PAGE 91-95

1.4K 98 7
                                    

           Dedicated to Abubakar ( boc🌺🌸

~~~~~~~~~~~~~
Kamar da wasa abindai sai ci gaba yake, gashi yau watan Raeesah hudu a  gidan miji hmm Rayuwa ta chanza , al'amura duk sun chanza,
Hmm.. abindai ba'a magana 😋 ( koh ni zubeefly da naga Raeesah da qyar na gane ta) 🤪
Back to business 🤞🏻a yau Monday da safe Jameel na gaban mirror yana gyara tie d'insa, Raeesah ce ta zo ta bayansa ta sanya hannayenta ta zagaye wuyansa tana faman yin shagwab'a sunshine pls ka zauna a gida yau I need you by my side pls sai wani narkewa take a jikinsa watermelon you know I have an important meeting in my office koh , kiyi haquri dan Allah ki barni in je I promise you gobe zan zauna InshaAllah kinji my love 😍
Da qyar dai ya shawo kanta ya manna mata peck a goshi amma duk da haka Raeesah dai bata haqura ba , har bakin qofa ta bishi tana shagwab'a kamar yadda ta saba, roqonta ya fara yi dan Allah my love ki bani brif case na I will be late, Toh shikenan zan baka amma sai kace kana sona! Okay ina sonki my Raeesah A'a ni ba da hausa ba da larabci zaka fad'a idan ba haka ba you are not going anywhere!
😏hmm kedai kamar yarinya wallah... ehh mai kace? No nace ke kyakyawa ce 🤣 Raeesah tace: Toh naji kace kana sona da larabci idan ba haka ba bazan baka brief case naka ba 🤪
Gyaran murya jameel yayi sannan!!! Yace
Ana ahabbuki ya habeebti 😘
Ah toh koh nayi daidai oho 😂
A ransa yake fad'in wannan, duk da haka da qyar ta miqa masa ya wuce , yana shiga mota mai gadi ya bud'e masa gate ya fita , Raeesah kuwa bata koma ciki ba har saida mai gadi ya rufe gate, addu'a ta kwararowa mijin nata!! Ya
Allah ina roqon ka ka tsare min mijina ka kaishi lafiya ka dawo dashi lafiya sannan ka kareshi ka bashi abinda yaje nema, ya Allah ka nesanta shi da cin haram ka bashi halak d'insa da yaje nema.
Ciki ta koma ta nemi waje ta zauna sannan ta d'auki wayarta ta kira Asmau da Ihsan, conference call ne kamar yadda suka saba, hlo girls how fa: lafiya kalau ya kuke, fine ya mai gidan klu !  Nace idan kun samu dama koh zaku d'an shigo gidana? Wallahi nayi missing d'inku ! Toh inji ihsan bari muga ni dai yanzu ina yiwa mom aiki ne zuwa anjima zaki gammu, alright bye bye sannan sukayi ending call d'in .

~~~~~~~~~~~~
Ba ayi minti ashirin da gama wayarsu ba Raeesah taji anyi knocking!! Yes come in '
Knock knock!! Aka qara knocking har sau hud'u! A'a waye idan bazaka shigoba Toh ka koma! Ance ka shigo kuma kana faman knocking Toh ba sai ka koma ba...
Da qarfi taji an bankad'o kofar an shigo 😳
Bak'uwar fuska ta gani tayi tsaye a kanta sai faman kalle kalle takeyi, Wow this is Amazing... fantastic 🌚lallai masoyina ka kashe kud'i a gidannan sai dai ba wannan ce matar da ta dace da shiga gidan ba , ni yakamata ace ina cikin wannan gidan!
Idanuwa Raeesah ta zazzaro tana mata kallon Rashin sani domin batasan wannan fuskar ba
Amina ce dai a cikin palon Raeesah a tsaye tana mata rashin arziqi,
Tsaye Raeesah ta tashi!! Ke kuma daga ina? Waye ya aiko ki? Kuma mai kikazo yi?
D'ai d'ai ta fara takawa tana zagaye Raeesah , sai dai Raeesah ta kasa jurewa, hannunta tasa ta bigi qirjin Amina da qarfi , har saida Amina taji zafi sosai
Dalla malama kyaleni, ke kin san koh wacece ni? Abinda Amina take fad'a kenan Toh bari in fad'a miki idan baki sani ba , nice Ex-girlfriend d'in jameel kuma ina dauke da cikin jameel a jikina, saboda haka nazo ne domin ganin uban babyna,
Shin yana ciki ne? Koh ya fita?
Raeesah dai was speechless domin abin ya d'aure mata kai
Hawayen dake k'okarin fitowa daga idanuwanta tayi k'ok'arin hana shi fitowa ta daddage ta shanye,
Ya salam! Ya salam,  ya salam!!
Abinda Raeesah ta dinga maimai tawa kenan a ranta, domin kanta ya kulle gaba d'aya ta rasa madafa,
Daurewa tayi ta daka wa Amina tsawa!
You bitch get out of my house , kije ku hadu a inda kuka had'u yayi miki cikin,
Tsaki Amina ta ja what ever! Xan fita amma fa zan dawo !
Tana fita Raeesah taja qofa ta rufe tareda matsanancin kuka, sulalowa tayi tun daga sama har qasa ta zube sharaf a kasa tana faman kuka,
Ni Jameel zai yiwa haka? Meyasa banga mutuwata kafin ganin wannan tsinanniyar ba, Allah ya isa tsakanina da kai jameel bazan yafe maka ba,
Saidai wata zuciyar na yi mata fad'a kan yanke wannan hukuncin da wuri, alhalin tasan halin mijinta koh waye ba mutum ne mai son kula mata ba,
Wani ihu mai gigitarwa ta saki wanda ya jawo har mai gadi saida yaji ihun kamar ana yankata,
Ihsan da Asmau ne suka qaraso da gudu domin sanin abinda yake faruwa,
A kwance suka tarar da ita tana tsanin kuka ,
Raeesah! Raeesah! Mai ya faru ? Meye aka miki ina jameel, keda wa, babu tambayar da ta iya amsawa a cikin tambayoyin da su Asmau suke mata, saidai nuni da takeyi da d'an yatsan ta tana nuna bakin qofa da alama akwai wani koh wata daya fita ba da dad'ewa ba.
Asmau ce ta ta nufi gate da gudu,
Gurin mai gadi ta nufa,
Mai gadi mai gadi!!
Naam! Ya amsa '
Yauwa mai gadi kafin shigowar mu waye kaga ya fita daga gidan nan,
Amsa mai gadi ya bata
"Eh Toh da safe dai oga ne ya fita kuma hajia ce ma naga ta rakoshi har parkin space, bayan shi kuma sai wata matashiya data shigo da mota harma ta dinga zagina domin ban bud'e mAta gate da wuri ba, da ta shiga gidan sai naga ta fito kamar ranat a b'ace, daga ita dai babu wanda ya shigo sai ku
Okay nagode, Asmau ta koma ciki da sauri,
Ciccib'ar Raeesah suka yi suka kaita har d'akinta,
Bayan wasu mintuna ne Raeesah ta bud'e narkakkun idanuwnan ta wanda sukayi jazir don kuka,
Magana ta fara cikin muryar kuka,
Wata ce ta shigo ta ci mun mutunci harda cewa wai tana d'auke da babyn Jameel.
What! Are you serious! Who is she
Wani sabon kukan ta tasa tana faman yi ,
Hak'uri suka fara bata suna lallashin ta tareda kwantar mata da hankali,
Amma dai wannan abu da mamaki , inji Ihsan
Raeesah bazan ce wannan matar tayi gaskiya ba domin kin fimu sanin halin mijinki, amma abin dubawa shine toh ita d'in wacece,
Bugu da k'ari ma kin san halin mutane a duniya baka san maqiyinka ba, akwai mutane da dama wanda basa son ganinki da mijin ki a kullum burinsu suga bakwa tare , amma ki qara haquri, kuma kiyi bincike tareda tunani mai zurfi kafin ki yanke hukunci,
Asmau ce ta matso daidai fuskarta ta share mata hawayen ta da gefen mayafinta, Raeesah bana so kici gaba da wannan kukan kuma ban so ki nunwa jameel cewa wani abu ya faru, ki natsu kiyi bincike , ki zama mar'atu saliha, kiyiwa mijinki biyayya sai ki rabauta, kar ki sake maqiya su shiga sha'anin ku kinji Raeesah na! Yauwa
A haka sukai ta bata baki har ta haqura sannan suka tafi ,
qarfe hudu jameel ya dawo gida, yaga palon babu kowa kuma bai ga matar tashi ba, domin ya saba idan ya shigo yayi arangama da kyakyawar fuskarta, 
Salam sunshine ! Sunshine! Where are you? Sunshine I'm back...
shiru kakeji, kofar d'akin Raeesah ya bankad'a ya shiga,
Sunshine, sunshine, meye yake damunki ? Hannu ta miqo mishi ya riqeta,
Tsorata yayi da jin yanda jikinta yayi zafi sosai,
Subhanallah! Meya ya same ki tashi muje asibiti ,
Cikin dashashiyar murya da tasha kuka ta amsa no I'm okay
Aa ki tashi muje asibiti ga jikin ki yayi zafi, kuka ta fara tana fad'in ni baxanje asibiti ba, na sha magani, okay my love barin samo miki abinda zaki ci, aa I'm not hungry, kiyi haquri , janyo ta yayi ya qanqameta a jikinsa yana shafa bayanta a hankali har wani sabon baccin ya dauketa.

V.O.T.E pls🙏🏻
Zubeefly🦋

D'iyar fari 🧕🏼Où les histoires vivent. Découvrez maintenant