"Makaranta nake so a maidani"
"Daman za'a maidake makaranta Mana Amman ki bari mu sami nutsuwa tukunna insha Allah karatu sai kince kin gaji"

"Ni gaskiya yau nake son komawa na gaji da fitintinu da matsalolin cikin gidan Nan I cannot bear it anymore, kowa Yana gani ana abubuwan da Basu dacewa"

Gyara zaman hannun riganshi yake yi ranshi na tafarfasa rashin da'an Haleesa har ya wuce kansu yayun ta ya koma Kan mahaifiyar ta? A jiya ya dauka cewa ta canza hali ne Ashe kuwa yayi kuskure dan ajiye shi tayi na wucin gadi, ya kuwa zamo Mata tamkar Dole ta ajiye wannan dabi'un ko tana so ko bata so,

"Lower your voice Haleesa"

"Why would I? Tana gani ana tauye Mana hakki Amman tana shiru" ta fada tana nuna mamanmu "Kai daman banyi tsammanin zaka goyi Bayan mu ba duk da ka gwada hakan Amman dole zaka Gaza a hanya saboda Sa'eed 'dan uwan ka ne,

Duk abinda za'ayi Mana tana kallo Amman sai tayi shiru, why won't you fight for your family mama? Meyasa ba Zaki tsaya tsayin daka a Kan 'ya'yan ki ba ana juya 'yan uwana Yanda aka so Amman Babu Mai iya cewa komai saboda ke an maida mu qaramin danga Mai dadin qetara ko wani Kare da doki yazo ya watsa kashin sa kanmu don yasan ba zaki taba hanawa ba"

Zuwa wannan lokacin ran Sa'ood ya Kai maqura wurin baci Amman Yana qoqarin controlling tempern shi saboda Yana gaban mamanmu ne ba don hakan ba da tuni yayi qasa_qasa da Haleesa shi Sam bayi daukan nonesense ko a wurin waye kuwa,

"Ki rufe min baki kafin ranki ya baci"

A tsawace tace "bazan rufe ba ya Sa'ood ko me zakayi saidai kayi Amman tozarci shine abunda bazan taba juran gani anayi ma want nawa na qyale ba, a gaban 'ya'yan ya Idris Sa'eed yayi mishi duka matar shi tana kuka Suma suna kuka baka........"

Wani tsawa da Sa'ood ya daka Mata yasa ta qame tsamm Dan har cikin qwaqwalwar ta taji shi ta runtse idanun ta ganin Yanda ya daga hannu Yana Shirin kafta Mata Mari da sauri mamanmu ta dakatar dashi

"Por favor no le des una bofetada(Dan Allah kada ka mare ta)" bai mare ta ba Kuma Bai sauqe hannun sa ba ya tsaya Yana qare Mata kallo cikin bacin rai gaba daya yayi jaa lokaci Daya jikin shi na tsuma har wani karkarwa yake yi,

Ta sake cewa "por mi bien (for my sake) please"

a hasale ya sauqe hannun shi sannan yayi snapping yatsun shi biyu Yana gwada ta da na tsakiyan da qyar ya samu maganar shi yake fitowa shima ciki_ciki,

"Idan ke Baki dauke ta a matsayin mahaifiya ba ni tana da matsanancin daraja a wurina Kuma Ina mutunta ta fiye da rayuwata, wannan ya kasance na farko Kuma na qarshe da zanji muryar ki ya haura nata idan ba haka ba duk abinda nayi Miki ke Kika siya da kudin ki, babu Wanda zai wulaqanta ta ya zauna lafiya matuqar Ina raye wallahi tallahi, ya zamo Miki dole kiyi Mata biyayya ko kinqi ko kinso, ko da wasa iyaye ba abun wasa bane kima gode ma Allah kina da shi, Kuma na dawo na samu kinci gaba da wannan Maganar kiga Yanda zamu qare dake"

Yana kaiwa Nan ya wuce ya fita ko breakfast baiyi ba a hanya ya hadu da Sa'eed Yana shigowa part din daga gani haquri yazo bawa mamanmu Yana jinshi Yana mishi magana Amman yaqi kulashi don shima haushin sa yakeji, da hanzari ya qarasa jikin motar da zai tafi aiki da ita ya karbi key a hannun driver ya Shiga ko warming baiyi ba ya zuge ta a guje ya bar gidan,

Sosai yake falla uban gudu a titi ya rasa ma tunanin me zaiyi 'daya kowa ya hada mishi caji a ka sun saka shi cikin tension baima San ta Ina zai fara ba, rage gudun shi yayi ya sauqa yayi parking a gefen hanya sannan ya dauki wayar shi ya Kira Adam bugu biyu ya dauka,

Murya qasa_qasa yace "hello barrister kana gida ne?"

"Aa na fita office yau da wuri saboda akwai wasu ayyukan da nake so na qarasa inason zan dauki hutu ne mu bar qasan tare da iyalina any problem?"

"Inaso mu hadu da Kai ne akwai magana Mai muhimmanci da nake son nayi da Kai so I'm coming to your office"

" Akwai wani matsala ne SD? Naji muryar ka wani iri ba Yanda na Saba ji ba ka fada min menene matsalar?"

Numfashi Mai zafi Sa'ood ya furzar Yana Jin takaici yace "barrister I choose the second option mu saka gwamnati cikin case dinmu a dawo Mana da hospital da orphanage yanzu me zamu fara a Kai?"

"Subhanallahi ai wannan ba maganar da za'ayi shi a waya bane ka qaraso sai mu yanke hukunci Allah yasa dai lafiya"

Katse Kiran Sa'ood yayi ya kunna motar shi ya nufi office din Adam Yana Shiga ya same shi a zaune sai lokacin shima yake breakfast Daman zaman jiran shi yake yi, basuyi wani dogon gaisuwa ba Adam yace

"Bari a kawo maka breakfast ka qara a Kan Wanda kayi a gida Dan nasan tunda mama tana tare da Kai ga amarya Babu zancen zama da yunwa"

Tsaki Sa'ood yaja in serious tone yace "joke aside ka dai San ba qaramin Abu bane ya kawoni nan idan zaka iya ka taimakeni please inason abun nan ya dawo Mana cikin sauri"

Sipping tea dinshi Adam yayi Yana kallon Sa'ood da wutsiyar Ido he seems restless, ya ajiye cup din sannan ya tattara dukkan hankalin shi gareshi,

"SD kaman Yanda na fada maka a baya wannan zabin Yana da hatsari sosai Yanda baka tsammani, ni nama kawo maka option dinne ba don komai ba sai dan na nuna maka cewa binciko Wanda yayi wannan crime din shine yafi, ku dada zurfafa bincike Zaku gano koma waye tunda Ina da tabbacin Yana kusa da ku, shi ya cancanci hukunci ba ku ba shi ya Kamata ya kasance cikin tsoro da fargaba ya Shiga cikin tashin hankali ba familyn ku ba"

" Na sani barrister Amman muna buqatar orphanage dinmu at the earliest na samu labarin Yanda yaran suke Shan wahala Basu samun kulawa Kai kana ganin na tsaya Bata lokaci na a Kan binciko mutumin da bamu San yaushe zamu gano shi bane? Ko Kuma muyi wani abu dan ceto rayuwar marayu"

Jingina jikin shi da kujeran da yake zaune a Kai yayi ya zabga tagumi Yana nazarin Sa'ood, daga look dinshi ya Gane Yana boye wani abu duk wasu sign na rashin gaskiya ya bayyana tattare dashi

"kana maganar marayu ka manta da familyn ka, sati biyu ne kawai da dawowar ku guri daya kada kayi kasadan sake jefa su cikin matsala think about it"

"nasan da haka Kuma na dauki alhakin komai da komai kaidai kasan Yanda saqon mu zai Isa gurin gomnati at the earliest"

" Ok Amman gaskiya zai dauki lokaci qarancin lokacin da zai dauka kafin mu samu feedback 3 weeks ne, zanyi komai da komai duk abinda ake ciki zaka jini"

Miqewa Sa'ood yayi ya dauki car keys dinshi "ni zan wuce office said naji daga gareka" suka sake shaking Sannan yayi mishi sallama ya fita,

_Manage please🤒 zazzabi nake fama dashi Amman insha Allah page din gaba zaiyi tsayi_ thanks

*Ummu Najma ce*😘

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now