Runtse idanu Sa'eed yayi da yaji ya ambaci sunan Saleeha, wato har yanzu Sa'ood na burin ta zamo matar shi? Qaddara batayi musu adalci ba da ta raba tsakanin su ta Sanya zai rushe burin 'dan uwan shi ba tare da son ranshi ba.

Gaba daya tunanin shi yayi nisa Bai ji sauran maganar da Sa'ood yayi ba har ya katse Kiran.

Inama ace Yana da wani hanyar da zai dawo da Salee gidan shi ba tare da ya aure ta ba! Yasan hakan ba Mai yiwuwa bane dan babu macen da zata yarda mijin ta ya kawo Mata wata haka kawai da sunan ta zauna tare dasu ba tare da wani kwakwkwaran dalili ba bare ma mace irin Zarah dole sai taji ba'asi bayi da Yanda zaiyi ya kula da Salee Kuma ya jawo hankalin Leesa ta dawo gida inba auren ta yayi ba.

Ganin tunani bazai ficce shi ba yasa ya tashi ya shirya ya tafi wurin Salee Yana so ya nuna Mata kaman Yana sonta don Kar ta fahimci wani abun, Bai nemi abinci wurin Zarah ba don har yanzu ba girkawa dashi take yi ba a gurin Salee yake kwasan girki,

Ko minti 10 da Isa baiyi ba ta fito taci ado babu laifi tayi kyau don  'yammatan shugaba sun dage wurin koya mata ado da kwalliya, hannun ta dauke da food plask din abincin shi da jug da cup,

Kallon dan yale yalen qaramin gyalen dake yafe a jikin ta da ko gadon Bayan ta Bai rufe ba yayi Ya girgiza Kai ya shimfida musu tabarma dake jingine a jikin bango suka zauna.

Murmushi dauke a fuskar ta ta gaida shi sai faman sunne Kai qasa take yi a dole tana Jin kunya,

"Kina so ki koyi rashin ji ko? Na Hana ki yin kwalliya da fitowa babu lullubi Amman kinqi ki Bari Mai yasa?"

Murya na rawa tace " kayi haquri malam Sa'eed umm...ma...makai fa nake yi kaga matar ka ta fini kyau...shh.. shiyasa ita..ita bata yi"

" To ki bari, idan yaso idan Kika shigo gida na sai kiyi son ranki Amman ban yarda ki sake fito min haka babu hijab ba Kuma bani son ki sake kwalliya, kema kyakkyawa ce kinji ko?"

Gyada Kai tayi, tana Jin Dadi sosai duk lokacin da Sa'eed ya yabe ta.

"And one more thing bani son wannan malam Sa'eed da kullum kike Kira na dashi idan matata taji zatayi Miki dariya, yaya Sa'eed Zaki dinga Kira na daga yanzu"

Gyada Kai tayi tace " to" sannan ta fara matso Masa da abincin gaban shi,

Shikuma he is lost looking at her, Yanda take qoqarin kame kanta kada tayi mishi ba dai_dai ba, Yana tausayin ta sosai Yana tausaya Mata da irin zaman da zasu yi tare ga Zarah a tsakani, Salee tayi qarama ma kalubalen da suke gaban ta amman Yaya zatayi? Dan Adam bayi wuce qaddarar sa.

Saida ya Gama cin abincin sannan suka fara hira, dukda kasancewar shi gwani wurin tsara zance da sace zuciyan Yan Mata cikin kalma daya a baya a yanzu yakan rasa me zai fada ma Salee ya Sanya ta nishadi, kwata_kwata wannan ba irin soyayyar da sukayi da Zarah bane Wanda ke cike da alfasha da ketare iyakokin Allah,

A haka dai suka qarasa hira, yawancin tadin a Kan Leesa ne don Sa'eed naso cikin dabara ya samu wani clue da zai gano inda Leesa take cikin sauri ba tare da ya auri Salee ba,

*********
9:22pm

"Dan Allah ki kwanta kuyi barci wallahi surutun ya hana ni rintsawa" Leesa ta fada tana Jan abun da take lullubuwa ta rufe fuskar ta,

Tashi Bilkisu tayi daga Kan gadon ta ta haura gadon Leesa dake sama ta yaye lullubin ta tana jijjiga ta da iya qarfin ta
"Ki tashi da'alla, ana Hira kin maqale a gado ki sauqo kema ayi da ke wannan shine kadai lokacin da muke dashi na junan mu"

Tashi tayi ta zauna cikin hasala tace " innalillahi ana Hira dole ne bilki? Ni 9 nake barci a gida ki rabu Dani barci nake ji kinsan yawan aikin da muke dashi gobe gwanda ki kwanta ki huta ma ranki"

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now