Mutumin ne ya fara cewa "welcome back SD we miss you so much"

Murmushi yayi yace "na sani barrister it's been long since we've met, I missed your company Yaya labarin future KD governor?"

" Hmm al'amarin Ameer sai a hankali yaje ya daura ma Kashi abunda yafi qarfin sa"

" Ko Kuma mace ta daura Masa abinda yafi qarfin sa ba?" Sa'ood ya fada Yana dariya "ai nasan Yanda take kurari Yana wani na qarya idan ya Shiga hannun mace wallahi sai yayi sanyi"

" Wa yace maka? Matar da washe garin auren ya sake ta!!"

Zaro Ido Sa'ood yayi cike da mamaki yace "subhanallah! A Kan wani dalili? Me tayi Masa da ya dauki wannan danyen hukuncin haka?"

" Haba SD kaman bakasan waye Ameer ba? Babu abinda baiwar Allah tayi mishi akan wannan mummunar aqida da familyn shi suka ginu a Kai yasa ya lalata rayuwar 'yar mutane, yanzu da kada na cika ka da surutu mu Shiga ciki sai mu qarasa tattaunawa"

" Tare da baquwa nake tana mota bari nayi Mata magana ta fito ka Shiga zamu biyo ka a baya"

" Oh! My! God!!! Babban tuzuru yau anyi abun Kai, kace Kuna qwato sunan ku ka santamo baby? gaskiya bana za'ayi ruwan sama da qanqara Bari na qarasa in gaisa da amaryan tamu na kwashi karama" ya fada Yana qarasa jikin windown Leesa ba tare da ya tsaya Jin ta bakin Sa'ood ba,

Dan dafa saman windown yayi Yana kallon Leesa dake ciki ita Kuma hankalin ta Yana Kan Sa'ood dake qarasowa inda suke,

"Amarya Ina wuni"

Kaman an shuka dusa haka Leesa ta zauna bata juyo ba balle yasa ran zata bashi amsa hasali ma Bata San da ita yakeyi ba, juyawa wurin Sa'ood yayi yace "SD ko ba ita bace amaryan?"

"Itace Mana me ka gani?"
" Kurma ce? Naga Ina ta magana Bata kulani ba"

Kyalkyalewa da dariya Sa'ood yayi, yasan wannan kadan ne daga shu'umancin Leesa taji shi Kuma taqi amsawa, dafa shi yayi yace "barrister Sarwa ce fa"

"What!!! Like seriously??? I mean yaushe kuka same su? A Ina? Ta Yaya?"

" Ikon Allah kawai, Amman munsha wahala sosai saidai alhamdulillah buqata ya biya"

Cikin tausayawa yace "Allah sarki! Amman Yaya maman su? Ta samu waraka ko? Gaskiya na tayaku farinciki lokaci Daya komai sun dawo dai_dai Allah ya dada kiyayewa"

" Ameen barrister, yanzu dai qafa kawai ya rage Mata Amman Baki da sauran gabobin jikin ta alhamdulillah tana iya amfani dasu"

" Wacece Daya a cikin motar? Saleeha ce ko?"

" No Sa'eed yayi min snatching din Saleeha wannan Haleesa ce, ka sake Mata magana maybe idan taga dama zata kula ka"

Sake komawa jikin windown ta yayi Yana fadin " kace madam din tamu Yar rigima ce" ya sunkuya daidai Yanda zai ganta da kyau yace "Ina wuni aunty Haleesa"

Saurin Juyowa tayi tana kallon shi, wannan magidancin ne zoqai_zoqai dashi zai Kira ta aunty? Amman ya ma Raina Mata hankali wani ma yaji Haka idan Bai ganta ba zaiyi tunanin wata tsohuwa ce tukuf, a taqaice ta amsa mishi da "wa'alaikumus Salam"

Dan Sosa qeya yayi Yana dariya sai yanzu ya Gane inda kwafsa yace "Assalamu alaikum, sorry for the misconception sunana Adam ni abokin yayanki ne if you don't mind ki fito mu Shiga ciki I will like to introduce you to my wife"

A hankali ta zuro qafarta Bayan ta bude qofar ta fito, suka qarasa inda Sa'ood yake tsaye tare da Adam sannan yayi gaba ya barta ita da Sa'ood sun biyo shi a baya har cikin gidan,

Matar shi da tuntuni ya fada Mata Sa'ood yazo ta zauna a kusa dan tarban shi ne ta miqe ganin sun shigo tana musu barka da zuwa,
"Honey look who's here" Adam ya fada Yana nuna Haleesa,

Kallon rashin sani matar tabi Haleesa dashi tana tambayar Sa'ood "who is she?"

"It's Sarwa, wannan itace babban Haleesa"

Kare bakinta matan tayi da hannun ta with amusement tana kallon Haleesa "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un I can't believe it, yaushe aka same su? A Ina?"

" Kinaga Nima dai tambayar da nayi Masa Kenan Amman har yanzu ban samu amsa ba tukunna, yanzu dai ki Kira yara suzo su gaida uncle dinsu, Bari muje parlor na"

Yaja Sa'ood suka tafi yabar Haleesa wurin matar Adam, Babu laifi Leesa ta sake suna 'dan taba Hira Amman duk Yanda ta kada ta rawa taqi taci komai dan already a qoshe take, tayi excusing kanta sannan ta kaima Sa'ood abinci da drinks ta tura yaran ta uku duka maza suka gaida shi sannan suka fito suka Basu wuri,

**********

"Wai nikam kayi min bayani please SD ta Yaya akayi Sa'ood ya kwace Saleeha daga wurinka Bayan kowa yasan takace?"

Matsowa kusa dashi Sa'ood yayi yana kallon cikin idanun shi looking serious yace "ba abinda ya kawo ni ba Kenan Adam, nazo ne Akan maganar hospital kasan cewa a qarqashin Mailafiya hospital akayi registering Mailafiya orphanage Kuma duk wani riba da aka samu a asibitin wurin yake tafiya da kudin ake ciyar da marayun ake Basu ilimi da wajen kwana,

har yanzu Basu bamu asibitin ba saboda ba'a gano ainihin Wanda ya shigo da qwayoyin Nan ba Dan sun bincika sun tabbatar ba Sa'eed bane, dukda an kulle shi a prison na tsawon lokaci idan ba sun gano ainihin Wanda yayi wannan aikin ba bazasu taba dawo Mana da asibitin Nan ba and muna buqatar ceto rayuwar marayun na we really need our orphanage back,

Kai kadai ne nake da yaqinin zaka it taimaka min ta wannan fannin Adam ka taimaka kayi wani abu a wanke sunan asibitin mu idan har ba'a bude shi ba duk Yanda mukayi HAR ABADA ba zasu taba bamu orphanage ba, nayi maka alqawarin daga Kan million 50 har zuwa million 200 zan ita bayarwa Akan case dinnan just help me please na roqe ka"

Furzar da numfashi Adam yayi ya jiqa maqoshin shi da ruwa sannan ya fara kwararo ma Sa'ood bayanai,

" Bani buqatar kudin ka Sa'ood idan na karba zan bawa abokantaka kunya, saidai kasan wannan case din ba qaramin bane Kuma ba Mai sauqi bane, it was a clean crime har gobe zanci gaba da fada maka wani na kusa daku sosai ne yayi wannan abun mutumin da yasan sirrin ku Kuma yasan komai Akan kadarorin ku dukda nasan ba yarda zakayi dani ba Amman in har kana son NASARA cikin wannan case din Dole ka amince da haka saboda Babu wani mistake da akayi Babu wani clue da muka samu ko kadan,

Babu record din shigo da magani Babu CCTV footage din lokacin da aka shigar dashi office din Sa'eed aka chanza Masa da Wanda ya ajiye zaiyi amfani da su so believe me na kusa daku ne yayi wannan aikin and idan har bamu Kama shi ba bazamu samu Mailafiya hospital ya dawo hannun mu ba,

Saidai idan zamu bi hanya ta biyu and it is very dangerous and hard, idan har muka saka gwamnati a ciki zata yaqi kanta da kanta ta gyara sunan ku ammafa zata iya amfani daku wurin biyan nata buqatun and duk lokacin da Abu yaje ya dawo Kuma Zaku fada ciki, idan gwamnati tayi rashin adalci you will also be blamed for it hatsarin San Kuma shine sunan ku zai baci a Karo na biyu Wanda a wannan lokacin bazamu ita gyara Muku ba duk Yanda mukayi kuwa, mutane zasu tsane ku za'ayi Muku kallon mugayen mutane Wanda idan ba'ayi sa'a ba bama zaman Kano kadai ba zaman Nigeria ma said ya gagare ku wallahi,

So kaje kayi shawaran idan zakayi qoqarin ka gano Mai laifin ne ko zakuyi taking risk din aiki da gwamnati? It's left to you idan kayi shawaran ka dawo ka sanar dani sai na fara aiki na".............🧚

#vote
#share
#comment

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now