" Ok da so kikeyi inzo kunnen ki na musamman ince Miki ki tashi mu tafi? Ai ke ba makauniya bace dake buqatar 'dan jagora" ya raba ta gefen ta ya wuce,

Qwafa tayi ta bishi a baya suka Shiga cikin motar shi ya tada suka bar haraban asibitin,
Sun danyi tafiya Mai nisa taga zaman shirun Nan bazai fishshe ta ba, Juyowa tayi tace
"Wai me kuka dauki 'yar uwata ce?"

Saida ya dan yi shiru sannan yace "Wata 'yar uwan taki?

" Inada wata 'yar uwa ce Bayan Saleeha Kun maida ta kaman wani qwallo sai passing_passing kukeyi da ita da Kai da wancan Sa'eed din ko ance Muku ita dabba ce da Bata da 'yanci Wanda kowa zai mallaketa a duk lokacin da yaso?"

Murtuqe fuska yayi ya ci gaba da driving ba tare da ya tanka ta ba cikin ranshi Yana takaicin rashin da'a da ita fitar da magana da Haleesa ta daukar ma kanta kwanannan, Jin yayi shiru yasa ta sake cewa

"Magana nakeyi da Kai fa baka bani amsa ta ba"

Sauqa yayi daga Kan hanya yayi parking sannan ya juyo yace Mata "fita min a mota"

"Saboda me?"

"Saboda haka nace, Zaki fita ne ko sai na fitar dake?"

A zuciye ta bude marfin motan ta fita hade da banging dinshi ta juya zatayi hanyar da ta gani ta hannun damar ta, Saida ya qarasa daff da ita ya sauqe glass Yana kallon Yanda take cika tana batsewa yace "mahaukaciya Mara tarbiyya kawai idan har kinason in zauna lafiya tare dake sai kin koyo manners"

Leesa Bata San lokacin da hawaye ya fara zarya a kumatun ta ba, maganar da Sa'ood ya jefeta dashi ya cakke ta har cikin zuciyarta meyasa zai kirata Mara tarbiyya? Duk iya qoqarin da fadi tashin da tayi Basu gani Kenan? Ai idan ta zamo Mara tarbiyya ma ba laifin ta bane laifin su ne gaba daya dan hakkin Basu tarbiyya a kansu yake,

Tafiya takeyi tana share hawaye ta tsani wa'innan 'yan biyun da suka zo suka wargaza Mata tsarin rayuwar ta sun raba ta da Salee sun Sanya ta cikin kadaici na HAR ABADA tasan indai Sa'eed na raye Salee ba zata taba goya mata baya ba yanzu haka zata ci gaba da gwagwarmaya ita kadai Dan ba zata taba komawa wancan gidan ba never!

**********

Kafin Sa'ood ya Isa gida sai da ya Kira Idris ya fada mishi saqon mamanmu Akan yazo ya same shi a gida daga nan sai su tafi tare, ya dade zaune a cikin mota Yana tunanin Yanda za'ayi ya samu Sa'eed bayison yayi tsammanin ya yafe mishi yaudaran shi da yayi,

Ana Haka sai ga hydar yazo wucewa da ball a hannun shi zuge glass yayi ya Kira shi,
"Daddy zo Nan"

Da gudun shi ya qaraso Yana washe haqwara " gani uncle"

"Uncle Sa'eed Yana gida?"

" Eh Yana Nan" " ok kace Ina neman shi Kuma yayi sauri"

Da "okay" ya amsa ya sake kwasan gudu yayi ciki ba'a dade ba Sa'eed ya fito ya zaga passenger seat ya zauna sannan ya juyo Yana fuskantar Sa'ood da murmushi dauke a fuskar shi,
"Brother gani kace Wai kana nemana ko?"

Da kaman ba zaiyi magana ba sai Kuma yace "bani nake nemanka ba mama ce tace aje a fito da takardun kadarorin mu,ta bani sarqan Sarwa shine makullin vault din sannan ta fada min password dinshi Kuma umarnin ta ne mu tafi tare yanzu sai ka jira brother ya qaraso mu wuce"

Gaba daya jikin Sa'eed yayi sanyi ganin Yanda yake magana ma ko kallon shi bayi yi, da hydar ya fada mishi Sa'ood na neman shi yayi tunanin shiryawa zasuyi Amman kaman har yanzu Bai yafe mishi ba,

Murya a sanyaye yace "brother har yanzu fushi kakeyi da ni? Dan Allah kayi haquri ka yafemin inason komai ya dawo Kaman da musamman yanzu da zamu koma cikin mansion dinmu bani son yaranmu su fiskanci halin da muke ciki "

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now