Kallo daya tayi Mata ta watsar ta qarasa tattara sharan taje ta zubar, Salee bata daddara ba ta sake maimaita "good morning momyn al'amin HAP...."

Maganar ta ya katse saboda dogon tsakin da Zarah ta ja tayi shigewar ta daki tabar Salee tsaye tayi sakare da Baki, wannan ne Karo na 4 da ta gaida yau da safiyan Nan taqi amsawa ko dai wani Abu tayi Mata Bata sani ba?

Komawa daki tayi ta zauna Dan har yanzu bata gama warware wa ba Zarah da kanta tayi lunch itama ta Shiga babu Wanda ya sake fitowa cikin su har Saida su Islam suka dawo daga makaranta sannan Zarah ta fito da fara'a ta tarbe su,

Babu laifi sun 'dan sake da ita saboda kwana biyu tana 'dan qoqarin kula dasu shiyasa abin ya dan fara bin jikin su, Basu yarda ta sauya musu Kaya ba suka wuce dakin Salee suka same ta kishingide a Kan kujera sai gyangyadi takeyi bacci Kuma yaqi zuwa,

Dariya Islam tayi tace "aunty momy ki kwanta Mana idan barcin kike son yi sai qifta Ido kikeyi,"

Tsaki al'amin yaja " to keep Ina ruwanki shegen magana kawai bakin ki kaman na aku"

"Dakata! Ni Kar ku fara min fada a Nan Tom and Jerry, yau ba ranar cacan baki bane we have to keep momy happy because it's her birthday"

Cikin murna suka hada Baki wurin fadan " da gaske?"

"Yess shiyasa na jira ki dawo sai muyi shawaran abinda ya Kamata, me kuke ganin tafi so wanda zamu siya Mata?"

Dukan su dariya suka sa suka maida Salee kaman wawiya sai binsu takeyi da kallo, al'amin cikin darya yace
"Wallahi aunty Koda Zaki Saida abin da Kika mallaka Tass ba Zaki taba siya ma momy abinda take so ba, ko kyautar me aka Mata bayi wadatar ta tana hangen sama, saidai kawai idan zamu jarraba wani Abu maybe she will like it"

Dan 'bata fuska Salee tayi tace "wannan kalaman da kukayi amfani dashi wurin bada shaida Akan mahaifiyar ku bai dace ba, kada na sake ji Kai ko ma wani ma ba wa ni ba kada ku sake fadan irin haka kunji ko?"

" Yes aunty momy Amman Bari na fada Miki abun da zamu Mata taji dadi"

Miqa kunnen ta tayi " ok Islam Dina fada min a kunne Kar Yaya yaji"

Zarah kuwa tana zaune a daki ta zabga uban tagumi tana tunani, shekarun baya da suka wuce ranar birthdayn ta yakan zamo Rana ta musamman a family saboda Yanda ake bidiri tun 12 na dare har zuwa 12 na wata daren,

Haka zasuyi booking tangamemen hall ta gayyaci qawaye da abokan ta yaran manya 'ya'yan masu fada aji a cika wuri da kida ana Taya matar doctor Sa'eed murna, idan sun Gama Kuma a dawo gida ayi na family haka kowa zai so nuna tashi bajintar ta hanyar presenting gift masu tsada, Amman yau an manta da ranar ballantana a shirya mata wani Abu na musamman don taji dadi harta 'ya'yan cikin ta ma sun manta Sa'eed ne kawai yayi Mata addu'a sosai kafin ya fita,

6:02pm

Zarah ta fito da niyyan daura dinner sai just tayi an watso Mata wasu Abu har Yana Shirin Shiga Mata Ido, da sauri taja baya tana karkade jikin ta sai Jin muryar Islam da al'amin tayi suna "happy birthday momy"

Dagowa tayi tana kallon su duka harda Sa'eed da Salee, Islam ne ta fara miqo Mata Dan qaramin gift da gift card akai, al'amin ma ya Bata nashi Wanda yafi na Islam girma kadan shima da card din a Kai, sai Salee ita kuma roban qananun chocolate ta Bata Sa'eed ma ya miqa Mata nashi,

Tsananin farin cikin ta ya gaza boyuwa yaune Rana ta farko da Sa'eed ya fara Bata gift da hannun shi ko wani lokaci sai dai ya turo a kawo Mata Amman bayi taba zuwa,

"Thank you, thank you so much I thought Kun manta, I really like the suprise nasan wannan shawaran ki ne Saleeha thank you so much"

Riqo hannun ta Salee tayi tana murmushi tace
"Naji dadi da kikayi farin ciki and I'm sorry idan na Bata Miki rai bada sani na ba Dan Allah ki daina fushi Dani gwanda ki kirani ki fadamin laifi na sai na Baki haquri Kuma na gyara"

KAMA DA WANE....(Completed)حيث تعيش القصص. اكتشف الآن