She is so unfortunate that kowa Yana samu masoyin shi na dawowa garesu Amman ita nata nisa zaiyi daga gareta, Yaya yaransu zasu dauki abun idan laifukan mahaifin su ya fito, Hala ma su zamo abun qyamata da Kuma tsangwama a Baki daya Mailafiya family ba za'a taba mantawa da wannan abun ba Hala ma HAR ABADA Sa'eed bazai yafe ma 'dan uwanshi ba"

Firgigit tayi ta juya Jin hannun mutum ya Taba ta, Zarah ta gani tsaye a bayanta tace "Mai ya same ki ne beelat? Gashi ana ta magana da ke Amman kinyi shiru"

Miqewa tayi daga mazaunin ta tana kallon mutanen wurin kowa hankin shi na kanta " umm...d...Daman.. excuse me I need to ease my self" ta dauki hanyar fita waje Haleesa ta riqo hannun ta,

"Ga toilet a dakin Nan aunty Ina Kuma zakije?"

" Ss...sor.. sorry na m..manta ne"

Kallon Yanda take zufa dukda AC dake wadace a dakin asibitin yasa mamanmu ta qaraso inda take tsaye da wheelchair dinta ta riqo hannun ta tana kallon cikin idanun ta
"Nabeela lafiya kuwa? Mai ya same ki? Ko Baki da lafiya ne?"

" Umm..lafiya ta qalau mama kawai dai Ina...in..Ina"

" Baki son zaman asibitin ne?"

Girgiza kai tayi "to me yake damunki? You look restless"

Kafin ta bude Baki tayi wani magana su Sa'ood suka bude qofar suka shigo da faffadan murmushi a Kan fuskar ko wannen su, Nan hankalin kowa ya dawo kansu mamaki ya Kama mutanen wurin ganin su tare wuri daya,

" Na fada?" Sa'eed ya tambaya Yana kallon Sa'ood,

"Baka Isa ba Kuma, Mun Gama magana a hanya zaka Bata Mana shiri?"

" To menene a ciki? Kawai fada musu fa zanyi yau da yamma zamu koma cikin mansion dinmu shikkenan fa"

Hakade shi gafe Sa'ood yayi cikin bacin rai yace " Amman Kai Kam anyi wawan banza, ba za'a taba sirri da Kai ba wallahi an Gama shirya suprise kazo ka bata, Allah ya taro ka wallahi Fatima ba qaramin qoqari kikeyi wajen kula da wannan sokon mijin naki ba"

Dariya duka parlorn suka saka Dan said yanzu suka tabbatar su din ne tun kafin aje ko Ina sun fara raba hali, Kan kace me kowa ya watse daga dakin sun tafi gida qarasa shirye shirye Dan basuyi tunanin komawan da wuri haka bane"

Bayan Zarah da Haleesa harma da Sa'ood sun taka mamanmu dakin ta ya rage daga Sa'eed sai Salee sai sheqe ayar su sukeyi, sai Kuma Nabeela da ta ambulance duniyar tunani,

Ta Kira numbern Idris yafi sau 30 Bai daga ba Nan wata dabara ta Fado Mata tasan wayar mutum daya ne ba zai taba qin dauka ba ko dan ya boye abin da take faruwa,

Qarasawa jikin gadon Salee tayi Wanda Sa'eed yake zaune dare_dare kaman shine patient din kanta a qasa tace
"Ya Sa'eed Dan Allah ka Dan bani aron wayar ka zanyi Kira dashi ne"

Bai tambaye ta ba'asi ba ya Ciro daga aljihun wandon shi ya miqa mata Dan bayi da wannan lokacin tayi saurin shigewa toilet tayi dialling numbern da taga an rubuta hermano Idris (bro idris) ringing uku ya daga,

"Hello brother"

Kuka Nabila ta saka Bata iya cewa komai ba, Jin sautin kukan ta yasa a hankali ya furta "Reina, me ya same ki?"

"Me yasa baka daukan Kira na? I was worried Ina ka Shiga ne baka dawo ba?"

" Komai ya kusa zuwa qarshe Reina, ya Kamata ki koyi rashin damuwa dani zanyi nesa take sosai, bansan hukuncin shekaru nawa zasu yanke min ba inaso ki Saba da rashi na ki daina gani na sosai tun daga yanzu, na cutar da rayuwar ki sosai na dauki hakkin marainiya Amman kiyi haquri dan Allah ki yafe min"

" Noo please ka daina wa'innan Maganganun ka dawo gida kawai please Ina jiran ka Dan Allah ka dawo"

" Ok Reina gani Nan zuwa"

Kashe wayar tayi ta wanke fiskar ta sannan ta daidaita nutsuwar ta ta fita ta bawa Sa'eed wayan shi sannan tayi musu sallama Kan zata tafi gida ta qarasa shirye_shirye, ta wuce dakin mamanmu Dan already sunyi magana da Sa'ood shi ze maidata gida,

Har sun fita Sa'ood ya dawo yace hallesa tazo ta raka shi, kallon kallo suka fara bin juna dashi ta kalleshi ta juya ta kalli mama, Wanda ita ma su din take kallo,

"Nazo na raka ka fa kace?"

"Yes bani son dawowa ni kadai ne"

Gyada Kai tayi tana binshi da wani irin kallo na rashin yarda tasan ba haka kawai Sa'ood zaice tazo su fita wani wuri ba,

"ina ba zaka sauqe ni a hanya kayi tafiyar ka ba?"

Dan Sosa qeya yayi Yana kallon mamanmu da ta zuba musu ido, Haleesa tana so ta barar Masa a gaban ta, wannan wace irin yarinya ce Bata mantuwa?
Murmushin Yaqe yayi yace "bazan sauqe ki ba har dakin Nan zan dawo dake safe and sound"

" Ok Ina ba zaka ci Zali na ba ba zaka zage ni ba?"

" Ni Kuma yaushe na taba cin zalinki Haleesa?"

" To na sani ko daga yau ka fara?"

" Ok bazan ci zalinki ba nayi alqawari"

" Yauwa, Kuma ba zaka tsokane ni ba"
" A'uzu billahi minal shaidanir rajim, haba dan Allah idan Zaki raka ni ki fada idan Kuma ba Zaki je ba fine sai nayi tafiya ta"

" I just want to make sure that I'm safe menene laifi a ciki?"

Murmushi mama tayi tana miqar da ita tace " jeki abinki 'yata, yayanki amintacce ne idan kina tare dashi hankali na a kwance yake Dan nasan ko yayi kuskure a baya ba zai sake bada qofa wani cutarwa ya same ki ba, so kuje Allah ya tsare hanya"

A gida suka ajiye Nabeela ko Shiga basuyi ba suka juya, saidai tun da suka fara tafiya a motar Babu Wanda yace ma wani qala sai Sa'ood dake ta Satan kallon Leesa dake faman magana ita Daya kamar zautacciya,

Dariya yayi cikin ranshi yace 'wato ita ba zata iya zaman shiru ba tare da tayi magana ba Kuma girman Kai ya hanata magana da ni, Babu matsala zan saki maganar dole ai"

Har zasu dauki hanyar da ze kaisu asibiti ya juya Kan motar suka dauki wani hanya daban, Leesa na ganin haka ta Bata fuska ta juyo tana kallon shi a masife tace

" Yanzu Kuma Ina zaka kaini? Bayan ga hanyar mu can ka barshi a baya"

Bai juyo ba shima ya Bata Rai kaman da gaske yace " Sayar dake zanje nayi"

" kutttt, tabdijam ai wallahi baka Isa ba..............🧚

Wattpadians Kun fara qoqarin voting 😅😍 thanks

*Ummu najma ce*

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now