Tarko/martani

1.1K 94 2
                                    

Godiya mara misaltuwa ga masu karatu
Masoya kuma y'an uwa ❤️🍯💝
Zubeefly na qaunarku , tsofaffin masu karatu
Harma da sabbin masu karatu 🤗💝
Babu laifi idan kunyi tambaya a comment box, a shirye nake da na amsa bambayoyinku da karb'ar gudun mawar ku 💝
Love you oll 😍😍

Thank you for giving me Nd my precious little book a chance.
Even if you decide not to continue reading, thank you for taking the time to check the previous pages. Maybe the time isn't right but it will always be here.

Always feel free to ask me any Question !Via
Comment box, DM, Twitter and Instagram everything is fine InshaAllah. 🤲🏻💝

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~,

Rana mai kamr ta yau laraba, Jameel bai fita aiki ba domin ya gaji sosai, kuma yana buqatar baiwa matarsa lokacin sa ,
A kwance suke a kan gado, tana maqale da shi, yana faman jan gashin kanta yana massaging d'in gashin ,
Sannan kuma ga wayarsa a hannun Raeesah tana faman dannawa , (are you thinking what I'm thinking🤔)
Sai faman shige-shige take, a wayar
Shi kuma gogan yana ta kwararo mata labarai kala kala , harama da labarin anty Humairan sa  yadda suka taso cikin qaunar junan su, saidai abu kad'an yake had'asu fad'a, saboda yawan zolaya irin ta jameel tun yana yaro .

Saidai fah ita Raeesah har yanzu bataga wani abu makamancin wannan bah don shi wayarsa ma babu lambobim y'an mata a ciki inba y'an office d'in sa ba,
Amma abin da yake qara d'aure mata kai shine Toh idan har jameel baya da alaqa da matar da tazo, Toh mai yasa zatace tana d'auke da babyn sa? Wannan shine abun tambaya!
A haka dai taji ma duk ta gaji da bincika wayarsa, inda ta waiga gefen fuskarsa taga da alamu bacci yayi gaba da jameel d'in nata , amma dai wannan mata sai kinci ubanki!
Tabbas kinyi da y'ar halak! Kuma mijina yafi qarfinki! Sannan zanyi maganin ki InshaAllah
Kinyi da Hauwa kulu.....
A ranta take fad'in wannan, (hmm yaya zata kasance?)
itama gyara kwanciya tayi a kan kirjinsa ta kwanta, basu tashi ba sai misalin qarfe hud'u na yamma .
~~~~~~~~~~~~~~~~~~
          Washegari

Raeesah ce a cikin BMW tareda drivern Jameel wanda jameel yayiwa umarni da ya dinga kaita duk inda zataje,
A qofar gidan su Ihsan akayi parking ko minti biyar ba ayiba saiga Ihsan da Asmau sun shigo tare ( dama Asmau tana gidan su Ihsan tun tuni) ,

Tafiya suka fara  gashi har sun kai kimanin mintuna Talarin suna tafiya a motar ,
Cikin mintuna arbain suka isa inda zasu , bayan tafiya mai tsaho da sukayi ,
Raeesah tace da su Asmau:
Ku jirani a moto,
Kar ku shigo, saidai idan nace ku shigo
Amma ku jira anan,
Toh suka ce da ita,
Ki dai yi a hankali , kuma harki yi mata da sauqi, ki nuna mata ke kin fita iya bariki, koh kadan kar ki raga mata, best of luck,
Abinda ihsan tace da Raeesah kenan, sannan ta fita a motar ta nufi cikin gidan da sukayi parkin a gate d'in,
Cikin isa da taqama Raeesah ta bud'e front door ta shiga cikin qwarjini , kai zaka zaci dama ta saba shiga gidan ne.

Sunglasses d'in dake fuskarta ta cire ta maida shi saman forehead d'inta,
Matar dake zaune a palon ce ta ragana don Ganin wacce ta shigo mata gida without permission '

Ke baiwar Allah ya zaki shigo min gida   
Ba tareda izini ba?
Ai a ganina bai kamata in shigo da neman izini ba,
And by the way ! Ba wajenki nazo ba
Wajen Amina nazo,
Hummm idan tana nan inason ganinta ,

Waya hajia binta ta d'auka ta kira Amina !
Hlo daughter where are you,
Mommy I'm in my room
Okay come downstairs!
Alright mom.
Da sauri ta sauko don taga mai ke faruwa domin Tasan dai mommynta bazata mata irin wannan urgent kira ba,

Mommy gani:
Yauwa nemanki aka zo yi

Raeesah wacce ke gefe ta fara clapping hannunta,
99dayz for the thief one day for the owner,
Abinda tace da ita kenan
Kina mamakin yadda akayi nazo gidanku,
Toh bayan kince min kina d'auke da cikin na mijina a jikin ki, tun daga ranar na na fara neman details naki,
Humm... sai gani yau a gidanku,
Nazo ne domin in miki warning akan mijina kar in sake jin kin ce mijina yayi miki ciki, idan ba haka ba toh sai nayi miki abinda koh kare bazai ci ba, and by the way ... ki shirya mu tafi asibiti domin ayi miki pregnancy test daga nan sai in raka ki court ki kai report,

Innalillahi wa inna ilaihi rajiun ,
Abin da hajia binta ke maimaitawa kenan, Amina ashe baki da hankali? Haka kawai kije ki samu mata kice mata kinada ciki kuma na mijinta?
Ince last month ma kinyi period, ?
Baiwar Allah kiyi haquri don Allah ki yafemata amma yanzu babu inda zaki da ita tunda babanta baya nan kiyi haquri wlh qarya take!

Amina kuwa dake zaune kan leather sofas hannu ta qame a kirjinta tayi shiru , tana mamakin yadda akayi Raeesah ta gano gidansu,

Da qyar dai Aka shawo kan Raeesah ta haqura Amma da tace sai Anje anyi Test zata kyalesu,
Fitowa tayi ta dawo cikin mota,
Babe yane?
An gama wannan sai dai kuma wani idan ta sake ,
Labarin yadda sukayi da maman Amina ta tsara musu, dariya suka tayi suna nishad'i

qawata shi yasa nace kibi abin a hankali saboda wannan shegiyar zata iya rabaki da mijinki, ki dai yi a hankali kuma ki ci gaba da bin mijinki ,
Taji dad'i sosai da irin shawarar Asmau ,  domin samun irin wannan qawayen da wuya,

Nagode dear Allah ya nuna min Auren ku
Ameen suka ce sannan  kowacce ta koma gida, Raeesah kuwa special dinner ta fara shiryawa jameel d'inta bayan ta koma gida,
Saidai wani irin shawqin soyayyar sa da ke qara shiga ranta. Tamkar sabuwar soyayya.

A b'angaren Amina kuwa tasha fad'a a wajen mommynta duk da basa yi mata fad'a amma yau dai kam tayi mata don yanzuma ta hanata fita har na tsahon sati uku.

How was this page?😍
Vote pls 🦋

D'iyar fari 🧕🏼Where stories live. Discover now