" Hmm Sa'eed Kenan I'm not surprised don ka dade da zama babban maqaryaci tunda har kake cewa kana son abubuwa su koma kaman da Bayan baka shirya bani abinda na nema daga wurin ka ba after all she is mine, kana rabuwa da Saleeha ni da Kai zamu koma kamar bamu taba samun wata matsala ba Amman nasan ba zakayi hakan ba dole sai na karba da qarfi"

" Haba brother ta Yaya kakeso na rabu da uwar 'dana ko'yata? Saleeha is pregnant with my child kaje ka auri Haleesa Mana Dan Allah, komai nasu iri daya ne Bayan murya babu abinda ya banbanta su....."

" Sai Kuma ruhi da halayya, ni Saleeha nakeso ba fiskan ta ba, Kuma ma Banga dalilin da zaisa ka hada ni da Haleesa ba fitsararriyar yarinya Mara kunya, tun a baya kasan tsarina bani son fallalliyar mace shiyasa nayi ta zaman jiran Sarwa su girma dan nasan idan suka dauko mahaifiyar su zasu dace da irin matar da nake son aura Amman Haleesa Bata dauko hali Mai kyau ba"

" So yanzu ba zaka haqura ka fita harqan iyalina ba Kenan?"

"idan kayi tunanin zan canza shawara to ka yaudari kanka don ni idan na dauki so bani taba ajiyewa"

" Wannan Karon ya zamo maka dole ka ajiye dan wallahi sai inda qarfi na ya qare a Kan iyalina zan Kare Saleeha da rayuwata ba zan taba Bari wani cutarwa ya iso gareta ba"

" Daman na riga na Sani duk iya qoqarina in Kai zuciyata nesa sai ka qureni Sa'eed mu zuba mu gani ni da Kai waye zai ci nasara Koda kuwa zan rasa rayuwata sai na maida Saleeha ta zamo tawa"

"jahilin banza kawai wataran taurin kanka sai ya kaika jahannama tunda an riga an fada maka babu aure a tsakanin ku Amman ka dage sai ka aikata Haram"

Da mugun mamaki Sa'ood ya kalli Sa'eed Yana nuna kanshi hade da fadin "ni ka Kira jahili Sa'eed?"

"Kana tantama ne? Ai abinda kake Shirin aikatawa yafi qarfin jahilci saidai a Kira shi da hauka"

Daga qarshe cacan bakin gagaran su yayi a cikin mota sai da suka fito waje suna hargowq kaman zasu bugi juna, Jin hayaniyan su yasa mutanen gidan fitowa suka zuba ma sarautan Allah Ido Dan babu Mai iya rabon wanna gagarumin fadan a cikin su gashi Idris bayi Nan,

Salee ne tayi qarfin halin qarasawa wurin su tana janye Sa'eed da 'dan qarfin da ya rage Mata, badan kalan kayan su ya banbanta ba Kuma tasan kayan dake jikin Sa'eed kafin ya fito ba ba lallai ta iya gane shi ba Dan Yanda yake tada jijiyoyin wuya har yafi Sa'ood dinma, Bata taba sanin Hala take da zafin rai ba sai yau,

"Abban Al'amin dan Allah kubari abinda kukeyi Bai Kamata ba"

" I don't care nidai babu Wanda ya Isa yace zai raba ni dake duk duniyar nan wallahi ko wanene sai yaga bacin rai na"

Gyada Kai tayi tana Qara janye shi gefe tace "naji babu Wanda zai rabamu, mu tafi ciki Dan Allah fada Bai kamace ku ba"

Murmushin gefen Baki Sa'ood yayi Yana girgiza Kai "ka Gama duk abinda zakayi Sa'eed Amman ka sani ko me zai faru I must make Saleeha mine saina raba ka da ita I promise you that"

Wani kukan kura Sa'eed yayi ya cukumo wuyan rigan Sa'ood Yana zare Masa idanu jijiyoyin jikin shi sun tashi rada_rada har wani karkarwa yake saboda bacin rai,

Billahil Azeem baka Isa ba ina son matata Kuma baka Isa ka rabani da ita ba Sa'ood, zan iya bari maka komai a duniya Amman Banda Saleeha Ina sonta Ina qaunar ta sannan ya zamo min dole na zauna tare da ita Kuma babu abinda zaka iya a Kai,

Ganin fada na son barkewa a tsakanin su yasa hankalin Salee a tashe ta Shiga tsakanin su tana qwace riqon da sukayi ma juna da qarfi Sa'eed ya ture ta gefe sai da tayi baya ta bugu da bango sannan ta zube a qasa tana sakin wani razanannen qara,

"How dare you touch him? Shi ba mijinki bane nine kadai mijinki kada ki kuskura ki sake qoqarin taba jikin shi"

Salee kanma ba Jin abinda take fada takeyi ba saboda wani azaba da taji bayanta da ta buga Yana Mata ga ciwo da cikin ta da qwanqwason ta ya kama lokaci daya, dafe bayan tayi tana kuka sai a lokacin qwaqwalwar Sa'eed ya hasko mishi barnan da ya aikata da sauri shi da Sa'ood sukayi kanta suna qoqarin daga ta ya buge shi Yana gwada shi da yatsa,

KAMA DA WANE....(Completed)Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin