" Baki mun komai ba, duk abinda ya faru ba laifin ki bace qaddarar muce tazo a haka, na gode Muku sosai Bari naje Naga meye na samu" tana fadan haka ta juya ta shige dakin ta,

Gift din Sa'eed ta fara budewa cikin dauki taci Karo da wata hadaddiyar evening gown orange color da veil dinshi Mai Dan girma a bakin shi anyi ado da black stones masu sheqi kaman Yanda yake a wuyar gown din da qasan shi,

Qare ma rigan kallo tayi she wonders nawa Sa'eed ya kashe don ya siya Mata Bayan ba kudin yake dashi ba, tana jujjuya rigan ta hango wani paper a qasa Wanda garin warware gown din ya Fadi,

Da sauri ta bude takardan ta fara karantawa,
'''Happy birthday Alma, I hope you like your gift, inaso ki shirya ki saka shi by 8 zan zo na dauke ki muje wani wuri'''

Dunqule takardan tayi ta manna shi da qirjin ta tana dariyan farin ciki she is super excited 8 yayi taga wurin da zasu je, da sauri_sauri ta bude na Islam taga fashion necklace da earrings black na al'amin Kuma plat shoe ne hadadde shima black,

Baje kayan tayi a Kan gado ta dauki bucket ta dibo ruwa ta Shiga wanka, tana fitowa ta zauna ta tsara simple makeup sannan ta shimfida darduma tayi sallan magriba ta zauna tana 'yan addu'oin ta har akayi sallan Isha,

Tana idarwa a gaggauce ta shirya dan taga lokaci ya kusan qurewa, tana cikin rolling veil din Sa'eed ya daga labulen dakin ya shigo cikin orange suit da black shirt ta ciki kanshi yasha gyara ya fito as tsohon doctor Sa'eed khalifa Mailafiya looking handsome as always,

Sake gyalen ta tayi ta taka wurin da yake tsaye a hankali tana Jin qamshin turaren sa da ya cika Mata hanci,
"You look great miel, na manta rabon ka da saka suit gashi suna maka kyau, inaga tun kafin ka Shiga prison kayi loosing din matsayin ka kadaina Shiga irin wannan, please bring back your spirit ka dawo kamar da but don't forget loving me on the way"

Murmushi Mai qayatarwa yayi ya kama gyalen kanta Yana gyara Mata zaman shi, Saida ya Gama tukuikuya Mata shi sannan yayi dariya yace "muje your highness" qarasawa jikin mirror tayi tana duba qullin da Sa'eed yayi Mata da sunan rolling ta turo Baki gaba tana gyarawa tana mita,

Basu Bata lokaci ba suka fita ta samu Keke napep Yana jiran su a qofar gida suka Shiga yaja sukayi gaba, sunyi tafiya Mai nisa kafin suka iso gaban wani hadadden restaurant ya biya Mai napep suka Shiga sai bin wurin takeyi da kallo,

Jan hannun ta yayi har zuwa wani table da aka tsara shi na mutum biyu yaja Mata kujera ta zauna, sannan ya miqa Mata menu Dan ya lura da irin kallon da take binshi dashi gaba daya a rude take,

Sauqe murya tayi ta Dan matso kusa dashi "miel me kakeyi haka ne? Kayi asaran kudi da yawa fa zamu iya facing financial proble...."

Bata rufe Baki ba waiter ya qaraso da medium size cake da Champagne ya ajiye Kan table dinsu, Baki ta sake shaa tabi cake din da kallo an rubuta Fatima Zarah @38 ta sake bin Sa'eed da kallo Yanda yake faman zabga murmushi,

"Happy birthday once again mi amor wishing you many returns of the day, may Allah bless you"

Bata iya amsawa ba ta fara jujjuya cake din,

"Did you like it"

"Miel me ya same ka ne? You spend so much money baka tunanin abinda zai je ya dawo, ga kudin da ka kashe wurin sayan wa'innan kayayyakin Salee fa ciki take dashi Kamata yayi da kudin da ka kashe min su a banza da tanadi ka fara yi Mata har Allah ya sauqe ta lafiya"

" This is the least I can do to make your day special, I know wannan birthdayn da na shekaru 2 baya da suka wuce ba Kai na baya ba but at least I want to see a smile on your face ba wannan rudewar ba domin a Kan ki zan iya yin fiye da haka so let's cut the cake"

Zarah Bata San lokacin da hawaye suka fara sintiri a fuskar ta ba ta sunkuya tare da rufe fuskar ta da tafin hannuwan ta tana rerashi a hankali, riqo hannun ta da ta rufe fuskar ta dashi yayi Yana share Mata Hawaye,

"Ki bar kukan Nan mi alma kada ki Bata min kwalliyan ki yau ranar murna ne ba na kuka ba"

Cikin sheshsheqar kuka tace "I'm sorry miel.....nayi nadaman duk abubuwan da nayi maka please forgive me" tana kaiwa Nan kuka yaci qarfin ta ta qwace hannun ta daga riqon shi ta cigaba da yi,

Miqewa yayi ya qarasa bayanta Yana rarrashin ta tare da fada Mata kalamai masu dadi masu sanyaya zuciya har ya samu ta sarara sannan ya koma ya zauna,

"Duk shekarun da muka dauka tare ban taba samun attention dinka Kuma nunamin kulawa sosai ba sai Bayan afkuwar qaddarar Nan, a da breakfast kawai kakeyi a gida Amman lunch da dinner duk bansan a wuraren da kakeyi ba Kuma ban damu da nasani ba Amman tun da muka dawo bamuda arziqi ko yaushe muna tare, safiya, Rana , yamma, dare ko wani lokaci idan ba kana wurin aiki bane to kana tare dani,

Lokacin da muke cikin mailafiya family idan bani da lafiya saidai driver ya kaini asibiti wani lokacin ma ba tare da sanin ka ba har na warke Amman yanzu idan bani Jin dadi da kanka a matsayin ka na likita zaka dubani wani lokacin har magani da kanka kake siyo min magani sannan kana kasancewa tare dani har na warke,

On birthdays, weddings, anniversaries, da sauran shagulgula, saidai Naga gifts be it cars, money, or expensive jewelries Amman baka zuwa, bani ganinka Kuma ba a asibiti kake ba bansan ma wace duniyar ka tafi ba,

Wannan halin da muka Shiga ya kawo Mana sauyi da yawa babban ciki shine tsoron Allah da Kuma soyayyar gaskiya, Mun koyi zama tare a matsayin mu na iyali guda daya ko da yaushe muna tallafawa juna, nayi sakarci a baya miel Amman bazan yarda na sake aikatawa ba don da gaske Nima Ina sonka shiyasa ban rabu da Kai ba, I hope zaka yafemin mu ci gaba da gina rayuwar mu Akan turba Mai kyau,

Thank you so much for making me realize my mistakes, na amince zan kula da Salee da abin cikin ta har kaje Mexico ka dawo, Allah ya kiyaye hanya"

Janyota jikin shi yayi ya manna Mata peck a goshi, sannan ya fara feeding dinta ba tare da wani ya sake ambata komai ba a cikin su,

**********
11:17pm 

Sa'ood ya shigo cikin gidan ya samu Leesa a tsaye sai Kai komo takeyi hankalin ta a tashe,

"Yaya ne wani Abu ya faru ne?"

Girgiza Kai tayi tace "Aa babu komai nayi tunanin wani abu ne ya same ka a wurin aikin naku, kaga babu Wanda ze maida ni gida shiyasa na damu"

" Oh! Asibiti naje wurin mamanmu na duba ta Kuma alhamdulillah akwai ci gaba sosai yanzu haha ma tana iya Kai hannun ta ko Ina ba tare da taimakon kowa ba"

Dan murmushi Leesa tayi tace "da gaske?"

"Na taba Miki qarya ne?"

"Aa kawai dai inaso nasan randa zaka koma ne, Nima inason naje na ganta"

Yatsina fuska yayi Yana kallon ta na tsawon 30 seconds sannan ya tabe Baki hade da fadin "ok gobe zan he Amman sai nayi tunani a Kan tafiya dake Dan nasan Zaki iya neman guduwa"

**********

Suna Isa qofar gida suka hango al'amin tsaye Yana ta kalle_kalle, duba agogon hannun shi Sa'eed yayi yaga dare yayi tsakiya ya qarasa gurin shi Yana tambayar shi Mai ya fito dashi,

"Aunty ne Bata da lafiya tun dazu sai amai takeyi tana murqusuwa a qasa............🧚

_na biya bashi_💃💃💃

#vote
#share
#comment.

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now