"Kaje kace Bata nan"

Toh yaron yace ya juya ai kafin ya Isa qofa Salee ta dauko hijab dinta a guje ta tsallake Salee ta fita, ta saka hijab dinta ta daidaita nutsuwar ta kafin ta qarasa wurin shi tana fadada fara'ar ta., Ta dan rusuna sannan tace
"Ina wuni malam Sa'eed"

Kallon ta yayi daga sama har qasa ba tare da yace komai ba, gata fara ta bulbula Jan powder a fuskar ta bakin ta kaman tayi kiss da dan wake sai shining yake yi ita a Dole tayi don ta birgeshi ne don ba wani iya kwalliya tayi ba koda yaushe Leesa Hana ta takeyi.

"Goge fuskar ki" shine kawai abun da ya iya fada Mata, babu musu ta jawo hijab dinta ta ciki ta goge kwalliyan Tass, sannan ya juya hade da fadin "biyo ni"

Tafiya sukeyi baice Mata komai ba itama Bata sake magana ba sai faman zumbure zumbure baki takeyi Bai Yaba kwalliya da tayi mishi ba, Yana shiga gidan shi ta jaa ta tsaya daga waje tana faman zare idanu.

Juyowa yayi yaga Yanda ta qame kaman sabuwar soja yace
"Ki shigo Mana"

Girgiza Masa Kai tayi idon ta na cikowa da hawaye
"Ke matar gidan Nan ne take son ganin ki fah"

Sai a sannan ta daga qafar ta ta taka a hankali tana binshi a baya, Bata shiga gidan ba Saida taji motsi alaman da mutane a ciki kafin hankalin ta ya Dan kwanta.

Da Zarah suka fara cin Karo tana zaune a Kan kujera 'yar tsunguno ta daura qafarta daya Kan daya tana kadawa a hankali, wani mugun yawu Salee ta hadiya ganin irin kyau da zati ga haiba irin na wannan matar no wonder malam Sa'eed bayi kula 'yammata Ashe ya ajiye zinariya a cikin gidan shi ne.

Muryar shi ne ya katse Mata tunani da kallon qurillan da take ma Zarah.

"Salee ki fada Mata abinda take tsanin mu please explain to her tunda ta kasa fahimta ta"

Shiru tayi tana binsu da idanu, ta kalleshi ta kalleta ta rasa wani bayani ne Sa'eed yake so tayi ma wannan gimbiyar, so yake yi tace Mata tana son shi ne ko Kuma qaqa it Bata Gane ba.

Jin tayi shiru yasa ya juyo da duban shi wurin ta yace "Dan Allah ki Mata bayani menene a tsakani na dake!"

Ita fa Allah ya gani malam Sa'eed Yana saka ta a duhu, Koko matar ce tace tanason ya aurota ita Bata gane ba.

Miqewa Zarah tayi tana tafa hannuwa fuskar ta dauke da murmushin takaici ta qaraso har wurin da suke tsaye tana binsu da kallon wulaqanci daga shi har ita.

"Hmm Sa'eed Kenan wato da nace na gani shine bai ishe ka ba kaje ka dauko ta ka kawo karuwa har cikin gidana na Sunnah Dan is gwada min isar ka ko? Very good na ganta Yar qarama as you say but mannerless characterless, she is just a whore but I believe she means a lot to you tunda tana maka abinda kake so, ka Gama zubar da mutuncin ka a wurin Yar cikin ka inda ace na yarda na aifi al'amin da wuri da yanzu ya kusan kamota a tsaye, naga isar ka ka burge qwarai da gaske a round of  applause for my courageous useless husband.

kuma shegiyar karuwa" ta fada tana nuna Salee da yatsa "Wai tsaya ma, Mai yayi Miki zafi ne Kika bar gaban iyayen ki da qananun shekarun ki Kika fito duniya Bata mazajen mutane? Ko Dan ba'a same ki a hanya madaidaiciya bane kike so muma namu mazajen su ajiye Miki irin ku saboda ki samu magajiya ko? Kada tambadanci da iskanci ya qare ko ba haka bane?"

By this time hawaye ya Gama wanke fuskar Salee, irin baqaqen kalaman da Zarah take jifan ta da malam Sa'eed dinta harma da iyayen ta jinsu take yi kaman mashi suna sukar zuciyar ta.

Sa'eed kuwa haushi, baqin ciki da takaicin Zarah ne ya hanashi magana, yaukam ta Gama zubar mishi da mutunci a gaban yarinyar da take girmamawa matuqa.

"Kinaji ina tambayar ki Baki bani ams..."

Bata qarasa magana ba Sa'eed ya dauke ta da wani wawan Marin da Saida ta kusan faduwa,  Salee kuwa ta qara volume din kukan ta tana ayyana ta shiga ukwu a cikin zuciyar ta.

KAMA DA WANE....(Completed)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora