Can anjima kaman anyi ruwa an dauke taji ciwon da cikin yake ya tafi sai dan sauran da ba'a rasawa hakan yasa ta tashi ta koma kujera sannan ta gyara zaman hijab dinta ta kwanta,

Miqewa Sa'ood yayi yana duban ta yace "are you okay?"

Gyada mishi Kai kawai tayi ya sake cewa "ko akwai abun da Kike buqata?" Shima girgiza Kai tayi ya Mata Allah ya sawwaqe ya koma dakin shi,

Leesa kuwa tunda ta tashi ta kasa komawa barci tunanin 'yar uwarta ya addabi zuciyar ta cikin wani Hali take ciki yanzu oho, Bata samu Daman rintsawa ba sai wauraren asuba ganin haka yasa Sa'ood ya barta ta Sha barcin ta, training dinshi ma a wani wuri yaje yayi dan kada ya Hana ta barci,

**********
Har Sa'eed yayi sallah ya dawo Salee tana barci ganin lokacin sallah na Shirin tafiya yasa ya tashe ta, ya taimaka Mata tayi sallah sannan ta sake komawa barci, shima ya kwanta Dan Daren jiya gaba daya bata samu barci ba shiyasa shima Bai rintsa ba,

Har Zarah ta kammala breakfast shiru babu Sa'eed babu Salee, ta nufi dakin da nufin dibasu sai Kuma tayi saurin dakatawa kada taje taga abinda zai dame ta, haka ta koma ta shirya Islam suka tafi makaranta ta qarasa sauran ayyukan ta sannan ta koma dakin ta ta zauna har zuwa wani lokaci Basu fito ba,

Qaran diban ruwa a rijiya ne ya tada Sa'eed ya leqa yaga Zarah be ta fito da wani qaton randa tana jidan ruwa ko me zatayi dashi? Oho, duba agogon hannun shi yayi yaga 10:37am, a zabure ya miqe ta Yaya akayi barci Mai nauyi ya dake shi haka,

Leqa fuskar Salee yaga har lokacin tana barci sannan yayi saurin Shiga toilet dinta ya wanke fuskar shi da bakin shi ya fita tsakar gida, sanin babu kowa a gidan yasa ya qarasa bayan Zarah a hankali ya daga ta cakk Yana Nishi,

"Mi Alma kinyi qatotuwa da yawa dole in siya Miki slimming tea idan ba Haka ba Nan gaba ni da ke saidai kallo da ido"

Murmushi tayi tana dada narkewa a jikin shi lokaci daya taji duk fushin da takeyi yabi iska, murya can qasa tace "good morning miel"

"Morning Bonita (pretty) how's your night? I'm sorry yau nayi latti ayi min afuwa"

"Babu komai miel Bari na Kai maka ruwan wanka kafin ka fito sai na Kai ma Saleeha abinci"

" Toh godiya nake Bari naje na jira ki" ya juya ya Shiga dakin ta, tana Kai mishi ruwan ta koma ta dauko mishi kayan da zai saka sannan ta dauki abincin Salee ta Shiga dakin ta still tana barci,

Ajiye abincin tayi ta fita Saida Sa'eed ya Gama shiryawa sannan yazo ya tada ta ya Bata abincin da qyar ya samu ya zauna a cikin ta Bata amayar ba,

**********
Su Nabeela sun Gama shiryawa zasu tafi asibiti suna zaune a parlo Idris kawai ake jira ya fito da waya a kunnen shi suna magana da Sa'ood,

"Gaskiya na dade ban ziyarce shi ba brother saboda wasu sabgogi da suka Sha min Kai Amman kwanan Nan zanje na dubo shi Dan gaskiya rabo na dashi tun kafin yayi aure"

" What??? Aure kace fah? Har Sa'eed ya samu kwanciyar hankalin da zaiyi aure Bai samo Mana Sarwa ba?"

" Wallahi kuwa brother Nima abun ya bani mamaki lokacin da ya zo min da zancen yanzu haka ma ance matar tashi tana da ciki kaga ai kwanciyar hankali ya samu matsuguni wurin su Kenan da alama yama manta damu ya manta da zancen Sarwa"

" Very very nice, Ina fatan a shirye yake Dan kwanan Nan zanzo na tuna mishi, wannan zuwan kuma da kaina zanyi shi ba turowa zanyi ba dole Sa'eed ya zaba ko ya fito min da Sarwa ko Kuma na dauki rayuwar shi a bakacin nasu, yanzu ka qaraso asibitin Ina jiran ka Nima gani Nan fitowa"

Da " toh" ya amsa sukayi sallama sannan ya juya wurin Nabila yace "mu tafi ko?"

Tagumi tayi tana kallon shi cike da takaici "yanzu dan girman Allah duk roqon ka da nayi Saida ka fada mishi Sa'eed yayi aure? For the past few months Mun samu kwanciyar hankali sosai Amman yanzu kazo duk ka wargaza komai Mai yasa baka son a zauna lafiya ne Amor?"

KAMA DA WANE....(Completed)Место, где живут истории. Откройте их для себя