Daga wurin ya wuce dakin shi Yana Shiga ya sakar ma kanshi ruwa Yana Jin kaman an sauqe mishi wani nauyi daga Kan qirjin shi, yau burin da ya dauka tsawon shekaru 17 sun cika ya Gama da chaptern Garba TK sauran Sa'eed Kuma,

Wannan karon ba zai je mishi da wasa ba dole ne kawai ya fada mishi a motan wa ya saka Sarwa Kuma Ina ya kaisu, zuwa jibi zai kammala komai insha Allah ya maida Haleesa gidan su ya Kai Sarwa ma mamanmu su koma rayuwar su kaman da,

Haka dai ya Gama imaginations dinshi da duk wasu tsare_tsare cikin toilet kafin ya daura towel ya fito ya shirya ya sake komawa dakin Garba, sai a lokacin yake sanar musu cewa ya rasu Kuma ko a fuska Bai nuna damuwa ba ko 'dan'dani a Daren ya shirya yabar Lagos Amman hanya da nisa Dole zai iya kaiwa washe gari kafin ya Isa Kano,

**********

Leesa na zaune yunwa ya addabi 'ya'yan hanjin ta sai faman duba agogo takeyi ta rasa Mai yasa har yanzu ba'a kawo Mata abinci ba, ganin zaman jira ba zai fishshe ta ba yasa ta tashi ta fita ko zata ga mutumin da yake kawo mata Amman kaman gidan ma babu kowa Bayan Mai gadi,

Zagaya Bayan gidan ta hau yi ko zata same shi Amman wayam sai qofar da suke fita waje koyan bindiga ita da Sa'ood ne kawai a bude, qarasawa tayi ta lelleqa Bata ga kowa ba da sauri ta koma ciki ta rarumo jakar ta da ta Dade da hadawa ta dauki Torchlight ta sidada a hankali ta fita daga gidan,

Gudu take fallawa cikin duhun daren banda kukan dabbobi babu abinda take ji cikin dajin gaba daya a tsorace take Amman ta quduri niyyan barin gidan, ita kanta Saida Tasha mamakin Yanda aka yi Bata manta  hanya ba a haka Saida tayi kusan 40 minutes kafin ta fara fitowa cikin gari,

Hamdala tayi ganin ta fara hango mutane, Amman damuwan shine daga Nan Ina zata je? Tasan Bata ma Isa ta fara zuwa gidan su Ameerah ba saboda matsalan da ta saka su a ciki haka ma gidan alhaji Habib shima ba gidan zuwa bane, tafiya kadan ta qara ta samu adaidaita sahu tace mishi Tasha ze kaita,

Suna Isa ta Ciro 1k cikin kudin Sa'ood da ta kwasa ta biya Mai napep, Tasha mamaki sosai ganin kamar da Rana Tashar cike yake da mutane ana ta Lodi a motoci, ganin masu Saida abinci a bakin tashar ne ya tuna Mata da yunwan da take ji, ta rungumi Jakarta sosai sannan ta qarasa wurin su ta siya awara Mai zafi taci ta koma neman wurin kwanciya,

Washe gari da sassafe Bayan tayi sallah tayi breakfast ta biya kudin mota ta Shiga ta zauna tana zumudin haduwa da 'yar uwar ta tasan Salee zatayi farin cikin ganin ta, har motan ta cika suka tashi tana lissafin irin wurinda zasu tafi su zauna da Kuma Yanda zata tona asirin Sa'eed Yanda Salee zata tsane shi HAR ABADA.

Tafiyar awa 2 da rabi ya shigar dasu birnin jigawa garin dutse, Daman already tasan gidan Sa'eed Dan tun lokacin da Salee take son shi baisan tana yi ba tasa aka bincika Mata,

Saida ta je wani shagon makanikai ta Kira wani yaro bello yayi mata bayanin duk mutanen da suke rayuwa cikin gidan har ya shaida Mata cewa Sa'eed bayi Nan sannan yaga fitar dayar matar shi ta Shiga maqwafta inda akayi aihuwa,

Godiya tayi Masa ta bashi na kashewa sannan tace ya saka Mata Ido har ta Shiga ta fito duk wani abun da ya faru ya sanar Mata,

Da sallama ta Shiga cikin gidan ta samu Salee zaune a Kan tabarma suna breakfast ga Islam da al'amin sanye da uniform din islamiya kasancewar ya asabar shiyasa suka Kai lokacin a gida,

Bata samu damar amsa sallamar ba ta miqe a dimauce ta jefar da cokalin hannun ta tana qare ma Leesa kallo lokaci Daya hawaye ya fara sintiri a Kan fuskar ta,

Su al'amin kuwa sai binsu da kallo sukeyi cike da mamaki, su kalli Salee su bi su kalli Leesa suna ayyana auntyn su yau ta zama guda biyu,

"Haleesa Ina Kika Shiga? Kinsan damuwan da na Shiga na rashin ganin ki kuwa? Mai yasa Kika tafi? Dan sabanin da muka samu baici ace ya raba tsakanin mu ba, hankali na ya tashi sosai na rashin ganin ki 'yar uwata"

Murmushi Leesa tayi ta qarasa wurinta ta riqo hannun ta Nana janta zasu fita daga cikin gidan, tana fadin
"Tafiya zamuyi Saleeha idan Mun Isa ma sauqin mu zanyi Miki bayanin komai"

Al'amin na ganin haka ya fita da gudu Kiran Zarah Salee kuwa tuburewa tayi ta qwace hannun ta daga riqon Leesa,
"Kin manta a qarqashin ikon wani nake? Bazan iya tafiya ko Ina ba Saida Izinin shi, ki zauna Dan Allah koma menene mu tattauna a Nan"

"Salee baki San da wani irin mutum kike zaune ba, ni nasan wanene Sa'eed Kuma bazan barki kici gaba da zama dashi ba baki San shi waye ba Kuma daga Ina yazo ba"

Hade Rai tayi tana kallon ta a kaikaice " ban gane bazaki barni naci gaba da zama dashi ba? Bake kike da iko da aurena ba, Kuma kema bansan daga Ina kike ba ban Kuma tambaya ba saboda na yarda dake to shima irin wannan yardan nayi mishi"

"Please don't be stubborn Salee kwata_kwata ma bakisan komai a kanshi ba, ko kinsan Sa'eed Yana da twin brother? Ko kinsan su waye iyayen Sa'eed Kuma daga wani family ya fito? Ko kinsan Sa'eed yasan asalin mu all this while ya boye Mana?"

Dai_dai Nan Zarah da al'amin suka shigo tabi Leesa da kallon tsoro da mamaki, kafin ta dago wayarta tayi dialling numbern Sa'eed ringing biyu ya daga,

"Hello mi Alma, gamu Mun kusa qarasowa...."

Bata tsaya sauraron shi ba tace " miel Dan Allah kuyi sauri ga Haleesa ta dawo yanzu Haka tana cikin gidanmu"

" You see, Kinga matar shi ma tasanni ba tare da ta taba ganin na ba, har inda mahaifiyar mu take 'dan uwan shi ya kaini na ganta da idanuwa na, Bari na nuna Miki gaskiyar mijinki"

Ta zazzage jakar ta a qasa, ta dauko duk abubuwan da kwaso daga wurin Sa'ood tana nuna Mata harda bindiga da kudi, Salee dai sakare tayi da Baki tana kallon ta al'ajabi kadai ya Hana ta magana Mai yasa sa'eed ya boye Mata Abu mai girma haka? Tasan ko menene Yana da dalili zata jirashi ya dawo ya fada Mata dalilin shi na yin hakan"

Muryar Leesa ne ya katse Mata tunani Ashe har ta Gama tattare kayan ta maidasu ciki jaka ta rataya, ta sake riqo hannun Salee a Karo na biyu,

"Mu tafi please kafin ya dawo ya Ida nufin shi a kanmu"

Murya na rawa tace
" I'm...p.. pregnant Haleesa"..............🧚

#vote
#share
#comment

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now