"Insha Allah" yace ya wuce ciki ya barta da tunani,
Tasan duk inda Salee Take Bata cikin qoshin lafiya tana Jin kwatankwacin ciwon da take ji a jikinta yanzu Dan tare suke rashin lafiya kusan ko wani lokaci saidai na wani yafi na wani tsanani,

"to ko Sa'eed din ne ya cutar da ita har ya saka Mata rashin lafiya? Ko Kuna rashin lafiyar daga ni ne? Allah ya tsaremin ke Saleeha bazan Bari Sa'eed ko familyn shi su cutar dake ba insha Allah zan cika Miki burin ganin mahaifiyar ki Amman Bayan haka zamu fita daga rayuwar su gaba daya, Allah ya riga ya tsara Mana rayuwarmu mu biyu ba zan Bari wasu su shigo ciki su tarwatsa musu sauran farin cikin da ya rage musu ba,

**********

Gyara kwanciya Salee tayi tana Qara shafo fuskar Sa'eed cikin kulawa take qarewa ciwukan da Sa'ood yaji masa kallo, murya na rawa tace
"Dadyn al'amin dan Allah kada ka sake Shiga abun hawan da baka da tabbacin nutsuwar Mai tuqa ta, kaga suni maka rauni a banza bazan iya jurewa ba idan wani Abu ya sake samun ka"

murmushi dauke a fuskar shi ya riqo hannun da ta riqe shi dashi yayi Mata peck a jiki sannan ya dunqule cikin tafin hannun shi,
"Kada ki damu babe babu abinda bazan iya ba a kanki, a fafutukar neman Leesa wannan abun ya same ni Amman hakan ba shi zaisa na daina neman ta ba, duk inda take sai na samo ta insha Allah"

" No, ka dakata da neman ta haka har sai ka sami lafiya yanzu nafi buqatar ka Akan Leesa dani da abin ciki na muna buqatar kulawar ka sosai, dukda nakan ji a jiki na cewa Leesa tana cikin matsala Amman dole na haqura da neman ta naci gaba da Mata addu'a, bazan iya salwantar da Kai saboda son zuciyar ta ba"

Gyara mata kwanciya yayi yace "sleep babe, you need some rest"

Babu musu ta rufe idanun ta shi Kuma yayi Mata addu'a ya today Mata zuciyar sa cike da fargaba,

Yana son Salee Yana son abinda yake cikin ta bazai iya rabata dashi ba, saboda da son da take mishi ne yasa ta dauki soyayyar duniya ta daura ma cikin nan yasan ba zata yarda ba idan yace zai cire shi Kuma shima zuciyar shi ba zata so cirewan ba, kwata_kwata ma bayi son sake aikata laifin kisan Kai dan yayi Imani cewa shine musabbabin duk matsalolin da yake ciki,

Amman Yaya za'ayi ya maida ta ma Sa'ood da cikin shi a jikin ta? Wani irin hukunci zai dauka a kanshi? Yaya ma mamanmu zataji idan tasan ya auri Salee a mafi qaracin shekaru ba tare da sanin kowa ba gashi harda Rabin tsakanin su? "Ya salam" ya furta Yana dafe goshin shi,
" Ya Allah na tuba ka fitar Dani daga qangin da nake ciki"

Washe gari
6:07am

Tana zaune a kan darduman da tayi sallan asuba ta jingina kanta da jikin gado tana Jin zuciyar ta Yana tashi, so takeyi ta fita Amman motsawa ya gagare ta ana haka Islam da al'amin suka shigo,

Cikin tausayawa suka tsuguna a gabanta suna gaida ta dayi Mata Yaya jiki, yunqurin da tayi zatayi magana taji amai yazo Mata da sauri al'amin ya kwabe rigan jikin sa ya saka Mata tayi a Kai sannan ya fita da rigan bakin rariya Yana daurayewa,

Zarah dake jikin murhu tana girka breakfast ta juyo tana tambayar shi abinda yake yi a wurin, gyara zaman glasses din idanun shi yayi yace
"Aunty ne tayi amai a jikin shirt dina shine nakeso na wanke na sauya wani"

Shiruu Zarah tayi cikin ranta tana mamaki al'amin da yake da tsananin qyanqyami ko wuri ne idan da jiqa bayi takawa da qafan shi Amman yau saboda Salee ya Bari anyi Masa amai a jikin rigan sawan shi har Yana wankewa da hannun shi,

Sauye_sauyen da take gani wurin mutanen gidan yanzu ya fara taba ta emotionally kowa ya dauki son duniya ya daura ma Salee da cikin ta da ko good 1 month beyi ba ciki harda 'ya'yan ta duk qoqarinta ta kawar da Kai ta kasa tana Jin kishin Salee sosai a qasan zuciyar ta, ita yanzu Bata buqatar kudi kwata_kwata she just want her family back!!!

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now