Salee tayi qarama sosai ma daukan ciki Yaya akayi yake bari irin wannan abubuwan suke faruwa da su? Qaddara ce ko Kuma sakaci? Kodai laifin da suke aikatawa a baya tare da babanmu ne yake bibiyar rayuwar shi?

"No no no bashi bane" ya bawa kanshi amsa Yana qoqarin kawar da tunanin cikin ranshi ai neman kudi kawai sukeyi alhaki Akan masu laifin yake ba Akan su masu wanke laifin ba,

To yanzu a Ina ma zai fara neman Leesa? Yaya za'ayi ya sameta ya dawo da ita wurin Salee ya samu ta dawo dai_dai ta cire damuwa daga ranta Dan farin cikin gidan shi ya dawo ya yarda duk wani annashuwa na mutanen gidan a kafadan ta yake harda nashi shi kanshi,

To wurin was zaije a cikin 'yan uwanshi masu Hali su taimaka mishi? Idris ne ko Sa'ood? Idan Idris ne ce masa zeyi ya samu qannen shi daya tana wurin shi Daya Kuma ta gudu ya tayashi neman ta a wurin da Bai sani ba ko me? Sa'ood is more dangerous than Idris Amman ko babu komai shi Dan uwanshi ne ciki Daya suka fito Kuma Sarwa cousin sister shi ce ba jininshi na kusa kaman Yanda suke tare ba, zai saurare shi ya tayashi Nemo Sarwa idan yayi Masa bayani yasan bazai qi ba,

Bai qara Bata lokaci ba ya rufe shagon shi yaje gida a sace ya dauko takardan su Salee ya fito, ya wuce tasha sannan ya Shiga motan KANO yasan ko ta Yaya ne Sa'ood zai saurare shi,

**********
4:20pm

Bude qofar dakin yayi ya shigo fuskar shi dauke da murmushi ya rufe qofar tare da jinginuwa a jiki Yana qare Mata kallo, kamar ko yaushe tana kwance kamar gawa idanunta suna kallon sama, da wires na supporting machine a jikinta Wanda suka zamo Mata abokan rayuwa,

Takawa yayi a hankali zuwa jikin gadon ta ya jawo kujera ya zaune hade da Kai Mata peck a goshi yace "good afternoon cariña yau nazo Miki da labari Mai Dadi, kin gani"

Ya fada Yana nuna Mata yatsarshi manuniya Wanda ke sanye da wani zobe Mai zanen fuskar kare Wanda akayi shi da baqin qarfe,

"Nima yanzu na Shiga cikin yaran Garba TK masu kusanci dashi, yanzu zan iya zuwa wurin shi kowani lokaci Naga dama, a yau dinnan an rantsar damu da zamu zamo masu yi Masa hidima Wanda zamu salwantar da rayuwar mu saboda tashi rayuwar ni Kuma a yau dinnan nayi rantsuwan sai nayi ajalin shi da hannuna zan hallaka shi in Allah ya yarda,

Hannun shi dake cikin nata yaji ta riqe da dan qarfi hawaye na tsiyaya a idanunta, cikin tsananin mamaki da al'ajabi Sa'ood yabi hannun da kallo, ya daga Yana kallo amman still hannun ta na riqe da nashi Bata sake ba, a take hawayen tsananin farin ciki ya fara zarya a idanun shi Ashe da gaske ne akwai improvement a condition dinta,

Daga murya yayi Yana qwala ma doctor Kira ba qaqqautawa, a rikice itama ta shigo ta dauka wani abun ne ya samu patient dinta, dariya dauke a fuskar shi take gwada Mata hannun mamanmu dake riqe da nashi,

"Can you see it doctor? Kinga ta riqe hannun na fa tana iya motsi kin gani?"

Dan murmushi doctor tayi tace " ai tun jiya ta fara iya motsa hannun ta saidai sunyi Mata nauyin sosai ba zata iya dagasu da garaje ba Amman muna iya bakin qoqarin mu wurin Mata duk abinda ya Kamata ana Mata gashi da excercises din da zai taimaka Mata ta miqe very soon insha Allah"

"To doctor Yaya maganar tafiya da magana Kuma?"

" Kada ka damu Mr Sa'ood komai a hankali muke bi step by step idan Mun samu nasara a na farko sai mu qara gaba yanzu muna da hope almost 50% na cewa zata tashi ta warke garau insha Allah sai ku dage da Mata addu'a, excuse me please" ta juya ta fita,

After many years yau Sa'ood ya tsinci kanshi Yana murmushi da dariya, wayar shi ya dauka ya Kira Idris ya shaida mishi abunda ke faruwa, ko 40 minutes ba'ayi ba suka shigo da Nabeela da yaran su gabaki daya, har wuraren qarfe 6 suna asibitin ana ta murna ana farin ciki,

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now