" It's not about trust SD ance idan raqumin ka ya Bata ka duba har cikin tandun kwalli so kaima ba abun yarda bane Akan wannan case din ballantana Idris in har dai kuason dawowan hospital da orphanage hannun ki soon you have to act fast, yanzu ka tashi muje muyi Sallah kada mu rasa jam'i" Adam ya fada Yana tashi daga mazaunin shi,

A maimakon Sa'ood ma ya tashi sai ya kwantar da kanshi jikin kujeran na tsawon minti 2 ya daidaita nutsuwar shi sannan ya tashi Yana sauqe numfashi,

"Muje barrister inaso idan Mun dawo ma na dauki Haleesa mu tafi gida kasan yau zamu koma tun safe ake ta faman gyara harda dry paint anyi Mana an canza Mana wall papers saboda komawan gaggawa zamuyi yanzu haka ma tun 3:00 wasu suka Isa mu kadai ake jira"

Suna dawowa daga masallaci Sa'ood yayi sallama wa matar Adam yace Leesa ta tashi su tafi, Babu Yanda matar batayi ba a bar Mata Sarwa tayi Mata Koda kwana Daya ne Amman qirmushishi yaqi haka kawai ba za'a raba shi da ita ana zaman lafiya ba,

4:27pm
Suka Isa gate din mansion dinsu, with amusement Haleesa take qarewa gate din gidan kallo, wato cinikin ta da sukayi a wancan gidan baiyi mishi bane shine ya kawota Nan saboda mutanen gidan sunfi kudi sai su sayeta a Yanda yake so to wallahi Bai Isa ba,

Juyawa seat din baya tayi ta dauko qafar Jan takalmin ta guda Daya da suka siya a mall ta saita daidai tsinin takalmin a fuskar Sa'ood kaman zata bula mishi Ido, saurin ja da baya yayi dan yanda ta kawo Masa ya Bashi tsoro badan ya Ankara da wuri ba da idanun shi sun Dade da tsiyayewa

"Menene haka Haleesa? Baki gani ne kike niman cire min Ido?"

" Ba na fada maka da Raina da lafiya ta Babu Wanda ya Isa ya siyar dani ba? To wallahi ko ka juya da motan Nan yanzu kokuma kaga abinda zai faru dakai"

" Ke! Gida fa muka zo wawiya kawai ki duba can ki gani" ya fada Yana nuna Mata wani sign board a jikin gate Wanda aka rubuta *Mailafiya mansion* a jikin da golden color rubutu"

Cike da kunya ta ajiye takalmin hannun ta tana murmushin dole, Sa'ood ya ja tsaki ya Danna hancin motar cikin gidan Bayan an wangale mishi gate Dan ba'ayi registering plate numbern shi ba ballantana ya budu da kanshi, tana ganin hankalin shi bayi kanta ta Kama dungurin kanta tana "stupid, idiot" a hankali Yanda bazai ji ba "duk laifi na ne gashi na jawo ya zage ni"

Girgiza Kai Sa'ood yayi Dan yaji ta Sarai Leesa sai godiya ma Allah Dan duk inda take tunanin ta tawuce Nan, a parking lot ya faka nashi motan Yanda aka ajiye wasu tamfatsa_tamfatsan motoci masu zafi makanikai suna ta faman gyara wasu ana canza mysu tayoyi wasu fenti ake sake musu wasu Kuma ana duba injinan su, haka dai Sa'ood ya gaggaisa dasu sama_sama Amman ita ya hanata magana suka wuce ciki,

Daga farkon gate na biyu kakejin dariyan yara suna tserwn Keke wasu Kuma suna was a playground dinsu na musamman dake cikin gidan da hayaniyan manya ana ta Kai koma kowa da fara'a manne a fuskar shi zuciyoyin su Yana musu 'dadi,

wani iska Mai Dadi yake Jin Yana bugashi, he's having inner peace rabon shi da yaji kwanciyar hankali da farin ciki yaga gidan su a cike happiness everywhere shekaru 17 da suka wuce Kenan a da kanma abun baikai haka ba Dan yawanci yara_yaran Nan daga baya aka haife su,

Haleesa kuwa bakinta kamar zai tabo qasa saboda al'ajabi ita fa ko a mafarki Bata taba ganin gida irin wannan ba idan ba ta 'bata gani ba ai ya kusa Rabin unguwar da take a day ga gini kaman zai tabo sararin samaniya, ko ta Ina daga interlocking sai grasses yaran turawa suna was a Kai, Tabb duniya juyin Masa Wai ita da Bata da ikon Shiga kowani gida a unguwar su Amman itane yau aka shigo da ita wannan babban gida Mai tarin daraja, ikon Allah kenan!,

Haka yaran suka dinda rugowa da gudu suna musu oyoyo Sa'ood Yana daga su sama Daya Bayan daya har suka shige part din mamanmu,

Zaune take a armchair nurse ta miqar da qafafuwan ta a qasa ana danna Mata su, sallamar su yasa duk hankalin su yakai garesu kallo Daya mamanmu tayi wa Haleesa ta gane ta Amman saita bigger da tamayar Sa'ood
"Cariño Kai da waye haka? Maraba da zuwa baquwar mu? Amma a Ina ka barmin yarinya ta?"

Dariya dukan su biyu suka yi yace " tace ba zata biyo ni bane shine na canzo Miki da wata 'yar"

" To madallah hakanma yayi tunda dai wacan ta qi ni ai ga Haleesa Nan tayi kwalliya tazo wurina Kuma tayi kyau kamar wata sarauniya"

Qarasawa wurin ta tayi ta zauna a qasa ta fara Taya nurse din matsa mata dayan qafan suna yi suna Hira jifa_jifa Sa'ood Kuma ya shige dakin sa dake part din domin yin wanka, suna zaune sajida ta shigo aika tana sanye da Riga da wando sai hula.a kanta saboda aikin gyaran da sukeyi, maganar ta ne ya tsaya sakamakon hango Leesa da tayi gaba daya ta canza kamanni,

"Haleesa!" Ta Kira sunan ta cike da mamaki saboda tasan ta baro Salee kwance a part din momy, dagowa Leesa tayi tana kallon ta ta amsa da "na'am"

Da gudu sajida ta fita ta shelanta ma sauran 'yan matan gidan yau ga Haleesa tayi kwalliya suka shigo part din da gudu suna kallon ta kaman yau suka fara ganin ta, ya Babu hijab dinnan da ko yaushe take manne dashi da kuma maiqon Vaseline da kullum fuskarta yake yi kaman Bata San powder ba, daga Nan suka dauketa suka fita zaga gidan aikin su Kam ya tsaya saidai maids su qarasa,

5:31pm
Fitowa yayi sanye da tank top da cargo Jean ya qarasa wurin da mamanmu ke kishingide da casbi a hannun ta Tana zikiri, zama yayi shima a qasa Yana fuskantar ta ya shagwabe fuska kaman Yanda yake Mata tun lokacin baya yace
"Cariño I'm hungry tun safe rabo na da abinci a Dan nema min wani Abu naci please"

Daddafawa tayi da hannunta ta tashi ta zauna "ka zauna Bari na saka kulu ta kawo maka inyaso sai ka dauka ka tafi dashi dakin ka nasan zaka fi son ci a can" ta daga wayan ta zatayi Kira yayi saurin dakatar da ita Yana wani hade rai,

"Aa cariño yarinyar ki me takeyi da ba zata kaimin dakin nawa ba sai nayi wani zaman jiran kulu?"

" Kaga mutumin Nan da rigima, an dawo Kenan zaka fara isata ka Hana ni sakat ko? Kai ba zakayi aure bane ka huta Nima na huta da fitinar ka? Haleesa ni banma San wace duniyar take ba Kuma a siyayyan ku Kun manta da waya ballanta na Kirata ta shigo"

Dan qaramin tsaki yaja shima sai yanzu ya tuna, abinda ya Kamata ya fara siya Mata Kenan saboda Yana samun Daman Jin muryar ta a kowani lokaci amman yanzun ma Bata baci ba zaisan abin yi,

"Ki kwantar da hankalin ki cariño insha Allah kwanannan zanyi aure Kinga a can gaban part dinnan za'ayi min gini Ina kusa dake Babu Wanda zai dauke no daga gareki"

Riqe Baki tayi cike da mamaki tace " ja'iri wato da 'yar tawa ce zakayi aure kayi gini gaban part Dina saboda baka da ta Ido ko? Ka nunamin gaka surikin zamani? To kaci gidanku maras kunya" ta fada hade da mishi danqwale,

Sosa qeya yayi Yana dariya yace " cariño Yaya akayi Kika sani ko wani ne ya fada Miki?"

" Wani wa? Yanzu sai wani ya fada min kana son wani Abu Sa'ood? Saikace bani na raine ka ba? Tun kana qaramin yaro by mere looking nake gane idan kana son wani abu, I can see love for my daughter clearly in your eyes ko kowa Bai fada min ba nasan kana son Haleesa Kuma so Mai tsabta nayi farinciki da hakan sosai, Amman kabi a hankali don ba'ayi ma so SHIGAR SAURI kabi komai a hankali kana amfani da zuciyar da ba da qwaqwalwar ka ba insha Allah zata samu abinda kake marari, yanzu tashi kaje zan turo ta da abincin"

Tashi yayi Yana dariya sai rufe fuskar shi yakeyi da tafin hannun shi a dole Yana Jin kunya, Bai qara magana ba ya wuce dakin shi ya zura jallabiya akan kayan jikin shi sannan ya dawo parlorn shi ya zauna Yana jiran shigowar Leesa,

Kulu mamanmu ta aika ta Kira Leesa Babu Bata lokaci tazo tace Mata ta shirya tray din abinci ta kaiwa Sa'ood, batayi musu ba ta shige kitchen kulu ta nuna Mata Yanda ake hadawa ta saka Mata plate da bowl da fork da spoon a Kai sannan ta dauka ta wuce dashi parlorn shi,

Da sallama ta Shiga ta dungure mishi abincin ta juya zata fita yayi saurin Kiranta
"Waye zaiyi serving Dina? Kin ajiye min abinci kin Kama hanyar ki zaki tafi"

" Nifa cemin akayi na kawo maka abinci kawai na fito Kuma gashi na kawo sai anjima" ta fice daga parlorn ta koma wurin mamanmu tayi zaman ta,

Tana ganin Kiran shi a way non-stop Amman taqi dagawa tasan Leesa ne batayi mishi abinda ya Dace ba don daga ganin Yanda ta fito tana cuna Baki tasan ta zuba rashin kunyar ta ne kuma ya Kira bane ya koka tunda yanzu tasan da maganar Kenan,

Amman ba zata taba bawa Sa'ood daman complain tun yanzu ba, dole idan Yana so ya koyi juriya da haquri yasan Yanda zai iya tafiyar da al'amuran shi ba tare da taimakon wani ba Kuma alqawari ne a kanta ba zata taba yi ma Haleesa dole ba.................🧚

*Ummu Najma ce😘*

KAMA DA WANE....(Completed)Où les histoires vivent. Découvrez maintenant