"Dan girman Allah kawu Dan qaunar da kakeyi wa Annabi Muhammad (saw) ka taimaka ka kaini gida wallahi nayi alqawarin bazan sake dawowa Kano ba har duniya ta nade, da Dinma qaddara ce ta shigo Dani, Amman ko Sa'eed bazai San na sanka ba wallahi tallahi, ka rufamin asiri kawu"

Maganar ta ba qaramin bashi dariya yayi ba aikuwa Saida ya Dara, dukda iskan fanka sai zufa take hadawa ga hawaye harda majina a Kan fuskar ta shi Bai taba ganin yarinya Mai tsoro irin wannan ba,

"Gwanda ma kije ki fada ma Sa'eed din idan nazo kashe shi Kinga sai na hada dake dukan ku na harbe ku da wancan bindigan"

Aikuwa kaman ance Leesa qara volume ta sake fashewa da kuka ganin bindigan Sa'ood ya taka Wanda ta gani a dakin alhaji girma,

"Wayyo Allah na Shiga uku kawu Dan Allah ka tausaya min, wallahi na sake ganin bindiga zan mutu"

Da mamaki yace "ko?"

Gyada Kai tayi " eh wallahi"

Ya miqe ya dauko sniper rifle da zasu fita operation dashi tsakar dare ya wurga Mata a Kan cinyar ta, ta daka wani wawan tsalle tana qwalla uban ihu ta koma can gefe tana kallon bindigar numfashin ta Yana sama_sama,

"Yaya har yanzu Baki mutu ba? Ina jira ki mutune dan na samu sauqi wurin aiki na, idan Kika bar duniyar Nan bani da asara iyakaci nasa yara na su dauki gawar ki a tona Rami a birne ki shikkenan, Kinga bani da sauran tsoro a Kan wani zai tona min asiri"

" Wallahi baniso na mutu yanzu bazan koma wurin Sa'eed din ba ma wata uwa duniya zan tafi Daman wurin da zanje din ma ba gidan mu bane gidan su qawata ce"

" A kan mene kike zama gidan su qawarki baki da iyayene da bazaki je gidan ku ki zauna ba?"

"eh wallahi, bani dashi Kuma baniso in samu"

"Amman kinsan mutanen Nan har yanzu niman ki sukeyi Kuma idan suka same ki Suma kashe ki zasuyi da babban bindiga irin wannan idan kina cikin gidan Nan ne kawai babu Wanda zai iya kawo Miki hari, Amman idan Baki amince da hakan ba Zaki iya tafiya su kamaki su harbe ki Ni Kuma na qona gawarki"

" Aa ni kawai ka kaini gida da kanka Dan Allah"

" To indai da gaske kinason zuwa gida lafiya ba tare da kin mutu ba sai kinbi dukka dokoki na kinji ko?"

Gyada Kai tayi, yace " Yaya sunan ki?"
"Haleesa"
"Haleesa very sweet name Nima Ina da 'yar uwa Haleesa, wata 'yar uwar ki ne take wurin Sa'eed da Kika rubuta a cikin papern da kika saka cikin aljihun riga ta?"

Shiru Leesa tayi ita Sa'eed ma tsoron shi take ballantana wannan Dan fashi da makamin Mai kashe mutane, yanzu idan ta fada mishi wani Abu a Kan Salee zuwa zaiyi ya hadu da 'dan uwan shi su kasheta ta Shiga uku, ita kadai ta rage Mata a duniyar Nan ba zata juri rasata ba,

"Yaya kikayi shiru? Ki fadamin abunda Sa'eed yayi ma 'yar uwarki yanzu naje na rabashi da duniya dan na lura daman kaman ya gaji da zaman cikin ta"

Dafe qirji Leesa tayi ta zaro idanu cike da mamaki tace " 'dan uwan naka ne zaka kashe?"

Murmushi yayi yace "an fada Miki Dan fashi da makami kaman Yanda Kika ce Yana da sabo ne? Ai shi bayi da aboki, Duk Wanda yayi qoqarin kawo mishi matsala maqiyin shi ne Kuma zaiyi komenene ganin ya kawarda dashi Koda Sa'eed ne ko kuwa kece, tashi ki wuce kiyi sallah"

Tashi tayi har tana hadawa da tuntube ta Shiga qofar da ya nuna Mata a matsayin toilet, tana mamakin Sa'eed wani irin mutum ne haka Yana nan kaman Mai hankali Amman lokaci Daya sai ya koma mahaukaci, ita dai Allah ya shigo da ita hannun shi babu abinda zata iya sai Yanda Allah yayi da ita.

**********

Suna zaune a Kan tabarma Salee ta kwantar da Islam a Kan cinyar ta tana musu tatsuniyar dare ita da al'amin, Zarah ma tana zaune a qofar dakin ta tana sauraron su,

Saida ta gama kafin tace " to wa zai fadamin tsakanin sarki da waziri da gizo wa yafi wayo?"

Da sauri Islam ta daga hannun ta al'amin ya bige yana hararar ta, "kullum ke kike bada fada ni Baki aunty tana Kira na good boy ko yaushe kece kawai good girl"

Dan Bata fuska Salee tayi tace " Yaya bamuson cin Zali ai basai ka daketa bane za'ace maka good boy, baby na fada Mana amsar kinji"

Gwalo tayi ma Al'amin tace " gizo ne yafi wayo saboda ya cinye Rabin garin sarki"

Tsaki Zarah taja tace "dukkan ku wawaye ne ana maganar kudi kina maganar gari, jiqa garin zaiyi a ruwa ya Sha? Amman waziri da ya samu kudi yanzu babu abinda bazai siya ba Dan Allah Salee kada ki tusa ma yarana wani banzan aqida irin naki ki barsu su so kudi kawai ai kudi abin so ne"

Murmushi kawai Salee tayi tace su Al'amin su tafi daki su kwanta itama ta miqe zata Shiga dakin ta ta shirya Sa'eed ya kusan shigowa dan yanzu an raba musu kwana Salee ta Shiga jerin matanshi babu Yanda ya iya,

"Momyn al'amin Saida safe" da "uhm hm" ta amsa mata, har ta kusa Shiga dakin ta ta juyo tace
"Momyn al'amin akwai sauran nama ne a cikin fridge Naga wani girki ne dazu a TVn ki shi nake so nayi Mana gobe,

"Na fridge Kam Allah yayi Masa rasuwa saidai ki fada ma miel ya kawo wani gobe"

"Toh" kawai tace ta juya...........🧚

#vote
#share
#comment

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now