Duk tsafta irin na mamanmu Wanda take dashi tun tana yammata, lokacin da take orphanage ita tace winning prizes na cleaniness a hostel da class, farkon abinda ya fara jawo hankali dady Aliyyu gareta Kenan har yaje orphanage ya aurota ta zamo musu tauraruwa a MAILAFIYA family Amman Wai yau itace take Bayan gida a jikinta! rayuwa Kenan.

Saida suka kintsa ta tsaff kafin suka koma dakin cikin bacin rai Idris ya koma gefe Yana tura ma Sa'ood text cikin hanzari Nabila ta qaraso ta kwace wayar
"Please Amor(love) kodan darajan idon mamanmu ka girmama abunda take so, kafi kowa sanin batason abunda zai taba twins"

Baiyi Mata musu ba saboda yara dake wurin Saida suka koma gida tukunna yace ta bashi wayar shi tunda yanzu an tashi daga wurin saiya Ida nufin shi.

"What you are doing is absolutely wrong, ka dauki lafin batan Sarwa ka daura wa Ya Sa'eed Bayan bashi kadai bane doctorn da yayi operating baban Garba T.K yayi failing, I'm sorry to say Amman harda babanmu bawai Ina daura Masa laifi bane he also deserve justice Akan kisan shi da sukayi, kana hada marayu fada Allah bazai barka ba Amor, da Bata lokacin neman Sarwa a wurin Wanda Bai gansu ba da kukeyi gwanda ku hada qarfi da qarfe ku taimaka ma ya Sa'ood wurin daukar fansar abinda Garba TK yayi Mana gaba dayan mu, idan Kun Gama dashi ku bazama neman Sarwa I believe idan kukayi teamwork zakuyi nasara ai sarkin yawa yafi sarkin qarfi".

Zama Idris yayi a bakin gado ya riqe kanshi cikin damuwa yace
" Reina(queen) abinda kike tunani bazai taba yiwuwa ba, babu Yanda za'ayi na hada Kai da Sa'eed Sa'ood Bai kulle ni ba, ta Yanda aka saka ake cirewa na riga na Bata tsakanin su idan har nayi qoqarin fitar da Sa'eed daga cikin matsala to ni zan fada ciki, Su ba wawaye bane da bazasu bincika abunda nayi ba idan suka gano cewa ni nashirya munaqisan da ya shigar da Sa'eed prison wallahi ba zasu barni ba, ni duk nayi hakan ne badon komai ba sai dan ya fada Mana inda Sarwa take,

yanzu ni kadai na rage wa mamanmu sun kashe daddy sun sace Sarwa Bata da kowa a duniyar Nan Bayan ni, mi reina kece ma'ajiyin sirrina ki rufamin asiri nayi alqawarin idan har aka samu Sarwa mamanmu ta tashi akan qafuwan ta , zan miqa kaina wurin hukuma da kaina"

Kuka Nabila ta saka ta zauna a qasa ta hade kanta da guiwa tana rerawa, ita tunanin ta rayuwar yaran da suke gaban su har 3, babu danda zai so ganin ubanshi ya zamo criminal.

"Dan Allah Mai yasa qaddara zatayi Mana haka? Irin wannan babban rashin adalcin Mai mukayi da muka cancanci haka? Gaba dayanmu rayuwar mu ta wulaqanta, Mun rasa kowa mun rasa komai ya Allah Mun tuba ka kawo Mana dauki"

Kallon ta kawai Idris yakeyi yanajin dama ace shine yake iya zubar da hawaye haka da yaji dadin shi.

**********

Yau tunda Salee ta tashi take farin ciki yau Monday tasan idan take makaranta zata hadu da malam Sa'eed din Nan, she missed his beautiful face.

cikin sauri ta qarasa aikin awaransu dan yau itace zatakai tallan daman haka sukeyi idan yau Leesa taje talle to gobe itace zataje aji dan bazasu iya registration ma junan su gaba daya ba, dole suna karatu suna neman kudi don tun suna primary 4 shugaba ta cire hannun ta a cikin harqan karatun su, saboda malaman Basu cika banbanta su ba shiyasa Basu damu ba kawai akayi register da sunan Leesa Dan ita tafi son karatun.

9:25am

Ta Isa makarantar tun a filing break ta fara baza idanu ko zataga malam Sa'eed Amman Bata ganshi ba da alama ma yau baizo makarantar ba, damuwan ta ya gaza boyuwa har Leesa taso ta gane.

Allah_allah takeyi a tashi gida ko zatagan shi, sai taga lokaci yayi Mata tsayi kaman bayi tafiya taje waje ta leqa wurin da baba yake ajiye amalenken shi Amman bayinan, haka ta dawo ta zauna ranta babu Dadi Daman tasan malam Sa'eed dinnan ba sake dawowa makarantar zaiyi ba, ranar ma qaddara ce ta hadasu don kwata_kwata baiyi Kama da masu Saida kayan marmari ba.

Da aka tashi suka fito makarantar kamar kullum hannun su cikin na juna, Salee sai Jan qafafuwan takeyi tana zuba shagwaba ma Leesa har suka fito waje.

Kaman ance ta daga idon ta ta hango shi zaune a gefen amalenken baba, wayyo Dadi kasheta Ashe tana da rabon sake ganin shi, muryar Leesa ne ya kaste Mata tunani
"Salee ki tafi gida ni zanje baya wurin hajiyar talatu na karbo Mana kudin wankin da mukayi Mata shekaran jiya, Dan Allah kada ki tsaya wurin 'yan iskan hanyar Nan"

"Toh" kawai tace mata ta juya ta tafi, ta daga hannun ta ta gode ma Allah yau ta samu Daman zantawa da malam Sa'eed.

Da sauri ta qarasa wurin shi cikin nutsuwa ta Kira sunan shi, ya dago ya kalle ta sannan ya kawar da kanshi don a tunanin shi wancan Mara kunyan ne tunda yau Bai ganta da uniform ba.

Turo bakin ta tayi tace
"Malam Sa'eed Ina bazaka kula qawar Kan bane? To gashi ka bani dabino na 20"

Dan qaramin murmushi yayi sai yanzu ya gane ta ya karbi kudin da ta miqo masa Yana fadin "Baki iya gaisuwa bane?"

Da sauri yace "Ina kwana"

" Yanzu safiya ne?"

"Oh sorry Ina wuni"

Murmushi ya sakar Mata yace "lafiya yau Yaya bakisa kayan makaranta ba"

Neman wuri tayi a gefen shi ta zauna ta fara tuttudo mishi zance
"Ai yau Leesa ce da zuwa makaranta Daman haka mukeyi, Amman Mai yasa yau bakazo da wuri ba tun dazu nake jiranka fa?"

Kashe Mata Ido daya yayi cikin tsohon salon shi da ya qware na yaudaran yammata tun Yana a Sa'eed khalifa mailafiya yace "why were you looking for me? Or did you missed me already?"

Nan Salee ta sake narkewa har zabga tagumi tana kallon shi cikin mamaki tace
"Daman ka iya turanci?"

"What? Did I look like an ilitrate to you?"

Yanda ya ware Ido long lashes dinshi suka wani bazu hazel eyes dinshi suka dada fitowa ya qara tafiya da imanin Salee haka ta Bata lokacin ta wurin Sa'eed har Leesa ta koma gida Bata dawo ba, ta tsaya Wai zata rakashi gida kafin ta koma.

Hankalin Leesa in yayi dubu ya tashi saboda batason ko na minti Daya Salee tayi nesa da ita, tana tsoron Wanda suke da mugun nufi a kansu su cim mata, haka ta bazama nemanta koraro_koraro lokacin ita Kuma ta rakashi ta dawo gida.

**********

Yana shigowa gida yaci Karo da Zarah zaune a qaramar kujerar tsakar gida tana jiran dawowar shi, Yana shigowa ko sallamar shi Bata amsa ba ta miqe tana fadin

"Wallahi abun kunya bayi qare maka Sa'eed, yanzu saboda lalacewa ka rasa wani sana'a zakayi sai Saida dabino da kankana ma students? Wallahi kaji kunya,

Shagonka na kasuwa ma yaushe yake ciyar damu Mai Dadi Amman saboda tsoron Sa'ood ka barshi, wata Rana Sa'ood har numfashi sai ya hanaka, yanzu har kunyar Kiran kanka likita kakeyi saboda Sa'ood, ya fitar dakai daga mailafiya hospital ya saka ka a gidan yari, ta saka aka kulle asibitin sannan Bayan ka fito yayi maka korar Kare daga gidanka ya jefamu cikin wannan quntattatchen rayuwar,
Anya kuwa Kai namiji ne?kamar Wanda kare ya lashe ma zuciya! Stand up and fight your brother tunda shi ya manta alaqan dake tsakanin ki kaima Bai Kamata ka girmama shi ba.............🧚

_wanda sukace numbern da na bayar a pages din farko na HAR ABADA bayi tafiya suyi haquri layin ya Bata ne, Amman duk Wanda keson magana Dani zai iya following Dina yayi messaging Dina privately on Wattpad @ayeeshatmuhd insha Allah I will respond to that_

#vote
#share
#comment

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now