Har aka lokacin sallah ya wuce Sa'ood Bai dawo ba Kuma Leesa batayi barci ba tana zaune idanun ta zuru_zuru tana kallon wall clock ta tashi tayi sallah ta dawo taci gaba da zama, wani tunani ne ya Fado Mata a Rai tunda Sa'ood bayi Nan Kuma bataji motsin kowa ba a gidan kawai guduwa zatayi,

Ta tashi ta leqa ko Ina babu alaman mutum ta saka takalmin ta ta iba a guje, taje jikin gate tana girgiza shi ta iya qarfinta Amman a rufe, zazzaga gidan tahau yi kamar mahaukaciya ko zata samu abinda zata balla lock din dashi kafin ya dawo, daga can jikin want daki ta hangi kwaranga ta saka tahau Kai ta tana Shirin dirqa waje taji qaran harbi bamm,

Ai babu shiri ta fado akan qafarta Saida yayi wani qara ta saki ihun azaba, juyowar da zatayi taga Sa'ood tsaye a kanta riqe da bindiga ya rungume hannun shi daya Yana faman tsiyayar jini,

Qoqarin tashi ta fara yi ta kasa Koda daga qafan, ya miqa Mata hannun shi Mai riqe da bindigar ta Kama ta tashi sai tasa Kuka a tunanin ta Bata yayi ta kashe kanta tunda ta Saba ma umarnin shi,

Jin zafin harsashin na dada ratsa tsoka da jijiyoyin jikin shi ya saka ya qaleta ya wuce cikin gidan Yana Shiga toilet ya cire rigan shi sannan ya fara qoqarin cire bullet din daga jikinshi,

Yasha baqar wahala kafin ya cire bullet din ya dinke wurin ya saka bandage ya rufe wurin ya dauro alwala, Yana fitowa daga toilet ya hango Leesa tsaye jikin qofa kallo Daya yayi Mata ya watsar ya bude wardrobe ya Ciro wani T shirt ya daura a Kan singlet dinshi Mai jini ya tada sallah,

Har ya idar Leesa na tsaye a wurin kamar soja Bai bi ta kanta ba ya wuce parlor ta dingisa ta bishi a baya, ba'a dade ba daya daga cikin yaran shi ya shigo da leda Mai dauke da take away guda biyu ya ajiye, ya dura ruwan allura a syringe yayi ma Sa'ood Yana gamawa ya fita,

Da dingishi ta qaraso wurin da take zaune

"Ba zaka je asibiti bane?"

Dagowa yayi Yana Mata wani irin kallo yace "Ina ruwanki?"

"To ni ka kaini gidan Mai dauri kaga na targade a qafa"

"Saboda ki Sami damar escaping ba? Ki bari zan saka a kawo Miki magani ki shafa a wurin"

" Maganin bazai yi amfani ba ai tunda ba'a ja qafan ba"

"You are kidding me, kin taba ganin mutum ya targade a qafa Kuma yazo takawa da qafan? To Bari kiji keda fita daga gidan Nan sai randa Naga dama, Kuma ki sake kuskuren trying guduwa ki gani wallahi saina fasa kanki da bullet ki qara gwadawa ki gani, ki dauki abincinki ki bani guri a nan "

Jin zancen fasa Kai da bindiga yasa sidin_sidin Leesa ta dauki takeaway daya ta koma gefe tana ci a hankali tana kallon Sa'ood lokaci daya tunanin qanwar ta dake wurin Sa'eed ya Fado mata, ko yanzu a wani Hali Salee take Allah masani, Allah dai yasa halin Sa'eed ba irin na wannan Dan fashin bane,

Tana lure da Yanda yake runtse Ido idan ciwon ya Dan tabashi Amman ko gizau bayi yi saboda taurin zuciya,

"Wurin na ciwo sosai ne?" Yaji ta fada, Bai kula ta ba ya dauko wayarshi Yana dannawa Amman still Yana Jin zafin wurin,

"To ka tafi asibiti Mana, kana ta Jin zafi kaqi kaje su baka magani kaqi duk jinin jikin ka ya qare kana zaune sauran mutuwa kawai ya ra....."

Cikin tsawa yace "shut up, I said shut up please, don't ever forget that you are a prisoner in this house Baki da iko a Kan kowa da komai na cikinsa so please mind your own business crazy girl"

Bata sake magana har zuwa wani lokaci Kiran waya ya shigo Masa da sauri ya fita ya bar gidan, tafiya sukeyi a mota ranshi fari sol domin haqar shi ta cimma ruwa, Saida sukaje gidan alhaji Habib ya Shiga motan shi suka sake daukan hanya,

A wani qaramin gida suka tsaya suka kafin su Shiga ciki Saida aka caje su ciki da waje, daga shigar su suka hangoshi zaune qafarshi Daya Kan daya ga wata qatuwar Kare a gefe sai muzurai take,

Dogo ne baqi murdadde bayi da kyan gani tun daga kanshi har fuskar shi qwal yake babu gashi sai shining yake fuskar shi babu annuri,

Wani kallo Sa'ood yake binshi dashi ruwan tsanar shi kwance a idanun shi Bayan wahalar na shekaru masu yawa yau Allah ya hadashi da babban maqiyin shi a duniya Wanda ya kashe Masa mutumin da yake a matsayin mahaifin shi, mutumin da ya zamo musu garkuwa ya fitar dashi da 'dan uwanshi daga quncin maraici har yau Yana ganin jinin Daddy Aliyyu a hannun Garba TK,

Shine sanadin da har yau mamanmu Bata tashi daga gadon asibiti ba, shine sanadin rarrabuwan Kan mailafiya family harda ma batan Sarwa Dan yafi Sa'eed laifi tunda shi sakaci yayi yabar su suka Bata,

Ji yakeyi kaman a yanzu ya kashe Garba TK irin kisan wulaqancin da ko Kare sai ya tausaya Masa saidai bayida Daman yi hakan yanzu Amman da Yana da dama da yayi Masa albishirin kusantowar ranar mutuwansa dan tunda sukayi Ido biyu dashi kwanan shi ya kusa qarewa,

Qarasawa gaban shi sukayi duk matsayi da ji da Kan alhaji Habib Saida ya rusuna mishi Amman Allah ya gani Sa'ood bazai iya tausasa zuciyar shi yayi hakan ba shiyasa a tsatsatsaye suka gaisa Sannan ya fara kwararo musu bayanin abinda ya faru Kan cewa KB shaye_shaye shiyasa suka samu matsala a operation dinsu dukda sunyi nasarar amshe Rabin abinda suke buqata,

Garba TK ba qaramin gwada bacin ranshi yayi na abinda kb ya aikata yayi ba a lokacin Kuma ya cire shi daga sahun yaranshi aka bada Sa'ood matsayin shi dan shi a tunanin shi qoqarin da Sa'ood yayi musu ne ya jawo Harbin dake kafadar shi,

Sa'ood yaji dadin wannan hukunci sosai har Allah Allah takeyi su Gama tattaunawa yaje ya sanar ma mamanmu da momy da Idris yasan ba qaramin farin ciki zasuyi ba burin su ya kusa cika,

**********
Leesa na zaune a parlo tana kallon dole taji ana qwanqwasa qofa, tana budewa Daya daga cikin yaran Sa'ood ya miqo Mata shopping bag tana karba ya juya ba tare da yace Mata komai ba,

Rufe qofar tayi ta koma ta bude laidan tana dubawa, Kaya ne ready made kala biyar harda undies, sai kuma maganin ciwon qafanta a ciki, kunya sosai ya Kamata wannan Sa'ood din Dan iska ne, a tunanin ta shi ya sayo Amman shi kawai kudi ya bayar ma me musu leqen asiri dan duk cikin su ita kadaice mace,

Wanka Leesa ta yi ta saka daya daga ciki ta wanke Wanda ta cire, ta fito zata shanya su a Kan flowers din gidan taga an ajiye takeaways guda biyu a bakin qofa, Saida tayi shanyan ta dawo kafin ta daga taci daya ta ajiye Masa Daya dan tasan dayan na Sa'ood ne,

Tunda ya dawo ya tsiri zama tare da bindiga matuqar Leesa na kusa dashi ta da bindiga a gefen say don tambaye tambayenta sun fara isan shi, saidai Bata ga Abu ba sai tayi tambaya a kanshi,

*********

Sa'eed yazo fita daga gidan Salee tayi saurin riqo shi tana kuka Mai tsuma zuciya, gashi duk ta jeme tayi duhu idanun ta sun fada,

Ya Sa'eed dan Allah ka taimaka min wallahi nasan ba lafiya ba tunda har sabon wata yayi nisa Banga saqon ta ba na tabbata wani Abu ne ya same ta Dan Allah ka taimaka ka nemo min Yar uwata na roqe ka,

#vote
#share
#comment

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now