Saboda Yanda ranshi ya baci ya kasa Mata magana Dan idan ya bude bakin shi Yana Jin kaman zai amayar da ranshi.

"Shikkenan alamu sun Gama bayyana a zahiri komai ya tabbata, yau na shaida ka daga hannun ka ka daki matar ka A kan karuwa Abu Daya ya rage, shine ka auro ta ka kawo ta cikin gidan Nan tana goga kafada dani sai nasan iskancin naku ya girmama ba qaramin bane"

Kamo hannun Salee dake sharban kuka yayi yazo daff da Zarah Yana kallon fargaban dake kwance a qasan idonta yace
"Wait and watch"  sannan ya ja ta suka bar Mata gidan.

Suna fita tayi daki da gudu tana kuka, ta gode ma Allah da yasa su al'amin sunje wuni gidan Idris da ya karuwan uban su a gaban idon su zata shigo gidan.

Sa'eed kuwa Jan Salee kawai yake yi a zuciye duk inda suka wuce sai an bisu da kallo a haka har suka Isa qofar gidan Shugaba, birki yaci ya tura ta ciki sannan yabar wurin a fusace.

Kaman ance ta juya sai idon ta cikin na Leesa itama ranta a bace ta finciko hijab dinta ta jawo ta cikin dakin su, suna shiga ta kwashe ta da Mari, kafin ta dago ta qara Mata wani sannan ta rufe ta da duka.

Kuka Salee take yi kaman ranta zai fita ta rasa da wanne daya zataji, da gudu Lateefa Tayo kansu tana qoqarin raba su Amman leesah tayi Mata mummunan riqo sai jibgan ta take yi kaman Allah ne ya aiko ta.

Saida shugaba ta taso da kanta ta shiga tsakanin su kafin Leesa ta tashi daga Kan Salee ta koma gefe tana haki.

**********

Sa'ood ne kwance a Kan madaidaiciyar bed dinshi sanye da singlet da three quarter, gaba Daya jikin shi a mummurde ba kaman na Sa'eed ba, ya zurfafa cikin tunani,
Har yanzu ya kasa cika alqawarin da ya daukar wa maman mu na kula Mata da Sarwa, Yana tuna lokacin da yake zaune a parlon ta Bayan ya gudo ma sumy ya samu maman mu na Shan fruit salad da tsohon cikin ta qatoto.

Bai Bata lokaci ba ya dauko spoon ya saka a ciki ya cigaba da Loma, murmushi tayi tana kallon shi tace

"Sa'ood Chéri har yanzu gudun 'yammata kake yi?"

" Nifa ba gudun su nake yi ba cariña sun cika takuri ne wallahi kaman wasu qudaje subi su ishi mutum ko Dan class din Nan na big girls Basu dashi"

" To haka zakayi ta zama babu aure? Yanzu fa qanin ka auren shi sauran wata biyu da sati uku Amman Kai ko budurwa baka tsayar ba"

Cika bakin sa yayi da fruits Yana fadin
" share Sa'eed Dan wahala ne shi, ni 'yarki nake so na aura, ko babu komai zata dauko qualities dinki Kuma duk Mai halinki wallahi ta Dace duniya da lahira idan har kin amince idan Kika aifi 'ya mace Zaki bani ni Kuma nayi Miki alqawarin ita kadai zan aura, Bayan ita babu qari"

Murmushin Jin Dadi mamanmu tayi tace
" To idan ba kyakkyawa na aifa ba fa? Yaya za'ayi ta zamo matar prince charming dina?"

" I don't care, ko ita tafi kowace 'ya mace Muni a duniya a haka na gani nake so saidai idan za'ayi min rowa"

" Duk abinda nake dashi naka ne 'dana na baka ita halak malak Kai kadai ne mijin baby na, I'm so proud to have you as my son in-law.

Tashi yayi yana rufe fuskan shi da hulan sweatshirt din jikin shi a dole Yana Jin kunyan ta, ya wuce dakin shi na part dinta ta bishi da kallo tana dariya, inama ace Yan matan dake binshi dasuzo suga abinda yake yi da wasu sai sun buga qasa sun rantse wannan ba Sa'ood bane.

Tashi yayi ya zauna Yana dubawa wallclock 6:30 har ya wuce jinginuwa yayi da garu zuciyar shi na mishi zafi yace
"I'm sorry cariña, na kasa cika alqawarin da na dauka na kula da Sarwa, na kasa Nemo ta na dawo Miki da ita I'm very sorry"

Ganin bayi da wani mafita yasa ya miqe ya shiga bathroom yayi alwalan magriba sannan ya saka milk colour jallabiya ya fice daga gidan.

**********

Bayan anyi su leesa sunyi sallan Isha shugaba ta Tara su a parlon ta kowa yayi kneeling a gaban ta tana sauraron shari'an tasu.

"Nasan nayi Miki alqawarin ba zamu shiga cikin 'yammatan ki ba saboda bamu San daga Ina muka fito ba, nayi Miki alqawarin zamu samo Miki kudi ta wani hanya daban Kuma Ina iya bakin qoqarina wurin kiyaye dokokin ki, Amman Salee ta karya wa'innan dokokin da sharudan shugaba har cikin gidan Nan aka zo aka Kira ta taje ta zubar da mutuncin ta Kuma ta dawo a wulaqance daga yau bazan sake shiga cikin abinda ya shafi Salee ba, na tsame hannuna a lamuran ta daga yanzu ita ba 'yar uwata bace"

Juyawa shugaba tayi ta fuskanci Salee tace
"Haka akayi?"

Da sauri ta girgiza kanta
" Aa shugaba, babu abinda Sa'eed yamin wallahi, bansan Mai yasa Leesa take min hassada ba,"

"Hassada Kuma Salee nice nake Miki hassadan?"

" Eh Mana wallahi tunda na hadu da Sa'eed Leesa take min baqin ciki, na riga na fada Mata Ina son Sa'eed Kuma fa mutumin kirki ne Amman tayi Kane_Kane ta Hana, Leesa ta maida ni kamar wata bajwar ta numfashi ne kawai nake shaqa bada Izinin ta ba, ni Dan Allah ta fita daga rayuwa ta, ta barni nayi amfani da dama ta tunda iyaye na da suka aife ni Basu Hana ni ba ai wani banza Bai Kamata yazo ya Hana ni ba"

Kuka Leesa ta saka ranta na suya, Wai yau Akan da namiji ne Salee take Kiran ta banza.

Sharia sosai shugaba tai musu kafin daga qarshe aka bada punishment ma Salee Wanda zata fara shi daga gobe.

Gaba daya a ranan Sa'eed Bai koma gida ba Dan baisan Mai zuciya zata tunzura shi yayi ma Zarah ba daga baya Kuma yazo Yana nadama, Daman akwai kudi da Dan yawa a jikin shi Wanda yake son zuwa sari dashi idan an kwana biyu, so Yana barin qofar gidan Shugaba ya wuce tashar mota ya shiga motan KANO, fatan shi daya ko da kuskure Allah Kar ya hada shi da Sa'ood.

Washe gari gaba daya aikin gidan Salee ne tayi Leesa Kuma ta shirya ta tafi makaranta, Bayan ta Gama jikin ta yayi luqus shugaba ta Bata abinci taci sannan ta saka ta kneeling a Rana ta umarce ta da ta daga hannuwan ta sama.

Har Leesa ta dawo daga school Salee Bata tashi a rana ba tayi kuka har ta gode ma Allah, Leesa na kallon 'yar uwar ta cikin wannan halin taji tausayin ta ya kama ta sosai, kaman take ta fadawa shugaba ta yafe Mata haka Nan Amman tana so tayi learning lesson dinta.

Rabawa tayi ta gefen ta zata wuce tajiyo muryar ta tana fadin
"Duk abinda zakiyi don ki raba no da Sa'eed ba Zaki ci nasara ba, ya riga ya zamo wani Bari na jiki na yafi Mun kowa a duniyar nan ciki harda ke, kince na zaba ko ke ko shi ko? To na Zabe shi sau dubu a kanki Leesa kiyi abinda Kika ga dama idan kinso kada ki barni da rai.

Kaman an ruwan narkakken dalma Hala taji maganar Salee tana qona zuciyar ta, shikkenan ranar da take gudu ya qaraso, amfanin ta a duniya yanzu ya qare tunda twin sistern ta no longer need her.

Batace Mata komai ba ta wuce dakin Shugaba ta Bata haquri a bar Salee haka ta yafe Mata.

Ana sake ta ko minti 5 Bata qara ba ta shiga daki ta dauko takarda da necklace dinta da aka tsince su dashi ta fita neman Sa'eed lokacin ma Bai dawo daga kano ba.

Ba ita ta sameshi ba sai Bayan sallan magrib shima da qyar ya yarda ya hadu da ita Dan yanzu ta fice mishi a Kai gaba daya tunda Shirin ruguza mishi aure take yi.

Bata bashi damar yi mata wani magana ba ta miqa mishi takardan
"Jiya matarka ta Kira ni da shegiya amman wannan takardan zai qaryata maganar ta please idan da Hali kaje ka gwada Mata ka Bata haquri"

Bai ma saurari abun da take fada ba ya fara duba takardan, abinda idanun shi ya fara cin Karo dashi shine MAILAFIYA HOSPITAL baro baro danqare a saman takardan...............🧚

#vote
#share
#comment

KAMA DA WANE....(Completed)Место, где живут истории. Откройте их для себя