Sadda Kai tayi qasa ita Bata San ma ta Fadi hakan ba wannan giant mutumin ne ya zaucar da ita har ta fita hayyacinta ta manta da matsayin ta, haquri ta fara bashi Amman tuni Sa'ood yayi gaba wurin Leesa,

"Ke! Baki ji na ne tun dazu Ina CE Miki ki zauna kin qi ko Baki gaji bane? Ina ta Miki magana kinyi min shiru wato kin maidani 'yar iska ko? Arniyar banza Kan ki ko dankwali Babu duk iskancin da kike ji dashi Naga Wanda ya taka naki a barikin 'yan iska kin tsaya kina qare min kallo ko mayya kike wallahi nafi qarfi nama na 'daci gare shi"

" Wai me kikeyi a Nan ne Haleesa? Me yake damun ki ne? Ko Ina shiru maganar ki kawai ake ji, meye ma'anar hakan?"

Qwafa tayi tace "hmm ya Sa'ood bar wannan 'yar iskan matan tana wani feeling, Mani zata gwada wa girman Kai?"

Tsaki yaja Yana tatattaba jikin statue din yace "kin gani fa ba mutum bane, gunki ne"

"Iye? Yaya zaka ce min ba mutum bane Bayan ga idon ta irin nawa ka kalli kanta fa harda gashi Kuma ta Tara farce kaman Mai cin Kare, sannan ta riqe qugu ta qura min Ido tana kallo na saboda rainin hankali"

" Wayyo Allah na Shiga uku na, irin gumakan da ake saka musu Kaya a kasuwa ne idan za'a siyar, me yasa kike Abu kaman wanda tazo daga qauye?"

Kai hannun ta tayi a hankali ta taba statue din sai kuma ta juyo tana dariya "eh wallahi ba mutum bane, ai da na ganta chocolate color kuma tana da Kai harda fuska ne nayi tunanin mutum ne, Amman ka daina taba ta mace ce fah Kuma ba Muharraman ka bace"

" Gunkin?" " Eh Mana ai gunkin na mace akayi sai ka duba na maza ka taba Amman Banda wannan"

Gyada yayi yace "to shikkenan muje ki zabi kayan kwalliya Kinga Rana tayi bamu da ishashen lokacin qarasa abubuwa Dole sai mun hanzarta"

"Yaushe ka taba gani na da kwalliya? Ni ko iyata banyi ba saidai idan zamu siya ma Salee itace Mai kwalliya"

Kiran wancar matan yayi ta zaba ma Salee duk abinda ake buqata sannan akayi packing suka cigaba da siye_siyen kayayyakin ta Basu Gama ba har Bayan azahar Dan har undies Saida Sa'ood ya Taya ta zaba mutane suna kallon su wasu na dariya ko a jikin shi,

Bata wuri sukayi ta zauna Kan wani kujera kafin yaje yayi sallah ya dawo suka kawo Mata drink sannan ta dauki magazine tana duddubawa qafar ta 'daya Kan daya sai zuba musu iyayi takeyi Wai taga alaman wancan staff din tana son Raina ma ajinta,

Wani jan top na Calvin Klein ta gani a jikin wata Mata ya dauki hankalin ta sosai rigan babba ne Mai dogo Kuma budadden hannu tsayin shi zuwa guiwa, Sa'ood na dawowa ta gwada mishi tana son irin rigan, Bai damu da tsadan shi ba yasa aka dauko Mata ta Shiga dressing room ta saka,

Baki bude Sa'ood ya tsaya Yana kallon ta Bayan ta saka rigan ta dauko fankacecen hijab dinta ta daura a Kai, ga skirt din atamfa ta qasa sai tayi wani fuss saboda yawan kayan dake jikin ta, gashi ta hada gaba da yamma fuskart Babu annuri hawaye ya taru a cikin idon ta

"Ya Sa'ood ba irin Wanda nace inaso suka bani ba, ka kalli fa banyi kyau irin na matar dake magazine din Nan ba"

Danne dariyar shi yake to kada ya fito ta hanyar toshe bakin shi da tafin hannun shi, Suma ma'aikatan wurin ta Basu dariya Amman suna tsoron su Bari ya fito wannan mala'ikan yaci musu mutunci,

Juyawa tayi ta koma dakin ta cire rigan ta maida nata sannan ta fito ta miqa wa matar da ta kawo Mata
"Gashi nikam bani son wannan bayi da kyau"

" I'm sorry madam Amman Yanda kika saka shi ba haka akeyi ba, idan kina so zan iya taimaka Miki yayi irin na matar jikin magazine din Nan harda kwalliyan ma"

" Yauwa aunty na dan Allah muje ki saka min amman gaskiya banison qafa na su fito waje"

"Don't worry ma'am duk abinda kike so shi za'ayi muje ko?"

Da sauri Leesa ta bita har wani beauty parlor dake waje Sa'ood Kuma ya Shiga zaben nashi kayan, kwalliya ta zauna aka tsantsara Mata dukda ba wani Mai yawa bane Amman sun Sha complain kafin a Gama saboda Bata Saba ba,

Ana gamawa suka dauko rigan aka saka Mata da white pencil Jean sai Kuma 4 inches hill jaa, sukayi Mata rolling qaramin farin gyale leesa ta fito looking so Masha Allah, taku daya biyu tayi da takalmin ta fara neman faduwa tayi azaman cire shi ta riqe a hannu Kuma taqi yarda a canza mata wani Dan a rayuwar ta tana matuqar son takalmi Mai tsini dukda a lokacin baya Bata da arziqin da zata siya irin su Amman idan ta gani a qafar wasu Yana Bata sha'awa sosai,

Ta Bayan Sa'ood Leesa ta tsaya sannan ta Kira shi tana murmushi, saurin matsawa baya yayi da yaga Leesa he was shocked baiyi tunanin Leesa zata iya chanzawa haka ba she looks gorgeous, jujjuyawa take cike da murna still takalmin ta Yana riqe a hannu tana mishi bayanin Yanda sukayi Mata,

Gogan naku was lost in another world, he was listening to his heart beat da lokaci daya ya fara fita da sunan Haleesa, ya kasa tabuka komai Bayan kallon ta tana narka mishi kitsen Imani kaman ya bude bakin shi yace ta daina jijjiga Amman ba zai iya ba bakin shi yayi mishi nauyi,

Shin daga shi ne ko daga ita ne? Wani ruhi ne daya yake qoqarin Jan na 'dan uwanshi? Sarwa ne yake so ne ko Kuma Haleesa ne ba zai iya banbancewa ba, yanzu ya fara amsa zancen zuciyar shi ya yarda Yana buqatar agajin gaggawa daga gareta idan har ya bayyana ma Leesa saqon zuciyar shi bata amince ba akwai qura,

"Wayyo Allah Yaya Sa'ood I'm starving wallahi yunwa nake ji sosai Kuma na fada maka kayi shiru" ta fada da qarfi tana taba shi da takalmin hannun ta,

Firgigit yayi ya dago fararen idanun shi ya zuba Mata, "me Kika ce?"

"Yunwa nace Ina ji dan Allah muje naci abinci"

" Ok muje" ya fada Yana tafiya ta bishi a baya har ya bude Mata marfin mota zata Shiga ya lura da qafarta Babu takalmi,

"Haleesa menene amfanin riqe takalmin a hannu Kuma kina yawo haka?"

" Mtsw bazan iya tafiya dashi bane"

Karba yayi yace ta Bari yaje ya canzo Mata Amman fir taqi haka ya dauko Mata wani plat ta saka ta cigaba da riqe dayan har suka Isa restaurant, kafin su Shiga Saida yayi reserving wurin ya zamo Babu kowa Dan bazaiyi sakarcin barin wani ya kalli kwalliyan ta har ya Yana ba ciwon zuciya zai iya Kama shi,

Yana kallo Saida kowa ya Gama fita sannan yayi Mata jagora sukayi ciki, yayi ordering kalolin abinci masu yawa sannan suka zauna zaman jira,

Shafa cikin ta takeyi tana yamutsa fuska sai faman Jan qananun tsaki takeyi,
"Yaya ne Haleesa ciwo cikin yake miki?"

" Aa kadan ne yake yi Amman zuwa anjima zai Bari"

" Wani magani kike Sha inje na kawo Miki?" Dan murmushi tayi dukda ciwon da takeji Yana qaruwa tace
"Me ya same ka ne ya Sa'ood why are you being so nice? Tunda muka fito baka ce min mahaukaciya ko Mara tarbiyya ba what happened to you?"

Murmushi Mai sauti yayi ya tsaya Yana qare Mata kallo, shi ya Kamata ace ya fara yi Mata wannan tambayar dan ko yaushe halayen ta ke angiza shi ya fada Mata abinda Bai Kamata ba Amman yau ta zauna silent kamar Salee"

" Ai nayi Miki alqawarin bazan zage ki ba Haleesa, Kuma yau kin fito ta musamman kamar ba haleesan da na sani ba, komi naki ya zamo na daban Dan Allah fada min menene sirrin" ya fada Yana daga Mata gira daya,

" Hmm Ina tunanin don Ina Jin yunwa ne Amman Bari naci abinci idan na samu wannan ciwon ya tafi zan dawo daidai Nima bani Jin Dadi a hakan, "da Kika nutsun?"

"Of course bani taba qaryan canza hali, bazan iya daukan dabi'un da ba nawa ba, I'm extrovert ko yaushe Ina fitar da abinda ke cikin zuciya ta ban Saba da boye_boye ba"

" Tunda haka ne Ina son ki fadamin abinda ke cikin zuciyar ki game da ni"

Karkata Kai tayi tana kallon shi ta gefe, " ban...ban Gane ba"

"Ina nufin Ina so ki fadamin ko kina so na.............🧚

*Manage😁*

#vote
#share
#comment.

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now