Ko sakin ta nayi babu aure a tsakanin ta da Sa'ood, bazan sake jefa kaina cikin bala'i ba Bayan Wanda nake ciki, yanzu zabi Daya gareni shine zuwa wurin baba alhaji dan shi kadai ze iya sasanta tsakani na da Sa'ood sai na fada mishi Salee itace Sarwa da yaqinin wata Rana Leesa zata dawo in yaso shi Sa'ood din ya aureta,"

Cikin kuka tace "noo please miel don't do this to me you can't love Salee kawai buqatar ka ka biya da ita right? Na yarda ka auri ko wacece a duniyar Nan amman Banda Sarwa please, ka barni zanyi wa momy na magana ta fada ma baba alhaji a fita cigiyar Haleesa da an same ta ka hada ta da Saleeha ka badasu duka ma Sa'ood idan ta aihu ka karbi 'danka Amman ka daina zancen kana sonta dan Allah"

" Kimin haquri Alma a wannan lokacin bani da iko a Kan zuciya ta na riga nayi nisa a son Sarwa bazan iya cire ta daga zuciya ta farat daya ba"

Qarasawa wurin da yake zaune tayi ta tsunguna akan guiwowin ta tana tsiyayar hawaye,
" Dan Allah ka tausaya min, wallahi nayi nadaman dukan abubuwan da na aikata a baya Yanda na dinga wulaqanta ka da tozarta ka saboda gudun talauci, yanzu a shirye nake na zauna da Kai da yarana cikin ko wani Hali zan zauna tare da ku, Salee ta riga ta nesanta ki daga gareni bazan juri sake yin nesa daku ba, please come back to me"

Sa hannu Sa'eed yayi ya tallabo fuskar ta sannan ya Kai Mata light peck a goshi Yana shafa gashin kanta yace "kalle ni Zarah"

Dago idonta da qwalla ke kwance a ciki tayi tana kallon kyakkyawar fuskar shi Wanda tafi qauna fiye da komai a duniya,

" I'm sorry to say Amman ba Salee bace ta nesanta mu daga gareki, ke Kika nesan ta kanki daga garemu da sakaci da rashin kulawa kin dauki son duniya kin watsar damu a lokacin Kuna Saleeha tana iya bakin qoqarin ta wajen kula damu, dukda da farko bamu Jin komai a kanta Amman ya zamo mana kaman dole ne mu sota Dan ko wani zuciya tana qaunar me kyautata Mata,

Amman hakan bayi nufin munbar sonki da Kuma qaunar HAR ABADA matsayin ki a zuciyar mu bazai taba goguwa ba, but please ki taimake ni ki bani hadin Kai wurin hada Kan Sarwa ki kula min da Salee har naje na dawo, please ko badan ni ba kiyi Dan mamanmu a matsayin ta na malamar ki Wanda ta kula da tarbiyyan mu gaba daya"

**********
8:13am

Leesa ne kwance a Kan 3 sitter tana shaqar barci hankali kwance saijin qarar wani abu tayi bammm, a zabure ta kifo ta diba da 'dan iskan gudu tayi cikin dakin Sa'ood amman bayi ciki, har toilet Saida ta Shiga da gudun ta shiru bayi ciki,

Nan ta sadaqar ta fara salati yau tasu ta qare, shi wannan 'dan ta'addan ya fita gashi an shigo gida za'a kashe su, shirun da taji na Yan mintuna yasa ta fara sauqe ajiyar zuciya Hala ba wani abu bane Bari dai taje ta saka a duba Mata,

Gyara zaman hijab dinta tayi ta fara takawa a nitse zata fita sai Jin wani qaran da ya taka na Bayan tayi ba..ba...ba..bam, da Leesa ta diba a 360 degrees Bata tsaya ko Ina ba sai waje, can take Bayan gidan ta hango wani qofa a bude,

Kaman zatayi kuka ta nufi wurin a hankali tana leqawa daga alamu daga wurin qaran yake zuwa,

Sa'ood ta hango ya toshe ga headphone da glasses hannun shi riqe da bindiga Yana harba shi jikin target, jinjina Kai Leesa tayi tace yau Kuma abun nashi Nan ya dawo,

Kaman ance Masa ya juyo ya hango ta tsaye ta qame kaman wata sabuwar soja, cire glasses din idanun shi yayi ya Mata alama tazo da hannun sa, a darare ta qarasa wurin shi tana qarewa dajin kallo ita Bata taba tunanin gidan ba a cikin gari yake ba, lallai idan tazo guduwa akwai aiki,

Cikin bindigogin dake ajiye yace ta dauki daya, ta saka hannu ta dauki sniper Dan taga yafi dogo,

Qaramin bindiga ya dauka ya miqa Mata ya karbi na hannun ta Yana fadin "zalamammiya kada ko a mafarki kiso Allah ya Baki ikon amfani da wannan"

Ya saka Mata spare headphone din da ya ajiye saboda rage Jin qarar bindigan sannan ya nuna Mata Yanda zata riqe bindigar tayi operating dinshi, leesa Tana jin ta sake harsashi tayi saurin jefar da bindigan ta sake zura a guje tana ihu,

Dariya Sa'ood yakeyi harda riqe ciki wannan da ace mutum ta harba faduwa zatayi Kenan ta mutu saboda tsoro? Lallai aiki ya same shi,

**********

Salee na zaune tayi crossing legs dinta Sa'eed na Bata abinci a baki tana ci suna raha, Saida ya jata da tadi ta cinye Tass dan yanzu da qyar take saka wani Abu a cikin ya zauna,

Ganin ta fara yunqurin amai yasa Sa'eed ya jawota jikin shi Yana shafa Bayan ta har ta dawo daidai sannan ya daga ta suka qarasa jikin mirror hannun shi Akan cikin ta,

"Babe kin rame da yawa baby na ne yake baki wahala ko?"

Girgiza kanta kawai tayi tana murmushi yace " kiyi Mata afuwa please kwanan Nan zata maidake 'yar lutiya, nide inaso ki ci gaba da jajircewa kaman Yanda kikeyi a ko wani lokaci, kiyi haquri da duk abubuwan da Zaki gani Nan gaba, inaso kisan ina matuqar SONKI sannan, duk abubuwan da suka faru ba'a son Raina bane"

Juyawa Salee tayi tana kallon shi cikin Ido a maimakon ta mirror, tajii dadi sosai da yace Yana sonta Dan idan Bata manta ba yau ne Karo na biyu da ya furta Mata kalmar so, Amman maganar da yayi daga baya ya daure Mata Kai,

"Wasu abubuwa ne suke faruwa ba da son ranka ba?"

Murmushi kawai yayi
" forget it, inaso jibi na tafi Kano sari Kuma na fara sayo ma babyn mu Kaya Amman zankai 2to3 days kafin na dawo"

" Kaii Abban al'amin babyn da bamu ma San menene ba shine har za'a fara Tara Mata Kaya"

" Ah to inaso itama ta samu gata Koda Wanda be Kai na yayun ta ba, yauwa na manta ban fada Miki ba yaune birthday Zarah I want you to help me in making the day special for her"

Dariya Mai sauti Salee tayi tace
" Woww ai ban sani ba da tuntuni munyi wishing dinta, Amman Bari ka gani gaba dayanku zamu Baku mamaki daman kaman Naga yau ranta a bace yake sai mun saka ta murmushi insha Allah"

**********

Saida Sa'ood ya kammala gaba daya training dinshi sannan ya shigo ya same ta tana breakfast,

baiyi wata_wata ba ya saita bindiga sama ya sake alburushi, da mugun gudu Leesa ta tashi garin wucewa ta kifar da abinci da ruwan a Kan carpet din parlorn ta shige toilet dinta da qarfi ta rufo qofa...............🧚

_manage please, a bini bashi gobe zan biya insha Allah_ 😅

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now