Dariya Sa'ood ya fara har da sunkuyawa qasa Yana riqe ciki
"Wayyo Allah na Haleesa duniyar Allah! tun da nake ban taba ganin yarinya Mai gagara da qiriniya irin ta ba Kasan Bayan ta gudu Ina taje?"

Girgiza Kai Sa'eed yayi yace " sai ka fada"

"Kano tazo, she was with me all this while"

"What???" Sa'eed ya tambaya so confused Yana qwalalo Ido,

"Yess, tana tare dani a gida na dake Bayan gari for months, Kuma ni bansan ita bace ban ma gane ta ba Amman Saida tayi min dabara tasan asalina, ta Gane cewa ni Dan uwanta ne a lokacin sai Kuma ta saka ni na koya Mata harbi da bindiga"

" Kaii you are not serious, Daman a wurin ka ta koyi bindiga tazo zata kashe ni?"

" Ba Kai kadai ba ma Nima taso kashe ni Dan cewa tayi tana so ta koyi bindiga saboda ta Kare kanta daga mutanen dake son kawo Mata matsala that means ni da Kai Kenan"

Riqe Baki Sa'eed yayi yace "tabdijam brother Anya yarinyar Nan Bata da aljanu kuwa? Ni fa wasu al'amuran ta har tsoro suke bani"

" Bata da aljanun komai wallahi, shaqiyyanci ne kawai yake damun ta, Kuma hakan sakamakon zaman da tayi a gidan karuwan Nan ne Daman ya zamo dole ta dauki halin da zai zamo Mata kariya kaman Yanda mage take amfani da faracun ta idan an kawo Mata Hari itama da wannan dabi'un take Kare kanta, har ta taba yanka hannun uban gidan ta ma ta tsere da ya nemi ya keta Mata haddi,

" Amman yanzu bani tunanin tana buqatar hakan tunda muna tare da ita mu zamu zame Mata kariya da yardan ubangiji irin wannan halin zai iya cutar da ita a cikin gidan Nan"

" Canzawar halinta lokaci Daya Abu ne Mai wuya Sa'eed, Dole sai ta samu Wanda zai tsaya a kanta Yana monitoring al'amuran ta Kuma mahaifiyar ta ba zata iya ba gaskiya tunda ba cikakkiyar lafiya gareta ba"

" To Kai kayi Mata hakan Mana"

" Mai kake nufi nayi Mata hakan? Ance maka Ina da ikon gyara Haleesa ne? Rabani dan Allah, ni yayan ta ne Daman nasan ya zamo kaman Dole a kaina na Shiga hidiman ta Amman yanzu Kam wannan ifirituwan yarinyar tafi qarfi na"

" Haka Kenan zaka barta ta lalace? Idan kayi haka kayi wa mamanmu halacci? Ka tuna fa kayi Mata alqawarin zaka saka Mata da dumbin alkhairan da tayi maka Kuma zaka kula da twins, nasan zatayi farin ciki Mara misaltuwa idan Haleesa ta zamo taka zata samu kwanciyar hankali sosai tunda na riga na dauke Saleeha Ina kula da ita a qarqashin inuwar aure na, please kaima ka auri Haleesa kunfi dacewa ma da ita wallahi idan ka Mata do sai tayi maka goma Naga itama 'yar gari ce ba zata Bari ka cuce ta ba"

" But I don't love Haleesa brooo"

" Amman kana son matar aure ko? Very soon zan maida Saleeha ta zamo mama zata Haifa min yara da yawa in Allah ya yarda, Kuma ai itama ba wani sanin ta kayi ba ballanta ka so ta, yanda ka koya ma kanka San Saleeha haka zaka koya ma kanka son Haleesa idan ma kana buqata zaka iya biyana in koya maka soyayya dan na lura ba wani iya ta kayi ba"

Duka Sa'ood ya Kai Masa yayi saurin kaucewa Yana dariya, qwafa yayi Yana nuna shi da yatsa yace "zaka zo ka same ni wato ya'ba min magana kakeyi Bayan ka hada ni da raqai, dani da Kai wanene babba da har zakace wani zaka koya min soyayya babu abin da zan baka kaje ka nemi aiki ko kuma ka koma inda ka fito dan bamu shiri da masu zaman banza"

" Naji tsohon tuzuru angon jaririya mu koma hospital a sanar dasu momy abinda yake faruwa kada suji shiru zuwa yamma nasan za'a iya Gama ayyukan gidan Nan sai mu dawo" ya fada Yana Jan hannun Sa'ood suka ja suka bar asibitin ba tare da sun nemi Idris ba dan sun ma manta tare suka zo,

**********

Tun Bayan tafiyar su bada dadewa ba suka samu labarin nasaran da aka samu Kuma sunga zahiri lokacin da ake daukan bayanan su a TV saidai Kuma tun lokacin hankalin Nabeela idan yayi dubu ya tashi tasan zancen da zai tashi Nan gaba na karbo asibiti ne Kuma a wannan lokacin ne asirin mijinta zai tonu,

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now