Cikin suratul duha aya ta 9 Allah yace
فأما اليتيم فلا تقهر
Amma maraya karka rinjaye shi (karka cinye mishi dukiyar shi ko ka Hana shi katabus)

Cikin suratul ma'un aya ta 1 zuwa na biyu Allah yace
الرؤيا الذي يكذب بالدين
فذلك الذي يدعو اليتيم
Kabani labarin Wanda take qaryata addini
Wannan shine Wanda take tunkuda maraya

Sannan cikin suratul nisa'i Aya ta 10 Allah ya Kuma cewa
إن الذين يأكلون أموال اليتامى ظلما إنما ياكلون في بطونهم نارا و سيصلون سعيرا
Duk Wanda suke cin dukiyar marayu saboda zalunci iyaka wuta sukeci a cikin cikkunan su Kuma qarshen su wuta zasu Shiga wutar sa'ira,

Wa'iyazubillahi lallai wannan ya Kai qarshen asara ka rasa lahirar ka, kayi asaran duniyar ka Kuma har qarshen rayuwar ka mutane ba zasu dauke ka da daraja ba,

Haka malam abdulhameed ya dinga zaburar dasu, ya dauki kusan mintuna 30 Yana wa'azantar dasu Akan hakkin maraya kafin salon ya juya ya koma ga hakkin iyaye a Kan 'ya'yan su nanfa Haleesa ta Shiga cikin damuwa Jin Yanda ake kwatanta azabar da Allah yayi alqawarin za'ayi ma Wanda ke Saba ma iyayen sa musamman mahaifiya, ya kawo ayoyi da hadisai da dama Wanda ke nuna girma da darajan iyaye,

Lokaci daya Haleesa taji fitsari ya cika Mata mara saboda tsoro ta kalli mamanmu dake opposite dasu a Kan wheelchairn ta hankalin ta kwance tana sauraron wa'azin da akeyi, saƙe_saƙe ta fara a ranta tana jaddada cewa Wannan itace matar da ta dauki cikinsu wata Tara tayi naqudan su biyu sannan Bayan ta Gama dawainiya da su aka dauke su yaye su batayi ba, Bayan ta Shiga tsananin tashin hankali ta same su Bayan tsawon lokaci sannan itakuma ta qara daura Mata wata damuwar, Bata dauki mahaifiyar ta da daraja ba Bata taba wani yunquri Dan farnta Mata ba, Bata tantance alaqa da magananun da takeyi da ita Wanda ita kanta tasan Basu dace ba, mamanmu it kadai ta rage Mata a duniya cikin iyayenta Amman tana was da damarta na samun rahama daga kyautata mata,

"Babu babban rahama da Jin Dadi na duniya da ya wuce ka tashi kaga iyayen ka suna raye Kai da wulaqanta har abada, Babu babban asara Bayan rashin tauhidi sai Saba ma iyaye, Babu shakka Mai Saba ma iyayen sa indai ba Akan abinda ya kauce ma shari'a bane ɗan wuta ne, shi da rahaman Allah sunyi hannun riga domin fushin Allah yana daga cikin fushin iyaye"

Zufa taji Yana karyo Mata ta ko Ina ta riqe gefen dankwalin ta da Bai samu zama a kanta ba ta fara fifita dashi hakan ya jawo hankalin Sa'ood gareta domin sanyi ya fara shigowa wasu har sun fara saka kayan sanyi,

Dan sunkuyowa yayi Yana leƙa fuskarta yace "lafiya Haleesa?"

A zabure ta dago tana kallon shi sai rarraba idanu takeyi tace " na Shiga uku ya Sa'ood bazan Shiga aljannah ba"

"Kai! Wa ya fada Miki haka?"

"Baka ji ba? Ance Wanda ya Saba ma iyayen shi ɗan wuta ne, Kuma Ina tsoro Sosai wallahi bani so in Shiga wuta"

Ganin hankalin su Sa'eed ya fara dawowa kansu saboda ana wa'azi suna surutu yasa yace mata "ki bari idan munje gida sai muyi magana Amman ba zaki Shiga wuta ba idan Allah ya yarda"

Gyada kai tayi ta gyara zaman ta taɓa nusar da kanta ba don hankalin ta ya kwanta ba don maganar ya tsaya mata a rai, tabbas a islamiyyan su ana yawan fada musu illar saba ma iyaye amman Baga taɓa fitowa ɓaro_ɓaro aka ce mata zasu shiga wuta ba,

Har aka gama taro lafiya aka watse hankalin Haleesa bayi jikin ta, bayan sunyi sallar magriba aka kawo musu abinci irin wanda kowa da kowa zai ci a orphanage din aka shinfida musu tabarma a basketball field kowa ya zazzauna a qasa ana cin abinci ana nishadi, Za hada kan yaranta tayi suna cin abinci a plate daya ta gefen idonta take leqo Sa'eed Yana feeding din Salee, kawar da kanta gefe tayi ganin abin nasu yana so ya wuce mizani daga cin abinci sun koma wani abu daban saboda suna can gefe wurin da babu wadataccen haske sosai a wurin,

Suna gama cin abinci suka sauro alwala a wurin sukayi Salman Isha sannan suka fara zagaye orphanage din suna duba gyaran da aka yi, manyan cikin wanda suka san tsarin wurin ne suke nuna ma su Haleesa wurare saboda renovation akayi ba'a canza tsarin wurin ba, Ita dai nutsuwarta bayi jikinta ta ƙagu a koma gida Sa'ood ya fada mata yanda zatayi ba zata shiga wuta ba,

9:27pm
Suka shigo gidan, sallama sukayi kowa ya shiga part dinsa, Haleesa na shiga parlorn mamanmu ta zube a kan guiwowinta tana kuka, sautin sheshsheqar ta yasa mama da ta kusan shigewa dakinta ta biyo tana kallon ta, hankali a tashe ta danna kekenta ta qarasa wurinta tana tambayar ta abin da ya same ta,

Riqo hannun ta tayi ta qanqameshi cikin nata cikin kuma tace "mama dan Allah ki yafe min, I'm very sorry" hakan yayi daidai da shigowar Sa'ood parlorn ya tsaya yana kallon su cike da mamaki,

"I know that I'm not a good daughter, bani Jin maganar ki ina muku rashin ji sannan ina yawan saɓa Miki amman wallahi daga yau na Bari bazan sake ba wallahi dan Allah koyi haquri bani son in Shiga wuta"

Stunned mamanmu ta tsaya yana kallon Sa'ood, bata san wannan aiki nashi ne ko kuma wani abu daban bane amman koma menene tana farin ciki sosai Finally ta samu cikakkiyar iko akan Haleesa,

"Kinji mama? Allah nayi alqawari bazan sake ba ki yafe min Please"

Ɗan dariya tayi mai sauti ta saka hannun ta duka biyu ta fari ta sannan ta rungume ta tana zaune a kujerar, sunfi 1 minute a haka sannan ta fari ta tana qare mata kallo still fuskar ta da murmushi ta shafa kanta
"Allah yayi Miki albarka Haleesa yasa koyi ingantacciyar rayuwa, uwa bata taɓa fushi da ƴarta ke ƴar aljannah ce cikin hukuncin Ubangiji"............🧚

*Yauma dai manage😁*
_Gobe idan na samu dama zan fanshe insha Allah_

*Sorry for the errors Ummu Nana ba Malama nace😅*

_Keep voting_
_Keep following_
_Ummu najma loves you so much_😘😍

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now