The next day

Kiran assalatu na farko a kunnen Leesa, ta zuba ruwa a butan su ta fita qofar daki ta dauro alwala sannan ta dawo daki ta daga Salee daga barci ta dauko Yale_yalen darduman su ta shimfida musu a kwance ta fara tilawan Al-qur'ani.

Leesa ma haka tazo ta zauna a gefen ta sunayi a tare har aka Kira sallah sukayi raka'atanul fijr sannan sukayi sallan asuba.

Gari na fara haske suka fita Leesa ta dauki tsintsiya tana share tsakar gidan Salee Kuma ta hada murhu ta daura musu ruwan wanka a babban tukunya ta firfito da kwanukan wanke-wanke Leesa na gama shara ta dauki bokitin suka fita borehole din bayan gidan dibo ruwa.

Saida suka ciga manyan randuna guda biyu suka dibo na wanke_wanke da na wankin da zasuyi anjima.

Lokacin da suka Gama har 8 tayi, suka shiga wanka da sauri don lokacin tashin shugaba ya kusa, da zaran ta bude qofa to barci ya qare suna shiryawa suka fito da wankin su day Bai taka Kara ya karya ba a cikin bokiti sannan Salee ta dauki food plask guda biyu ta fita sayo musu breakfast da nasu da na shugaba.

Har Salee ta dawo Leesa Bata sake fita ba saboda garadan da suka kwana a cikin gidan sun fito yin wanka, suna gamawa suka fita wanki suka kwashi tarin na shugaba ta Basu kudin sabulu.

Suna cikinyi sauran matan gidan sai su kawo nasu a qirga a Basu kudin wankin su, Basu suka Gama wanke kayayyakin ba sai wuraren azahar gaba daya gajiya ya nuna a jikin su, yatsun su yayi wani fari fatan ya tattare Yanda idan ya bushe dole sai yayi Saba.

**********

Yau Sa'eed a dame yake Yana Jin tsoron zuwa shagon shi na kasuwa yaran Sa'ood su sake dawowa, ya rasa Yanda zaiyi gashi bayison Zarah ta gane dan saita qara wani rigima da tashin hankali Akan na jiya.

Fita yayi daga gidan badon yasan Yanda zaiyi ba ya shiga cikin kasuwa layin bayansu shagon wani abokin sa ya roqe sa yadan zauna mishi a cewar shi kayan da suka saro Bai iso ba Kuma bayi son ya bude shagon azo neman Kaya babu.

Mutumin baiyi musu ba ya barmishi shagon yayi tafiyar shi don sun aminta da Sa'eed dukda Bai Dade a kasuwan ba don be wuce watanni 10 ba.

Sai yamma mutumin ya dawo ya biya Sa'eed haqqin shi ya mishi sallama ya tafi gida, Bai koma gida cin abinci ba Dan yasa Zarah Bata girka dashi ba, ya tsaya a wurin wata Mai Saida abinci ya saya yaci a qyamace Yana taraddadin domin duk ranar da yaci abinci a wurinda Bai aminta dashi ba sai yayi ciwon ciki.

*********
Bangaren Idris kuwa Shirin da Sa'ood yayi ma Sa'eed Kan maganar Sarwa ba qaramin Bata mishi rai yayi ba, dan yaso Yanda ya kunna Sa'ood yaje ya kunna boma_bomai a tsakar gidan Sa'eed sai ya fito da ita daga Yanda ya boye ta, tunda Sa'ood yace Masa tana raye ya yarda tana rayen Bata mutu ba.

Nabila tayi iya qoqarin ta wurin fahimtar dashi fadan da yake hadasu bashi bane mafita ba Amman shi baiji, ya riga yayi nisa idon shi ya rufe a neman Sarwa don ya gaji da ganin mamanmu a cikin wannan halin da bayi da dadin gani Wanda take ciki tsawon shekara da shekaru.

Sun Gama shiryawa zasuje asibiti tun da suka qarasa parking lot fuskar shi ta sauya, damuwan shi ya gaza boyuwa shiyasa bayi son ziyartan mamanmu akai_akai saboda zuciyar shi bata iya juran ganin yanayin ta.

Suna shiga dakin suka samu ta bata jikinta da Bayan gida saboda kwana biyu tana fama da bacin ciki, likitoci sunce sign ne na improvement saboda yanzu jikinta ya fara banbance favourable da unfavourable condition dan ko sanyi ne yayi Mata yawa tana nuna sign.

Da sauri Idris ya fito daga dakin qolla na taruwa a idanun shi, yabar Nabila da 'yarshi sajida suna Taya nurse gyara ta, khalifa da hydar Suma sukayi joining dinshi a waiting area suna jiran su Gama.

KAMA DA WANE....(Completed)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora