PAGE 71-75

1.1K 81 5
                                    

~~~~~~~~~
Matsanan cin kuka takeyi mai ban tausayi tana share majina wallahi baxan yafewa zuciyata ba idan har ban auri jameel Aliyu bah, dan Allah qawata ki taimaka min ki ceto rayuwata pls
Wata matashiya ce ke fad'ain wannan maganar tana mai zubar da qwalla
qawarta Fatima itace mai bata haquri haba babe kina yarfa mata wallahi duk wannan kyawun da Allah yayi miki ga ilimi sannan gaki da dukiya ga isa , ga mulki da Allah yabawa babanki sannan gaki da sura mai kyau , bayan haka kinada abinda duk namiji xaiso ace kece a matsayin matarsa Toh menene naki na zubar da hawayenki a banza a kan wanda baisan kinayi ba!
     A,a fatima duk dukiya ta Jameel ya fini, duk kyawuna jameel ya fini sannan shima yanada ilimi, nidai burina ace ni ce matarsa ta sunnah amma kash.... wata banza wacce batasan menene yake mata ciwo ba itace zai aura
Ba niba! Babban abinda ke damuna shine jameel baya sona baisan inayi ba ,
Kuka taci gaba da yi idanuwanta kuwa sunyi jazir
Fatima ce tace Amina karki damu akwai mafita
Cikin hanzari Amina ta juyo ta kalleta dan Allah ki fad'a min mecece mafitar
Matsowa fatima tayi kusa da ita my Friend relax... everything will be okay! But stop crying
Da sauri Amina ta share fuskarta I have stopped..
okay inji fatima! What we will do is kawai mu kawarda d'aya daga cikinsu... koh jameel koh kucakar da zai aura
OMG! Fatima are you in your senses?
Yes.... I I'm
Wannan shine kawai abinda zamuyi ! Idan kuma ba hakaba ki tsaya a banza kinaji kina gani zai auri wata ba keba, ke kuma sonsa ya kasheki  daga nan kuma kin zama mara amfani , toh what do you think?!
Amina dai ranta bai soba domin ita gani take bazata iya kashe mutum ba ballantana ma ace wanda takeso perhaps dai tasan baya sonta amma bazata iyaba
     Eh na yarda saidai bazan iya kashe jameel ba kuma bazanso ace ya mutu ba, saidai mu kashe wacce zai aura amma ba shiba
Okay fatima tace idan har kin yard zakiyi abinda na saki toh baza kiyi nadama ba kuma xaki samu jameel
Cikin farinciki Amina ta juyo are you sure fatima? Idan har hakan ya kasance toh nayi miki alqawarin zan baki 30 milliom naira
Hahahah fatima tayi wata irin dariyar mugunta... ni kaina nasan bani da mutunci kuma zan iya koh menene indai da gaske kike zaki bani 30 milllion toh ni kuma daga yau zan fara neman information akam yarinyar da zai aura
Za kiga aiki da cikawa kuma kukanki ya qare daga yau
Dariya suka fara suna raha da farinciki ita da Fatima

~~~~~~~~~~
A b'angaren su Raeesah kuwa abin yayi nisa yau aure saura sati biyu
Komai da ake buqata a gani a gidan amarya abbanta yayi ordering daga abroad sannan anyi inviting manyan mutane zuwa wajen bikin , gida har ya fara cika su anty salma anyi kiran masu SPA na gargajiya da na zamani maman su basma itace ta d'auki nauyin kayan mata da dilke
Kai da ka ganta kasan ta sha gyara irin na amare  fatarta sai shining take kamar ka taba jini ya fito kuskarta kuwa sai wani haske da take yi ,
Shi kuwa jameel baki yaqi rufuwa saboda farinciki, Hajiyar sa kuma ana ta hidima akai a kawo d'an autan ta zaiyi aure koh ina sai murna
Humaira yayar jameel wacce ke aure a Ghana har tazo itama da y'ay'anta anas da ummi
Gaba d'aya way'an nan families guda biyu kowa a b'angaren sa babu komai sai murna da farinciki.
Raeesah ce xaune akan doguwar kujera suna ta hira da baqi y'an uwa da abokan arziqi
Maman hauwa ce ta fito daga kitchen tayi kiran Raeesah! Ke baki da kunya ne mai yasa zakizo cikin mutane ki zauna ai sai ace baki da kunya ki wuce d'aki ki zauna karki qara fitowa cikin mutane
Kwanciya tayi akan gado ta dauki wayarta ta dokawa jameel d'inta kira
Sau d'aya wayar tayi qara ya d'auka
Hlo my heartbeat 💗
Darling inata missing d'inka yaushe zaka zo?
Hmmm ..... next tomorrow !  ya amsa
Why not tomorrow Tace
A,a baby idan nazo gobe ai sai ace na cika gaggawa, dariya dukansu suka fara
Toh !
zafafan kalaman sa ya zubu mata da kuma qauna!
A haka suka kashe wayar gaba d'ayansu Suna farinciki.
Bayan sun kashe wayar ne ta  kira ihsan da asmau tare a conference call suna shawarar abinda ya kamata suyi
Fatima ce ke waya a d'akinta tana bada umarnin a nemo mata bayanai akan hauwa Husseini domin taga sunanta a invitation card sannan a nemo mata bayani akan hall din da za,ayi dinner d'in bikin
Ita dai fatima ji take kamar ta samu 30 million a hannunta
Gata y'ar talaka amma Allah yayi ta da son abin duniya don ita cikakkiyar yar bariki ce wacce idanunta suka bude da duniya.
Ita kuwa Amina kullum sai tunanin wanda baisan ma tanayi ba.

🦋🦋🦋

D'iyar fari 🧕🏼Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora