PAGE 31-35

1.4K 106 0
                                    

~~~~~~~~~~~~~
Masoyiya ashe haka dama kike da sauqin kai?
Ashe bazan sha wahalar samunki ba? Ashe haka soyayya take da dad'i?  A kullum burina shine a d'aura min aure da abin da nafi so a rayuwata, zan nuna miki soyayya irin wacce babu wani namiji daya tab'a gwadawa, zan so ki kamar yanda Romeo yake son Juliet, sannan zan haukace a kanki kamar majnoon Laila .
Maganganun sane suka rastsa cikin jikin ta a lokaci guda taji kamar ba,a  duniyar take ba saboda d'ad'in kalaman nasa
Kanta ta d'ora a kan kafad'arsa tana fad'in da gaske? Eh da gaske ya amsa, Toh idan haka ne toh ashe tunanin mu iri guda ne nima haka nakeji a cikin jiki na
Amma nayi mamakin kaina da sonka ya shiga cikin zuciyata cikin lokaci qanqani domin ban tab'a zato ba,
Hannunta ya kamo yana murzawa a hankali masoyiyata ki yarda dani wallahi ina son ki, watermelon din dake cikin plate ya dauko ya sa mata a baki tareda kalamai masu dad'i
Nima ina son.....k...
A daidai wannan lokacin ne Raeesah ta farka a firgice daga baccin da take
Hankalin ta ya tashi, batayi tunanin yin addua ba ta fara kuka tana fad'in:wayyo Allah Abba.....maman hauwa kizo......
Wata irin azaba ban zafi takeji dukda air conditioner din dake d'akin amma sam ji take kamr babu
A lokacin ne ta samu bakin yi addua , duk adduar da tazo bakin ta yi take
Wayyo Allah! Ubangiji ka tsareni daga sharrin shed'anun Aljanu 😭 ai dama saida na fad'a wataqila ba mutum bane ya bani umbrella tunda gashi nan harda fitomin a mafarki.
Agogon bango ta kalla taga 3:42pm , tashi tayi a tsorce ta shiga toilet ta dauro alwala ta dawo d'aki ta d'aura xani ta hau sallah tana roqon ubangiji daya rabata da duk wani abun da zai cutar da ita , bayan ta idar da sallar ne  bud'e side drower ta bud'e ta dauko Alqurani ta fara karantawa , don rabanta da Alqurani ma ta manta tun a islamiyya amma gashi yau ta tuna dashi ( kuma dama ance duk wanda ya bar Alqurani toh Alqurani zai barshi fiye da yanda ya barshi) .
A haka dai ta samu ta karanta wasu y'an ayoyi na neman tsari da neman kariya sannan ta rufe Alquranin ta tofa addua a jikinta da fuskarta
A kan abin sallar ta fara bacci har asubahi yayi kafin ta tashi tayi alwala tayi sallah .
Kasa komawa baccin tayi domin kamanin mutumin da ta gani a bacci sune suke mata yawo a cikin zuciyar ta da kuma idanun ta.
Tabbas shine! Shine mutumin daya bani umbrella jiya, Toh idan yasan shi mutum ne ba aljani ba toh mai yasa danayi masa tambaya bai bani amsaba ya wuce? Kuma mai yasa zai biyoni har ma yace yana sona a mafarki?
Ita kadai takeyi wa kanta way'anan tambayoyin da batasan amsarsu ba amma dai abin da zuciyar ta ke gayamata shine wannan mai umbrellar aljani ne! Wata zuciyar kuma tana gaya mata ba aljani bane tunda har ya iya taimakon ta ya bata umbrella .

~~~~~~~~~~~~~
Har karfe 7:00 n safe batayi bacci ba domin a tsororace take amma ta yanke shawarar bazata gayawa kowa abinda ya sameta ba sai ihsan da Asmau koh Abba bazata gayawa ba balle ya tada hankalin shi
9:00am tayi wanka ta gyara gadonta sannan ta shiga kitchen ta had'a breakfast d'inta da kanta tana aiki tana saqe saqe a ranta kuma tana kallon fuskarsa a idanun ta da kuma muryar daya mata magana lokacin daya bata umbrella, bayan ta karya ne ta dauko wayar ta fara neman lambar qawayenta, conference call ta had'a musu su ukun sannan ta kwashe labarin ta kap ta gaya musu ,
Alhamdullilah at last my bestie is now a woman......
Asmau ce ta fad'i haka tana dariya tana tsokanar Raeesah, Taji haushi sosai yanzu abinda zaku ce kenan? Nida nayi tunanin zaku bani shawara ashe qara min haushi zakuyi? Toh ba damuwa sai anjima!
Haba hauwan mama.... haba hauwan Abba
Kiyi haquri kinsan halinmu ai idan ba muyi tsokana ba bamu jin dad'i,
Ihsan ce ta fara bata haquri tana kwantar mata da hankali sannan tace mata ta dinga yin addua idan zata kwanta , kuma ta dinga kwanciya da Alwala
Haka suka gama waya har kowa ya kashe wayarsa,
Raeesah kuwa tunani  ya mata yawa  haka ta wuni ranar koh palour bata fito ba.
Har lokacin da Abba ya dawo bata fito ba tana d'aki , zama yayi akan sofa Hadiza ta kawo masa mango juice  har ya fara sha ya sauke kofin kan table ina wannan yarinyar ta shiga ne? da safe na fita ban ganta ba gashi yanzu na dawo ban ganta ba! Kirawomin ita... koh kin mata wani abune bayan nafita?
B'ata rai Hadiza tayi sannan tace: me kwa zan mata tsaki tayi sannan ta nufi d'akin Raeesah tace mata taxo Abba yana son ganinta.

~~~~~~~~~~~
Jummuah mufida Allah ya had'a mu da Alkhairan wannan dare
Light upon light
Have a nice weekend 😘
🦋🦋🦋🦋🦋
V.O.T.E

D'iyar fari 🧕🏼Where stories live. Discover now