Qura Mata Ido yayi Yana kallon cikin idanun ta da suka Tara hawayen tsoro, baisan dalili ba Amman idan idanun ta sukayi haka qara kyau suke Masa suna kashe Masa jiki har wani shining sukeyi,

Sauqo da idanun shi yayi Yana kallon lips dinta da suke trembling ya saki murmushi yaufa zai more, fesa Mata iska yayi a fuska tayi saurin kawar da Kai tana Jan tsaki,

"Baby Yaya akayi Kika zamo ta daban ce? Komai naki daban yake Dan haka tukuicin ki ma zai zamo daban, ki Fadi duk abinda kike so nayi Miki ni Kuma nayi alqawarin zuwa yammaci zan Miki shi, ko mota ko kudi ke na qare Miki zance idan ma wani qasa kike son fita ko Ina ne zan kaiki Kinga daga baya sai na biyo ki mu cigaba da Jin dadin mu a can right?"

Galla Mishi harara Leesa tayi ta ja dogon tsaki fuska a tamke tace "da'alla malam 'dagani tunda na lura baka da mutumci baka cancanci a girmama ka ba, ka daga ni ko yanzu nayi maka abinda baka tsammani ni ba irin 'yan iskan matan banzan ka bane kaji na gaya maka"

Murmushi yayi yace "to Bari na maidake irinsu Kinga sai komai ya tafi dai_dai, ya daga hannun shi Yana Shirin sauqe sa a Kan qirjin ta tayi saurin zaro qaramin wuqan dake boye a jikinta ta Bai Ankara ba sai ji yayi ta tsaga mishi tafin hannu,

Cikin radadi da azaba yayi saurin tallafo hannun Yana matse fuska ga jini dake kwaranya a qasa, da sauri Leesa ta jefar da wuqan ta saka hannunta cikin aljihun shi ta ciro key ta bude qofar ta fita da gudu,

Bata ko koma ciki ba tayi hanyar waje tasan ko qara minti daya tayi a cikin gidan Nan kaman ta salwantar da rayuwar ta ne, ga jakar kayanta da 'yan kudaden ta a dakinsu Amman babu halin dauka dole kawai ta gudu ta tseratar da rayuwar ta,

Saida ta daidaita kanta kafin ta qarasa gate ta nemi su bude Mata ta fita, babu musu suka bude Mata Dan sunsan takan je gida lokaci zuwa lokaci hala tafiyar Tata ne ya tashi,

Tana fita daga gidan ta sake dibawa da Dan iskan gudu Dan taji ana Kiran security tasan ita zasu biyo shiyasa tayi amfani da iya qarfin ta take zabga uban gudu,

Saida ta fita daga unguwar wata mota ta ja birki a gaban ta aka bude Mata back seat taji wani murya yace Shiga mu tafi, batayi wani tunani ba ta shige ciki Dan taga motocin su suna biyota, tunda ta Shiga motar Bata sake sanin inda take ba,

Sai bude idon ta tayi tagan ta a kishingide a Kan armchair a wani daki babu abinda ya firgita ta kaman Sa'eed da ta gani zaune Yana facing dinta ya qura Mata Ido, a razane tace "Sa'eed!!! Ina ne nan? Me yasa ka kawo wurin nan? Ina....."

"Shhhh please take it easy ni ba Sa'eed bane"

" Mai kake nufi? Ka dauka ban sanka bane ko me? Ko Nima yaudarar tawa kake son yi?"

" Seriously bani bane Sa'eed" yayi displaying pic dinsu tare a wayanshi ya miqa Mata, karba tayi tana mamakin zallan Kama da sukeyi kaman ita da Salee,

"Suna na Sa'ood, ni twin brothern shi ne Amman a Ina Kika sanshi?"

"A garin mu na sanshi, Dan Allah ka kaini gida inaso na tafi jigawa a yau dinnan na koma wurin 'yar uwata"

"Dare yayi yanzu ki tashi kiyi sallah  sai ki huta zan turo Miki da abinci" Yana fadan haka ya miqe zai tafi tayi saurin jawo qasan rigan shi, ya juyo Yana binta da wani qasqantaccen kallo, "sake ni" ya fada cikin wata muryan bada umarni,

Sake shi tayi tace "Dan Allah kawu Sa'ood ka kaini gida, I need to go and save my sister please ka fitar Dani daga nan"

" Kiyi haquri Amman bazan iya hakan ba yanzu, kin riga kin sanni Zaki Bata min aiki, sai na samu na kashe Wanda nake buri kafin na barki ki tafi, yanzu Zaki iya amfani dake su gurfanar da ni da family na ma gaba daya"

Kuka Mai sauti Leesa ta saka, ta fita daga qaramin matsala ta Shiga babba, yau gata ga makashi saboda tsananin tsoro ji takeyi kaman ta saki fitsari a jikin ta, Ashe ba zallan Sa'eed ba harda 'dan uwan shi mutanen banza ne shikkenan qarshen su ita da Salee yazo,

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now