi da quna Yana taso Mata ta wani bangare na zuciyar ta hakan yasa ta sauqa daga gadonta ta shige bathroom ta dauro alwala tazo ta tada Sallah raka'a biyu tayi ta roqi Allah alkhairin tarayyan ta da Sa'ood tayi addu'oi sosai sai a sannan taji zuciyar ta ya danyi Mata sanyi ta hau gado ta kwanta Bata Dade ba barci yayi awon gaba da ita,

Washe gari
10:08am

Zaune yake tare da mamanmu a dining suna breakfast, minti 1_2 sai ya dubi qofar dakin ta Amman har yanzu Bata fito ba, wayan shi ya daga ya tura Mata text

"Good morning princesa"
"Hope kina lafiya Naga Baki sauqo breakfast ba I was worried please ki fito na ganki"

Haleesa Kuma saboda barcin da Bata samu Jiya da daddare isashe bane sunsha love da Sa'ood yasa yau ta makara Bata tashi da wuri ba, fitowar ta daga wanka Kenan taga message din Sa'ood da sauri sauri ta daure gashin kanta ta zurma Kaya ta daura hijab a Kai ko Vaseline Bata shafa ba ta dauki wayarta ta fita itama Bata San dalili ba Amman haka kawai taji tana son kallon shi,

Tun daga nesa take qare Mata kallo har ta qaraso wurin su ta gaida su cikin ladabi, sannan tayi serving kanta taja kujera ta zauna tana Jin irin kallon qurillan da Sa'ood yake Mata a jikinta,

A nitse ta fara cin abincin ta, taci yafi Rabin plate Amman Sa'ood Bai Gama ba Yana jiran yaji amsan da zata bashi Dan Allah ya gani barci rabi da rabi yayi jiya dan har mafarkinta saida yayi,

Ganin Bata da niyyan kammalawa yasa ya jawo wayan ta ya sake tura Mata text,
" Mi princesa kin tambaye ta?"

Kallon wayar tayi tayi murmushi hade da gyada Masa Kai,

Da sauri ya sake turo Mata "me tace?"

"Tace Wai anyi min wani mijin kayi haquri kawai"

A zabure ya dago Yana kallon ta har zaiyi magana ya tuna mamanmu tana kallon su sai sign ya fara Mata da Ido Yana wasu puppy eyes, langabar da kanta gefe tayi ta Dan turo Baki gaba kadan showing him ita ba laifin ta bane,

Sake tura Mata text yayi fuskar shi kaman zaiyi kuka,
"Yanzu kin amince a Rana ni da ke Haleesa? Zaki iya rayuwa Babu ni? Yanzu kin yarda zakiyi zaman aure da wani namiji ba ni ba?"

Ruwa ta kurba tana kallon text din wani nishadi take ji a ranta Wai ita ne yau ake nuna Mata irin wannan tsan_tsan so, ta ajiye tumbleren sannan ta tura mishi,

"Kana so in Saba ma umarnin mahaifiyata ne ya Sa'ood? Kaifa kace na dinga Mata biyayya yanzu Kuma Kai kake so na Saba Mata?"

Ya daga wayarshi zai sake Mata text mamanmu taja dogon tsaki tace "bani son Bata lokaci Kuna kusa da juna Amman Kuna Bata credit dinku, gata a gaban ka kayi Mata magana ba sai Kun ishe ni da qaran notification ba, aikin banza kawai"

Sum_sum Leesa ta miqe ta koma dakinta Sa'ood Kuma ya bar dining area ya koma main parlor dan yanzu bayi Jin zai iya zuwa wani wuri Bai samu amsan shi wurin Haleesa ba ya gaji!, text yaci gaba da tura Mata Amman ba reply, a Haka har mamanmu ta qaraso Kan kekenta,

"Chéri" ta Kira sunan shi a hankali, dagowa yayi Yana kallon damuwa shimfide a fuskar shi,

"Yaushe zakayi magana ma uncle dinku a fara hidiman biki? Dan bani so a dauki lokaci"

Kallon rashin fahimta yayi Mata sannan yace
" Tace Wai kinyi Mata miji fa! Wai da ta fada Miki kince nayi haquri"

"ni? Yaushe mukayi irin wannan Maganar da ita?"

"hakan ya nuna Bata so na Kenan ko?"

"Wa ya fada maka? Ka daiyi abinda na fada maka ka Sami baba alhaji ayi magana sai ka fara daga gini Amman ba'a gaban gida na ba kaji na fada maka, ni zanyi komai na wurin uwa, my second son is getting married I'm so happy nidai ka kula da sirika da kyau, kada ka kuskura a kawo qaran ka wuri na domin ba zanyi maka da Dadi ba ko kadan" tana fadan haka ta juya Bata bashi daman magana ba,

Tana shigewa ciki Sa'ood ya daga tsalle hade da dunqule hannun shi ya naushi iska Yana mai_maita alhmdllh, Kuma ya saka a ranshi sai ya Rama abinda Haleesa tayi mishi, ba zata San da maganar auren Nan ba Saidai taga ana yi,

Sa'ood Bai tsaya jinkiri ba ya samu baba alhaji da maganar, basu tsaya wani dogon zance ba saboda wannan al'amarin tsohon alqawari ne, ya Kira uncle Ishaq ya shaida mishi abinda yake faruwa, daga Nan Sa'ood ya bada sadaki a take a wurin, suka bashi go ahead ya fara shiri Suma zasuyi nasu na iyaye, aure Kuma sai ginin su ya kammalu,

Cikin qanqanin lokaci zancen auren Leesa da Sa'ood ya karade Mailafiya family saidai ya gargadi kowa kada su sake su fada Mata abinda ke faruwa, Haka ake ci a cinye Bata sani ba,

Bayan kusa wata 1 gini har ya fara nisa, Wanda suke yinshi tsakanin part din momy da na mamanmu Kuma a gaban na Idris, randa aka fara aikin mamanmu tayi fada kaman ta ari Baki Saida tayi mishi kashedi Akan kada yayi gini kusa da nata Amman Sa'ood kaman Mai kunnen qashi,

Bangaren Haleesa Kuma yanzu Bata wani Gane mishi sosai, sun kusan yin second term examination ya biya Mata waec da neco ya saka ta you ba tare da wani qwaqqwaran dalili ba,

Karatu yasha kanta sosai kaman Yanda shima hidima da aiki yasha kanshi Basu samun time sosai idan ba wurin breakfast ba da Kuma idan ze kaita makaranta, wani lokacin har tayi barci Bata ganshi ya dawo ba sai da safe idan ta tashi taga good night text dinshi Wanda ya zamo kaman wajibi kullum Babu fashi,

Bangaren soyayya Kuma Babu fashi har gobe Yana nuna Mata irin tsananin son da yake mata ko yaushe Yana kashe Mata kaifin qwaqwalwa da kalamai, tausasawa, da kyautatawa Kuma harwa yau Bai fada Mata an bashi ita ba, ya dai zauna a matsayin Mai baran soyayya,

Zarah da abin cikin ta kula ta musamman suke samu daga wurin Salee da Sa'eed, irin Yanda suke Mata gata har wani lokaci taken ji kaman har abada kada ta aifi cikin jikinta Dan tasan maybe albarcin sa take ci, ko motsi tayi sai sun duba sunga ko lafiya ko a cikin ta na farko Bata samu irin wannan kulan ba,

Yau dai Haleesa ta kasa haquri ta fito jikin ginin da mutane machines suke faman yi ba dare Babu Rana har an kusa gamawa, hango ta tsaye riqe da qugu yasa Sa'ood qarasowa Yana danne dariyar sa don daga ganin ta a hasale take,

"Yaya dai princesa, tsayuwar me kikeyi a Nan? Kuma waye ya Bata Miki Rai naje na same shi?"

Gwada building din tayi da yatsa tace "wannan gidan waye ne?"

Saida yayi Dan murmushi sannan yace "nawa ne aure zanyi.........🧚

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now