Sai lokacin ma ya tuna cewa tun da ya shigo gidan Bai ga Haleesa ba, to Ina ta Shiga? Jakar shi ya dauka ya Shiga bedroom dinshi ya rage kayan jikin shi sannan ya Shiga wanka yasan kafin ya gama ta fito daga inda ta Shiga,

Har ya shirya cikin qananun Kaya ya fito babu Haleesa babu alaman ta, ya qarasa qofar toilet dinta Yana knocking shiru babu amsa, duk inda yake tunanin tana zuwa a cikin gidan sai da ya duba Amman baiga Haleesa ba,

Gurin yaransa dake kula da ita lokacin Bata Nan yaje ya tambaye su ko sun ganta, Wanda ke kawo mata abinci yace
"Boss nayi tunanin ko barci ma take dan tun jiya da na kawo abinci Bata dauka ba, na yau ma da na kai haka na qaraci buga Bata bude ba"

Bai ce dasu komai ba ya wuce cikin gidan ya duba inda take ajiye jakar kayan ta Amman bayinan a wurin, haka ya dinga dube_duben duk wasu properties nata dake ajiya a dakin Amman ko daya bai gani ba duka ta tattare,

Ranshi a bace ya bude drawer zai dauki bindiga yaga a cikin su babu daya, Yana bude drawern saman shi yaga babu komai a ciki duk takardun su ta kwashe,

"Sa'eed!" Shine wandda ya fara zuwa ranshi, baisan yarinyar Nan wacece ba Amman Yana da tabbacin Sa'eed ne ya turo ta, Ashe yayi kuskure da ya yarda da Haleesa har ya fada Mata wasu daga cikin sirrikan shi, dole ita da Sa'eed su biya ha'intan shi da sukayi Dan bazai barsu haka ba sai ya dau fansa,

Ko kulle cikin gidan baiyi ba ya fita, tun daga nesa yake zagin yaran shi yana faman masifa kaman ya ari Baki,
"Stupid fools, bunch of idiots Ina kuka Shiga har yarinyar Nan ta fice daga gidan Nan Baku sani ba? Menene amfanin barin ku da nayi cikin gidan nan?"

Babu Wanda ya iya bashi tsayayyen amsa cikin su sai haquri suke faman bashi,
" To wallahi ku kuka da kanku idan har bansami yarinyar Nan ba kowa ya tattaro makaman sa yau ko ni ko Sa'eed dole daya ya haqura da duniya"

Suna fitowa da bindigogin su ya Shiga cikin mota Suma suka Shiga ko warming motan basuyi ba yaja sai jigawa,

**********

Leesa na zaune gefen shagon su bello ta zabga uban tagumi, ko ruwa ta kasa kaiwa bakinta gashi har Rana tayi ana shirin Kiran sallan azahar Amman ba'a dawo da Salee daga asibiti ba, tana so taga wani hali sistern ta take ciki amman bazata iya zuwa asibiti ba don Bata son haduwa da Sa'eed,

Da gudu bello ya qaraso wurinta yace "aunty Haleesa gasu sun dawo Amman Basu dawo da Saleeha ba"

Dago kanta da zatayi taga suna nufo wurin da suke gadan_gadan, kallo 'daya tayi mishi ta gane Sa'ood ne wannan ba Sa'eed ba da sauri ta tashi ta buya inda ba zasu ganta ba,

tana kallo suka shiga gidan Sa'eed ba'a dade ba suka fito suka koma cikin mota suka Kama hanyar asibitin da Al'amin ya fada musu an kwantar da auntyn su harda room number ya fada musu don da sukayi waya da momyn shi ta fada musu, da sauri Leesa ta tsari napep tabi Bayan su,

Sa'eed tsaye a pharmacyn asibitin Sa'ood ya wuce ciki, direct dakin da aka kwantar da Salee ya wuce, Haleesa Kuma tana ganin kaman Sa'eed zai ganta ta koma ta buya har ya gama abinda zaiyi ya wuce ciki tabi bayan shi,

Bankade qofar dakin yayi ya Shiga da bindiga a hannun shi ba qaramin tsorata Salee da Zarah sukayi ba ganin Yana saita bindigar Kan goshin ta,

"Kinyi tunanin Zaki tseremin right? Ko Ina kikaje Ina biye dake Haleesa Kuma zan tabbatar na kassara rayuwar ki Idan kikayi qoqarin was da hankali na"

Wani mugun yawu Salee ta hadiye 'muqut' Ashe Daman maganar da Leesa take fada Mata akan Sa'eed gaskiya ne Kenan ya boye Mata abubuwa da yawa, amman ba zata iya fada mishi ba ita bace Leesa gwanda ya cutar da ita akan ya cutar Mata da 'yar uwa,

Bude Baki tayi zatayi magana yayi saurin dakatar Mata tsawa "shut up! Har dake ma Zarah, ban taba tunanin za'a hada Baki da ke a yaudare ni ba"

Zarah Kam bakinta ya kasa buduwa mugun tsoron Sa'ood da take fama dashi tun da ya tashi jikinta sai kyarma yakeyi, ana haka Sa'eed ya bude qofar ya shigo da mamaki yake bin Sa'ood da kallo ga bindiga akan matar shi,

"Brother no! Please don't hurt her babu abinda tayi maka nine Mai laifi ba Mata na ba"

Juyowa Sa'ood yayi Yana kallon shi da wani qaramin murmushi akan fuskar shi,
"Wow Ashe Haleesa matarka ce very nice, shine ka turamin ita taje ta dubo maka abin da nake yi ko? Amman ta fada maka cewa na kashe Garba TK Kuma Kai da ita ne next target dina?"

" Sa'ood please calm down ba Haleesa bane Saleeha ce wannan su biyun Sarwa ne please don't hurt her she is *pregnant* "

Tsayawa numfashin Sa'ood yayi cakk na 'yan sakwanni, he can't believe what he heard, Sarwa? Tare dashi? Matar Sa'eed? That too pregnant?,

Ganin kamar Bai yarda dashi ba ya ranqafa jikin Salee zai Ciro mishi necklace dinta ya gani da sauri Haleesa ta bude qofar ta saita Masa bindiga tare da 'dana kunaman bindigan a zafafe tace
"Kada ka kuskura ka taba min 'yar uwata mayaudari kawai"

Kallon kallo suka fara bin juna dashi musamman Sa'ood da ya Gama Shiga rudani, tun da Sa'eed ya fada mishi Sarwa ne tabbas sarwan ce, Amman Yaya akayi ya auri burin shi? Me yasa zaiyi mishi haka? Tsawon wani lokaci suka dauka tare aka barshi Yana ta bulayi ga Haleesa kusa dashi Amman bai gane ba?

Fincike hijab din Haleesa yayi Dan ya tabbatar ma kanshi ita din ce da sauri ta dawo da bindigar saitin shi tana ja da baya,
"Kada ka taba ni idan ba Haka ba zan illata ka"

Bai saurare ta ba ya dago necklace dinta ya duba pendant din tabbas wannan sarqan Sarwa ne, wani kukan kura yayi ya cukumo wuyan rigan Sa'eed jikin shi har wani tsuma yake yi saboda bacin rai, idanun shi sunyii jaja wur jijiyoyin jikin shi gaba Daya sun tashi, da sauri Salee ta fincike drip din da aka saka Mata ta Shiga tsakanin su,

"Dan Allah kayi haquri kada ka cutar dashi, me yayi maka?"

" How dare you decieve me Sa'eed how dare you!!! Kasan Yanda mahaifiyar su take tsumayen ganin su kuwa ka boye su a wurin ka? Wallahi yau sai na kashe ka babu Mai Hana ni raba ka da duniya wallahi"

Zarah na ganin haka ta dauki waya ta Kira baba alhaji ta shaida Masa abin da yake faruwa, kafin ta ajiye wayan Salee ta sake yankan jiki ta fadi.............🧚

*Ayi manage zaku same posting da dare insha Allah*

#vote
#share
#comment

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now