"Reina Yaya kike ganin yanzu idan na Kira Sa'ood na fada mishi Sa'eed yayi aure?" Dan murmushi ya sake yace "I can't imagine irin tashi hankalin da gaba dayan su nasan sai ya saka bindiga a Kan amaryan Nan ya harbe ta"

Da sauri Nabeela ta ajiye comb din hannun ta ta qaraso kusa dashi ta tsunguna hawaye na taruwa a idanun ta
"Dan girman Allah kada kayi Haka Amor, Mun samu zaman kwanciyar hankali Bayan lokaci mai tsawo Dan Allah kayi haquri haka Nan Sa'eed ya riga yayi maka alqawarin zai dawo da Sarwa cikin qanqanin lokaci ka daga Masa qafa"

" Amman Baki da wayo beelat tsawon shekaru 17 Kenan Sa'eed na Mana wannan alqawarin har yau Bai cika shi ba, Baki ganin wannan wata dama ce da muka samu da zamu saka shi yayi abinda muke so"

Girgiza Kai tayi hawayen dake idon ta suna samun damar sauqowa Kan cheeks dinta
"No please don't do this ka daga mishi qafa zuwa Nan gaba na yarda zaka iya fada mishi zancen auren Amman ba yanzu ba nasan ko baka fada mishi ba zai sani ,ko badan shi ba ka tausaya ma matar da ya aura 'yar qaramace sosai wallahi"

" Shikkenan Sa'eed yaci darajan ki Amman Nan da wata biyu idan Bai kawo min Sarwa ba hmm babu Wanda ya Isa ya cire shi daga matsalan da zan saka shi"

Da sauri ta gyada Kai hade da fadin "eh na yarda" tana da hope kafin lokacin hala Sa'eed ya samo Sarwa,idanma bai samo ta ba zata sake dakatar dashi a Kan mugun nufin shi tunda bayi iya komai sai ya sanar da ita,

**********

Washe gari asuba Salee ta farka hawayen fuskar ta ya Gama bushewa, tashi tayi ta kunna wutan dakin tana kallin fuskar ta a jikin mirror,

Jan qafarta tayi ta shiga toilet tayi alwala sannan ta fiddo da darduma daga cikin akwatin ta tayi sallah, tana idarwa ta wanko toilet dinta ta gyara dakin ta Tass sannan ta fita waje,

Cikin sa'a akwai ruwa a famfo ta cika komai sannan wanke tsakar gidan ta daura musu ruwan wanka a murhun gawayi, har tayi wanka ta shirya tayi breakfast Zarah na sharar bacci da yaran ta, Basu fito ba sai 9 lokacin Salee ta gama Gama hada breakfast, har yanzu tana cikin damuwar abin da ya Hana Sa'eed dawowa gida tun jiya,

Zarah na farkawa taga gida ba a atmospheren da ta 'yan biki suka barshi jiya ba, fitowa tayi ta bude food plask din da tagani a bakin qofar ta taci Karo da lafiyayyen abinci, bata Gama mamaki ba Salee ta qaraso wurin da take tsaye fuska a sake tace
"Ina kwana aunty Zarah"

Kallon sama da qasa tayi Mata babu laifi tayi kyau cikin sabuwar atamfar ta dinkin ya zauna dass a jikin ta, tabe Baki tayi tace

"Ashe Daman karuwai sun it's gaisuwa?"

Sosai Salee taji zafin kalaman ta Amman sai ta share ta nuna Mata food plask din da ta ajiye Mata abinci tace
"Momyn al'amin ga abincin ki"

Tsungunawa tayi ta dauka tace
"Na gode Amman ba sai kin nuna zaqewa da yawa ba, ki haqura na Baki girkin Mana Amman kinyi caraf kin dauka ke bakisan mace tana da kunya bane? Ko dayake karuwai Basu dashi, nasan kinzo tambayan angon naki ne ko juya baizo ya raya daren ku ba right? Ki qara haquri fa idan ya dawo sai kin gaji dashi, ohh Ashe Bai Kamata na Fadi haka ba tunda already Kun riga Kun Saba"

Duk Yanda Salee tayi qoqarin shanye kukanta kasawa tayi Maganganun Zarah sunyi Mata tsauri da yawa Ashe abun da ke cikin gidan Sa'eed dinta Kenan tun daga day one ta fara cin Karo da bacin rai,

Shaida Tasha kukan ta ta qoshi sannan ta wanke fuskarta ta sake fitowa ta samu Zarah ta shimfida taburma a tsakar gidan ita da yaranta suna kwasan girki,

Haka ta zauna tana kallon su har suka Gama ta dauki Islam tayi Mata wanka ta tura ta wurin Zarah ta shiryata, al'amin ma har toilet takai mishi ruwa ta saka musu wani abincin daban a lunch box, tana Jin zagin kasuwan da Zarah take mata amman ta basar ta dauki mayafinta ta raka yaran qofar gida,

Daidai zasu fita saiga Sa'eed Yana shigowa, tsayawa yayi Yana kallon su yaran suka qaraso suka rungume shi, peck sukayi mishi a cheeks suka Kama hannun juna tare dayi musu sallama suka wace makaranta,

Murmushi tayi tadan duqa kadan tace "Ina kwana ya Sa'eed barka da dawowa" ta miqa hannun ta ta karbi manyan laidojin hannun shi,

Sosai yaji kunyar ta ya dauka zatayi fushi sai Kuma yaga akasin haka, lallai Salee yarinya ce tunda Bata gane girman laifin da yayi Mata ba,

Dan Sosa qeya yayi yace
"I'm sorry babe jiya banzo gareki ba kiyi haquri uzuri ne ya taso min Amman insha Allah....."

Bata Bari ya qarasa magana ba tayi saurin shigewa ciki harda hadawa da Dan gudun ta, Sa'eed Saida ya dara Dan shi babu Wani abu da ya fada na Jin kunya a Nan, bin bayanta yayi fuskar shi dauke da murmushi aikuwa shigan su sai a idon Zarah tana jabe a wurin da Salee ta barta gaban kwanon abincin da sunfi 30 minutes da cinyewa Amman kawar dashi daga wurin ya gagara,

Kallon su gaba Daya tayi taja tsaki ta tashi ta wuce ciki, ganin haka yasa jikin Salee yayi sanyi batason tana ganin bacin ran Zarah batasan dalili ba,

Ratsawa tayi ta gefen Sa'eed zata wuce ya riqo hannun ta Yana Jin laushin sa cikin nashi kaman auduga ga yatsunta sirara kaurin hannun ta Bai wuce na al'amin ba ya ayyana a ranshi,

Dawowa gaban shi tayi tana kallon shi, ya miqo Mata Daya daga cikin laidan hannun shi
"Gashi babe bashin kazar ki da kike bi na, na biyaki ko?"

Girgiza Kai tayi tace "no na yafe babu bashi a tsakanin mu ka kaiwa momyn al'amin ta raba sai a bani kaso na"

" Aa babe wannan naki ne ke kadai suna ga nasu Nan"

Karba tayi tana murna duk da ba wani 'da'data da qasa Naman yayi ba,

"Na gode sosai Allah ya qara arziqi Mai albarka"

Lumshe idanu yayi ranshi na mishi Dadi ya amsa da "ameeen babe, Bari na sallami auntyn ki sai muzo muyi magana, yanzu kije ki huta nasan ki gaji"

Gyada Kai tayi ta juya shiga dakinta shi Kuma ya wuce dakin Zarah, ta fito daga wanka Kenan daure da farin towel a jikinta yace ta zauna suyi magana, batayi musu ba zauna tana sauraron shi,

"Mi Alma please ki bani hadin Kai wurin tabbatar da zaman lafiya a cikin gidan Nan Kinga kece shugaba dan Haka Ina matuqar buqatar taimakon ki, ki zauna da yarinyan Nan lafiya Ina da tabbacin zatayi respecting dinki don nasan irin macen da na aura"

" To angon jaririya, gashi ya Sa'ood baiyi ba Kai kayi, ko kunya fa bakaji Wai da sunan kayi aure kaje ka auro 'yar yarinyan da Bata wuce sa'an Sarwa ba har zakace nayi zauna lafiya da ita, to Ina abun tashin hankali a Nan da 'yar ciki na kake son nayi kishi Allah ya tsare ni"

" Itadin Sarwa ce Zarah" ya Fadi haka Yana so yaga reaction dinta,

Da sauri ta miqe ta dafe qirji tace "miel Sarwa fa kace! To Ina Yar uwar ta? Arziqin mu ya dawo wayyo Dadi alhamdulillah"

" Ke nifa ba haka nake nufi ba, I mean da ace ita sarwan ce Zaki zauna da ita?"

" Mtsww kaji wani abun haushi, wallahi na dauka da gaske kakeyi har na fara ganin kaina cikin mailafiya mansion ga danqara danqaran motoci sai Wanda na zaba, maids ta ko Ina sunamin hidima tufafi kuwa idan yayi qasa da 50k bani sakawa, gaskiya ka jamin Rai Kuma ban yafe ba"

Qaramin murmushi Sa'eed yayi dama yasan Zarah ba matan sirri bace, ko mutuwa zaiyi idan tasan su Salee be Sarwa sai fallasa,

Haka suka qare maganar rabi tsiya da rashin arziqi ya koma wurin Salee itama yayi Mata Bata jawabin wanda nusar da ita tayi biyayya ma Zarah da haqurin zama da ita yafi yawa Dan shima Bai tsallake uqubar ta ba,

Bai hadasu ya musu tare bane saboda yasan zaman shi da Salee ba Mai daure wa bane so no need ayi wani rabon kwana and stuff's,

Yana shiga wankanta gyare dakin shi Tass kafin ya fito ta fesa air freshener ta fita shirya abincin Rana Dan already 12 ta wuce, Sa'eed da kanshi ya fita samo Mata Dan aika ta bashi saqon duk abinda za'a siyo Mata tana jin kaman tayi abincin Rana Kuma kaman ta Bari Dan har yanzu maganar da Zarah ta fada Mata da Rana Yana Dan damun ta............🧚

*Manage,😁*

*Ummu najma ce😘*

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now