51-55

1.1K 114 3
                                    

Dedicated to Raudatul Jannah,hauwa Adam, Asmau Adam & Sadiya Bello 🌸🌸🌹🌸much love .


~~~~~~~~
Tuqi Abbah yake cikin hanzari kamar zai tashi sama, yanayi yana kuka yana fad'in Mamana dan Allah kiyi haquri karki mutu kece rayuwata, kece farin cikina Kiyi haquri na fasa aura miki wanda bakyaso,
Maman hauwa dake rike da raeesah itama kukan take tana fad'in: dan Allah kayi sauri ka tuqa motarnan da sauri idan yarinyar nan ta rasu ka cuceni kuma bazan yafemaka ba, shi kuwa abba hankalinsa ya tashi kansa ya d'au zafi, zuciyarsa na quna gashi tuqin yake kamar zai tashi sama amma gani yake kamar baya yi.
Suna isa asibitin doctor sule yaro nurses guda hudu suka iso wajensu suka karb'i Raeesah suka shiga da ita , umarni aka basu da su tsaya a reception kar su shigo ,
Doctor sule da yake yasan komai baiyi kasa a guiwa ba don taimakawa Maman hauwa akan plan d'insu, bayan ya fito daga Emergency room ne ya tarar da abba da maman hauwa a reception suna zaune sunyi tagumi , zuwansa ne yasa suka tashi tsaye suna tambayarshi halin da d'iyarsu ke ciki.
Innalillahi wa innalillahi rajiuna abin da doctor sule ya fad'a kenan yana yi musu tsawa! Menene haka !!meyasa zaku bari yarinya kamar wannan ta shiga halin damuwa? Toh gashinan abinda kuka ja mata ai! Ku biyoni office d'ina
A gaskiya hankalin abba ya tashi maman hauwa ta tausaya masa sosai, bayan sun shiga office d'in Doctor ne ya basu dama su zauna, sannan ya basu advice akan abinda ya kamata suyi kuma ya gayamusu abinda ya kamata ta dinga ci, saidai bai basu maganiba yace suje an sallamesu  sannan suka tafi gida.

~~~~~~~~~~~
Kwana biyu Raeesah ta nuna alamar samun sauqi 😂 abba yaji d'ad'i sosai da yaga jiki ya ware.
Abbane zaune a garden yana hutawa , wayarsa ya d'auka ya kira lambar Raeesah,
Assalma Abba
Wslm mamana! Kizo Garden ki sameni inaso muyi magana
Kashe wayar yayi sannan ya ajiye wayar, koh minti biyu ba,ayiba saiga Raeesah tazo wajen Abban nata, zama tayi akan carpet d'in da aka shimfid'a a garden din wanda ya qarawa garden din kyau da tsari,
Magana Abba ya farayi kamar haka: mamana ya jiki da sauqi tace, Toh abinda yasa na kiraki shine dama na fad'a miki tunda bakyason aurenan toh na fasa miki, ki daina damuwa kinji mamana! Toh Abba saidai itama ta tausayawa abbanta kuma tayi tunani mai tsaho kar Allah ya hukuntata akan bijirewa babanta,
       Abba na amince ka auramin wanda kakeso ni kuma InshaAllah zanyi biyayya !!
Abba ne ya d'ago kansa cike da mamaki! Mamana da gaske kin amince da auren zab'i na? Cikin shagwab'a tace eh abba na amince, na tsaya nayi tunani ne kar in sab'a maka Allah ya hukunta ni shiyasa nace nikuma zanyi biyayya. Na gode miki mamana ina Alfahari dake Allah yayi miki Albarka Allah ya sa ki gama da duniya lafiya mamana. Nan dai yayi ta sa mata albarka yana mata godiya. Bayan ta shiga cikin gidane ya dauki wayarsa ya kira Alhaji Aliyu yana k'ara jaddada masa auren na nan, kuma yanaso zuwa nanda sati d'aya a turo yaron domin su daidaita da Raeesah .
Bayan ta shiga gidane ta nufi d'akin maman hauwa , sannan ta sanar da ita abinda ke faruwa, lallai ma Raeesah yanzu ke kin yarda da auren? Karki manta fa da plan d'inmu ya tashi a banza kenan? Lallai na yarda baki da hankali yaronda koh ganinsa baki tab'ayiba shine zaki aura, ba damuwa bazan takura miki ba
Maman Hauwa kiyi haquri na tsaya nayi tunanine kar Allah yayi fushi dani akan mahaifina shiyasa kawai nace na yarda kuma na amince da auren d'an Alhaji aliyu kundi kuma zanyi biyayya dukda ban tab'a ganinsa ba.
Toh shikenan Allah yasa shi yafi alkhairi Allah yasa mu dace, Ameen Raeesah tace tana sunkuyar da kai,
Saidai batasan ya zatayi da tunanin jameel ba don Har yanzu bata dainaba kullum saita ganshi a mafarki .
Har an fara tsara abubuwan da za,ayi a bikin gashi maman hauwa ta fad'a wa anty ta nijar cewar zata kawo yarta ayi mata dilka da magungunan mata irin na y'an Nijar, ita kuwa Raeesah bataso don magungunan mata haushi suke bata koh kad'an ranta bayaso
Anty salma ce mai yi mata fad'a: ke baki da hankaline toh darajarki ake so a d'aga da kuma samar miki mutunci a wajen mijinki da kuma qauna .
Toh Anty salma mutumin da koh ganina bai tab'a yiba maybe ma baya sona tunda gashi kullum sai ance yazo ya ganni amma sai yace wai yana da aiki a office kamar shi kad'ai ne mai office,inji Raeesah.

Can you vote?
🦋🦋🦋🌹🦋

D'iyar fari 🧕🏼Where stories live. Discover now