**********

Shiga bedroom dinshi tayi ta hango shi kwance a Kan gado Rabin jikinshi a rufe he looks so takeaway, tafi 2 minutes tsaye tana qare was kyakkyawar fuskar shi kallo sannan ta taka a hankali zuwa jikin gadon ta bude bedside drawer,

Kaman Yanda tayi tsammani bindiga ta gani a ciki har guda biyu, cire tsoro tayi hannun ta na rawa ta dauki daya ta saita shi a kanshi da mamakin ta ta hango shi zaune yayi crossing hannun shi a qirjin shi Yana kallon ta, Bata San tun shigowar ta motsin ta ya tada shi ba,

Tabe baki yayi Yana kallon Yanda take bari zufa sai karyo Mata yake Wai dan ta riqe bindiga ya sake wani murmushi sannan yace
"Shoot!"

Gaba daya ta rasa Yanda zata dana kunaman bindigan Bata ma San Yaya akeyi ba, kwata_kwata Yanda ta riqe bindigan ma ba daidai bane ta saka hannun ta biyu ta rungume shi, Amman taso ace zata iya operating bindigan da ta harbe Sa'ood ta gudu sannan taje ta harbe Sa'eed ta dauki 'yar uwarta su gudu,

"I said shoot!!!" Ya sake fada a tsawace, kasa tabuka komai tayi ta tsaya jikinta na kyarma, ya miqa Mata hannun shi na dama fuska a tamke yace "bani bindigar"

Bata iya miqa mishi ba ta ajiye jikin qafan shi ta koma gefe ta qame,
"Me ya shigo dake daki na?"

Kame_kame ta fara "Uhmm....t..t..toilet zan shiga"

"A Kan wani Abu ya Sami naki?"

" Aa, Daman drainage dina ne ya toshe shine nazo daukan pumper"

"Saboda kin taba ganin na ajiye pumper a toilet Dina?"

Zatayi magana yayi saurin katse ta " don't you dare to ever enter my room without my permission again! I so much respect my privacy dan kinsan ni waye ba hakan Yana nufin nuna sharing wani relationship bane da zai Baki daman ganin tsaraici na, get out inason na saka riga"

Fita tayi ta koma parlo ta zauna Bai dauki 1 hour ba ya fito cikin shigan shi na fita, ta bashi address din Ameerah sannan ya fice,

Bayan fitar shi da away biyu aka Danna doorbell, tana budewa taga Daya daga cikin yaran shi ya miqa mata pumper a laida sannan ya sanar da ita oga yace a fada Mata ya mayar da Ameerah gida,

Murna sosai Haleesa tayi dan tasan ta saka Ameerah da iyayen ta cikin wani hali, dole duk ranar da ta samu ta kubuta daga hannun Sa'ood taje ta nemi gafarar su kafin su gudu,

**********

Salee na zaune da Islam Kan tabarma a jikin dakin ta suna shan iskan yammaci Al'amin ya shigo hannun shi dauke da farin laida Wanda take cike da agwaluma,

Kafin ya qarasa wurin su Zarah tayi saurin Kiran shi ya Shiga dakin ta, ya tsaya daga bakin qofa yace
" Gani momy"

"Menene a hannun ka"

Dago laidan yayi Yana gwada Mata yace "dady ne ya bada kudi a siya ma aunty agwaluma Wai tana sha'awar shi"

"Bani laidan nan" ta saka hannu ta karba ta raba gida biyu sannan ta bashi rabi tace ya fita ya bata wuri, ta bare agwaluman tana Sha tana matse fuska tsamin shi Yana  ratsa jijiyoyin jikin  ta dan ita a rayuwar ta Bata taba Sha ba,

Sumbatu ta fara ita kadai " bansan yaushe miel ya fara rashin adalci a gidan shi ba, Yana fifita Salee a kaina bansan wani laifi nayi mishi ba ko daman so na da ya fada Yana yi na qarya ne? Wani qualities Salee ta fini? ko Dan ita ta yarda zata zauna dashi cikin talauci shi yasa yafi Jin dadin zama tare da ita? Idan haka ne to Nima na amince zan zauna tare da shi a kowani hali Koda ace zamu wuni bamu ci ba zan jure Amman bazan jure rashin shi a kusa dani ba Ina sonka sosai miel" ta qarasa tana share qwalla zatayi qoqari yau tayi magana dashi,

Koda aka Kai ma Salee kadan batayi complaint ba saima dadi da taji Zarah taci Abu da sunan ta, Dan har ta Shiga damuwa na share ta da takeyi tayi tunanin ko fushi takeyi da ita,

**********
8:05

A gajiye Sa'ood ya shigo gida ya zuba a kujera Yana sauqe numfashi, Garba TK na Basu wahala sosai duk da sunan training Dan akwai special operation da zasu tafi su dibo ganima,

Cire facing cap dinshi yayi da bindigan aljihun shi da wayoyin shi ya zuba su a Kan table sannan ya miqe ya kwanta Kan 3 sitter,

Leesa da taji shigowar shi taje ta juye mishi abincin da yaron shi dazu ya kawo a plate ta saka mishi exotic Mai sanyi da cup ta saka a tray ta fito,

Tana hangoshi kwance taje can gefe ta ajiye tray din sannan ta dawo inda yake ta tsaya tana kallon bindigan dake Kan table tana kallon shi, zuciyar ta cike da fargaba ta Kai hannun ta ta dauki bindigan kafin ta qare Masa kallo taji muryan shi Yana fadin

"Ki ajiye bindigar nan ki bani wuri"

A firgice ta juya tana kallon shi ba tare da ta ajiye bindigar ba still idanun shi a rufe kamar me barci, juyawa yayi ya Bata baya Yana fadin
"Me zakiyi da bindiga ne Bayan tsoron ta kike ji?"

Dakewa tayi tace "shirya neman kariya daga mutanen da ke Shirin zama Mana matsa da Kuma daukar fansar wulaqanci"

Tabe Baki yayi yace " ok! If that's the case ni da kaina zan koya Miki Yanda ake amfani da ita"

" Seriously?? Yaushe zaka fara koya min?"

" Gobe, oya go away ki barni nayi barci"

**********

Sa'eed na Gama Shirin kwanciya yaje dakin Salee ya duba jikin ta  yayi Mata sallama sannan ya wuce dakin Zarah Dan ita Bata zuwa saidai shi ya bita,

A kishingide ya same ta tana kallo a wayar ta, yayi plugging nashi wayan a caji sannan yazo gefen ta zai kwanta da sauri ta dakatar dashi,

"Yau kayi niyyan zuwa Nan ne? Ai da ka zauna wurin amaryar ka zinariya na riga na sallamar Mata da Kai"

Bai tsaya musu da ita ba ya tashi zai fita dan yau gaba daya ranshi a bace yake ko dogon magana bayi son yi, tayi saurin Shan gaban shi tana watsa mishi harara,

"Yaushe ka zamo Mara adalci ne miel? Yanzu da nace ka fita shine zaka fita saboda ka gwada min fifikon da Salee take dashi a kaina? Me yasa? Kun juya min baya gaba Daya yanzu Baku damu dani ba, Ina sonda kake fadan kana min? Me yasa kafi son Salee a kaina why Sa'eed? Why???"

" Saboda ita *Sarwa* ce..........🧚

#vote
#share
#comment

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now